_*Tambaya:*_
malam dan Alllah idan miji ya sumbaci matar sa da ramadan shin haka xai iya bata azumin su ko bazai iyaba.
nagode
_*Amsa:*_
_Zance mafi inganci shi ne ya halatta ga mai azumi ya sumbaci (kissing) din matarsa, amma da sharadin idan za su iya control din sha'awarsu ta yadda hakan ba ze sa su yi jima'i ba ko maniyyi ya fita._
_An karbo hadisi daga Aisha (r.a) ta ce: “Manzon Allah ﷺ ya kasance yana sumbanta alhali yana azumi, kuma yana runguma alhali yana azumi, amma shi ya fi ku mallakan sha'awarsa”. Bukhary da Muslim._
Wannan hadisin na nuna mana:
_Halas ne mutum ya rungumi ko sumbanci (kissing) din iyalinsa a cikin watan Ramadan matukar zai iya kare kansa daga jima'i ko fitar da maniyyi._
_Runguma da sumbanta ya halatta, amma ba jima'i ba._
_Wanda ya sumbanci matarsa kuma maniyyinsa ya fita, to azuminsa ya lalace, kuma zai kame bakinsa daga ci da sha har sai rana ta fadi, kuma zai rama azumin, bayan ya nemi gafarar Allah da tuba zuwa gare Shi._
_Amma idan madziyyi ne kawai ya fita, to azuminsa bai lalace ba kamar yadda mafi yawan malamai suka yi bayani._
_Don haka, sumbanta na iya karya azumin mutum matukar maniyyinsa ya fita._
Wallahu a'lamu.
Dalibinku:
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_
Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.