Jukun

Wani bajukune ne (yaren jukun) bashi da lafiya, gashi 'yanuwansa basu da kuɗin da zasu kaishi asibiti. Haka dai suka ciwo bashin dubu biyu da ɗari biyar suka kaishi asibiti. A can asibitin kuwa lamari ya girmama domin bayan an basu gado kuma sun sami kimanin kwana biyu sai kuɗin da suka ranto suka gaza. Ana cikin hakan ne sai wannan mara lafiya ya mutu. Koda mutuwarsa sai 'yanuwansa suka fara ƙoƙarin kimtsa gawarsa. Ana cikin haka sai aka ga dubu goma a cikin aljihunsa. Saboda tsabar haushi kawai sai wani ɗan uwansa ya ciro ɗamarars(belt) ya cirewa mamacin wando ya dinga zaneshi.

Post a Comment (0)