.UKU BALA'I
NA.
KAMAL MUHAMMAD LAWAL.
(KAMALA MINNA.)
07039355645
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร
BABI NA HAMSIN DA BIYAR
Dubanta yake yi cikin wahalallan yanayi zuciyarsa na ta faman kokarin bankado masa abin dake boye amma kwanyarsa sai hayaki take yi masa ji yake yi kamar ya mike ya shaƙo Hajiya Layla don ya tabbata akwai wani boyayyan al'amari game da ita zai iya cewa ma halin da yake ciki a halin yanzu ita ce sanadi ba kowa ba runtse idanunsa yayi gami da sakin wani nishi mai karfi kamar macen da ke nakuɗa.
"Hajiya Layla mai ya dawo dake rayuwata a daidai wannan lokacin kuma meye hadinki da MATATA?".
Ya fadi cikin yanayi na azaba da raɗaɗi da yake jin ko ina na jikinsa ya dauka numfashin sa sai sama da kasa yake yi.
"Dr.Erena kenan kana tunanin akwai abin da zai sake dawo dani rayuwarka a wannan karnin kar kayi zaton wani abu amma abu daya nake so ka tuna a rayuwarka shi ne Sharri dan aike ne duk in da aka tura shi zai je ya dawo abu daya nake so ka kuma tunawa shine Malam Nata'ala".
Areefa da ke tsaye tun dazu idanuwanta na tsiyayar da hawaye Hajiya Layla ta dube ta sosai kafun tace da ita.
"Zo ki samu waje ki zauna mana kin tsaya a tsaye in har kika ce kallon wannan mutumin za ki din ga yi kina zubda hawaye kina da aiki sosai a gabanki hawaye ya kamata ace ya tsaya miki a wannan matakin da kike".
Girgiza kai tayi tana mai sake watsawa Dr.Erena wani matsiyacin kallo ji take yi kamar ta shako shi ta kashe shi don wata tsanarsa take jin na sake buɗe fili a zuciyarta mai girman gaske.
A hankali ta shiga takowa tana isowa gareshi warin da take ji yana tashi daga jikinsa shi yafi komai tayar mata da hankali idanunta ta runtse gami da rike numfashinta idanuwanta akafe akan sa ba abin da ke cikin su sai zazzafar kiyayya mai girman gaske shi kansa sai da yayi mamaki kan irin kallon da take masa kau da kai yayi yana tambayar kan sa mai ke shirin faruwa dashi ne tun da ya tashi yau ya rasa gane kansa tun kafin ya isa wajan aiki ya samu tsautsayin haduwa da yan fashi ko makasa zai ce masu oho suka yi masa dukan shan gishiri gami da kwace jakar makuɗan kudaɗen da zai je da su Company din sa domin zubawa ga wata harkalla da akayi masa tallarta ya amince zai yi ta.
Bayan sun dake shi sun fasa masa mota sun kwace kudaɗen kuma wanda hakan bai dame shi ba akan yarda yake jin jikin sa a yanzu sosai ya fara fargabar abin da yake kokarin faruwa dashi a yau din fuskar Hajiya Layla da ta bayya a gareshi akanta ya diga ayar tambaya.
Kofar da aka turo aka shigo ne ya sanya shi tsinke zaren tunanin sa sosai yake bin kofar da kallo a daidai lokacin yayi arba da Alhaji Abdulwahaab suna kallon junansu ido cikin ido mamaki al'ajabi ya sake narkar dashi kau da kai yayi tare da runtse idanuwa yana mai tambayar kansa mai ya kawo Alhaji Abdulwahaab gidan sa a daidai wannan lokacin ganin abin yake yi kamar a mafarki ba gaskiya ba sai faman jan numfashi yake wanda yaji yana kokarin kwace masa.
A hankali ya shiga takowa tsakiyar falon yana dubansu su duka cikin wani irin yanayi musamman yarda ya ga Dr.Erena aciki abin ya bashi mamaki gefe ya koma ya tsaya yana duban Hajiya Layla da ita ma shi take duba.
"Ka zauna mana".
Ta fadi tana nuna masa kujera, gyaɗa kai yayi tare da zama bakin sa cike da tambayoyi masu yawan gaske amma ya rasa ta ina zai fara ko da yake akwai abin da yake hasashe akan faruwan haka...
Muryar Hajiya Layla ce ta katse masa tunanin da yake yi.
"Lokaci yayi sakon Malam Nata'ala zan isar kamar yarda ya bani shi amma bisa mamaki shi ya manta da waye ma Malam Nata'alar".
Ta karashe tana sakin wani mugun murmushi kafin ta mike kan kafafuwanta da hanzari ta shiga kai kawo a tsakar falon hannayenta goye a bayanta.
****
A hankali take jan motar cikin yanayi na fargaba da tsoron yanayin wajan haka kawai take jin zuciyarta na gargaɗin ta akan ta koma kar taje amma wani sashin na kara mata kwarin gwuiwar zuwa din runtse idanu tayi tana kara kurɗawa cikin dajin da tun da take a filin duniyar nan bata taba zaton akwai wannan dajin ba.
Tafiya tayi sosai har ta fara yanke tsammani da rabon samun abin da ta zo nema ji take yi kamar kwatancen da Areefa tayi mata ba haka bane domin ta fara sarewa da tafiyar nan da ta kwasa kamar wacce zata bar duniya.
Burki ta taka da sauri ganin uban tafiyar taki karewa gashi wani abun da take shirin gani ta baro surkukin daji amma nan kuma ta fara hango filin Allah kamar an share shi hakan ya fadar mata da gaba ba tare da ta karasa shiga filin ba don zuciyarta sosai ta tsoratar da ita akan ko wani mugun abun ne a shimfiɗe a wajan.
Shiru tayi tana tunano labarin da Areefa ta bata akan zuwan su gidan Malam Nata'ala sosai ta fara gano komai da sauri ta sakeyi wa motar key ta fizgeta bayan ta nemi tsari wajan Allah da ya kareta daga duk wani abun ƙi da yake tattare da wannan wajan ba ta gama wannan tunanin ba ta fara hango wani farin gida daga can tsakiyar filin wanda ya kasance shi kadai hakan ya tabbatar mata gidan kenan.
Tsayar da motar tayi gami da kasheta baki daya ta shiga kallon gidan yana yarda Areefa ta kwantata mata ba abin da ya sauya daga cikin sa mamaki ne ya cika ta dama a duniyar nan a irin wannan dajin har za a samu wanda zai iya rayuwa a cikinsa shi kadai ba tare da wani ba girgiza kai tayi gami da buɗe murfin motar ta fito a hankali ta fara takawa cikin yanayi na tsoro bayan ta rufe motar tana tafiya tana waiwaye don gabadaya tsigar jikinta ji take yi tana tashi kanta yayi mata nauyi sosai.
Gidan taga kamar yana sauyawa a idanuwanta tsoro na kara shigarta amma duk da hakan bata daina kusantar gidan ba a haka har ta isa kofar gidan a buɗe yake hakan ya bata damar shiga ba tare da wata fargaba ko tsoron da take ji zuciyarta na kawo mata ba lokaci guda taji duk wata fargaɓar na raguwa sosai.
A tsakar gidan ta tsaya tana mai kallon cikinsa komai tsaf-tsaf kamar gidan sabuwar amarya.
Daki guda ta hango wanda labule ke sake wajan ta nufa tun da ta tunkari wajan take jin wani wari na kawo wa hancinta farmaki da sauri ta buɗe jakartaa ta zaro farin hankicif ta toshe hancinta amma duk da hakan ba ta daina jin warin ba.
Hannunta daya ta saka ta buɗe labulan da sauri ta saki gami da ja da baya idanuwan ta a warwaje abin da ta gani yayi matukar faɗar mata da gaba nan ta shiga ambaton Allah da neman tsari sai da ta kwashe mintina kafun tayi kundunbalar sake buɗewa hango shi tayi kan buzu a takure sai ka rantse ba mutum bane a wajan fuskar nan tayi kaca-kaca da kasumba zallar fuskar tashi ba ka gane wa kafarsa kuwa guda daya sai faman wari take yi kana hango tsutsuni na yawo a cikinta.
Runtse idanu tayi lokaci guda taji wani tashin hankali ya ziyarce ta zuciyarta ta karye hawaye ya shiga zubo mata lokaci guda a hankali ta jingina da bango tana jin yarda kanta ke juyawa kamar zata zube a kasa numfashinta na sama da kasa.
"Baiwar Allah".
Kamar daga sama ta tsinkayo muryarsa wanda hakan yayi matukar bata mamaki jin muryarsa raɗau kamar ba wanda yake cikin mawuyacin hali ba dubansa ta shiga yi da buɗaɗɗun idanuwanta zuciyarta na tsalle da tsoro.
"Me ya shigo dake wajan nan kin san bala'in da ke cikin nan kuwa kinsan masifar dake tattare da wannan wajan kuwa kiyi wa kanki fada in ma wani abu ki ka zo nema to kiyi maza ki fice tun kafin wani abu ya same ki".
Kalamansa taji suna yi mata yawo a kwanya da sauri ta durkushe tana dubansa kafun daga bisa tayi kokarin yi masa sannu bai ansa ta ba illa kau da kai da yayi wani hayaki ne ta ga yana fitowa daga bangon dakin na hagu yana shawagi a tsakar dakin yana murɗewa hakan ba karamin kara rikita Hajiya Layla yayi ba da sauri ta fara ja da baya tana kokarin ficewa daga dakin.
"Na san abin da ke tafe dake kuma nayi murna sosai da kiƙa zo a daidai wannan lokacin Dr.Erena ko na san akan sa kiƙa zo nan ba zan boye miki ba na san na cuce Khairiyya a rayuwarta nayi dana sani domin tun daga kanta na fara fuskartar matsalolin rayuwa har zuwa wannan lokaci da nake wannan halin...".
Tari ne ya sarke shi wasu abubuwa su ka shiga zubowa daga bakin sa kamar tsutsotsi sai motsi suke yi Hajiya Layla gabadaya ta rikice ji tayi fitsar na kokarin kwace mata.
"Ki tashi ki tafi lokaci na nan zuwa kuma Dr.Erena shima sai ya dandani bala'in da nake ciki banta taba mugun aiki ba kamar yarda nake yi wa Dr.Erena shine mutumin da naƙe yi wa aiki wanda ni akaran kaina ina tsoro da fargaba in ina yin sa sannan ina kara jinjina rashin imani irin na Dr.Erena domin kuwa a duk sahun mutanan da nake yi wa aiki shine yafi kowa kawo mani mugun aiki".
Shiru yayi yana jan numfashi kafun ya sake fadin.
"yace zai yi aure ko kuma tsarin aikin da nayi masa babu zancen aure har gaban abada to wannan auren shi zai zama SILAR AJALI gareshi duk ranar da aka daura auren to tabbas shima yarda na zama shima haka zai zama yarinya ta shi ki tafi tun kafin wani abu ya same ki sannan karki sake ki hana Khairiyya aurensa ki bari a yi ko da na rana daya ne na tabbata daga wannan ranar salo zai sauya".
Mamaki ne ya cika ta zuciyarta na kara karyewa da tashin hankali mamaki take yi sosai da maganganun Malam Nata'ala tun da take a rayuwarta yau ne rana ta farko da ta ji ta tsani duniyar nan gabadaya taji ta tsani zama cikin ta...
"Da hannu na nake amfani da ayar Allah tsarkakankiya domin biya masa bukata ina amfani da jinnu a nan Dr.Erena ya sha cin naman jarirai wanda aka dafa su da ayar Allah da wani suddabaru na jinnu ya sha zuwa da mace mai dauke da ciki wanda bai haura wata biyar ba in saka jinnu su barar dashi tare da yi masa magani don kawai yana so ya zama daya daga cikin ATTAJIRAN DUNIYA nayi da nasani nayi kaico da rayuwata da ta kasance a haka na san ko a lahira bani da wani amfani hukunci na mai girma ne domin tawa ta kare amma ki sani yarda na shiga bala'i shima sai ya shiga nan kusa kadan Sharri dan sako ne ya na nan tafe gareshi".
Yana gaman fadin haka nan ya shiga tari wannan abubuwan masu kama da tsutsotsi na sake zubowa kamar an buɗe wani matattarar su tana kallo wannan hayakin ya shiga wuce ta cikin hancin sa jikinsa lokaci guda ya shiga canzawa yana baƙi gami da ruwan toka kansa da duk wani gashi dake jinsa yana canzawa zuwa fari gami da fidda wani hayaki da sauri ta rarrafa ta fice daga daki gabadaya ta gama rikicewa ta fice daga hayyacin ta tashin hankalinta ya kara ninkuwa duniyar gabadaya tana tsoron ta cikin yanayi na ɓarin jiki da rashin hayyaci ta fice daga gidan idanuwanta a rufe kawai jefa kafafuwanta take yi har Allah ya kaita inda motarta take..
****
Hawaye ne ke zuba sosai a idanuwanta zuciyarta na kara karyewa bata so tuna wannan labarin ba amma ba yarda zata yi domin ta gama tsorata da halin da ta tsinci Malam Nata'ala a ciki wani tsoron Allah take ji yana samun gurbi a zuciyarta duniyar take ji gabadaya ta fice mata daga rai duban sa tayi kafun ta dauke hawayen da suke zuba mata.
"nasan yanzu zaka tuna labarin da ya shuɗe sama da shekaru ashirin da doriya a duniyar ka na san zaka tuna yarinyar da ka lalata mata rayuwa yarinyar da kayi amfani da ita don kawai cikar burin ka Khairiyya da kasani to ita ce wannan Areefa da ka aura da sunan matar aure na san kuma zaka tuna waye Malam Nata'ala".
Kuka ne ya ci karfin ta da sauri ta toshe bakinta da hannayenta tana duban Areefa wacce gabadaya kukan take yi da shassheka kamar numfashin ta zai dauke.
Wani irin tari ne suka ji ya sarke dashi hannunsa daya a saitin Areefa idanuwansa lokaci guda suka shiga sauyawa fizga yaji numfashin sa nayi kamar ransa zai fita gabadaya ya gama rikicewa da labarin da yaji domin ya manta da wani mutum wai shi Malam Nata'ala..
*Kamala Minna*😍😍