RUBUTACCIYAR WAKAR SO SANADI NA SADIQ GATAN NAIJA

RUBUTATTUN WAKAR SOYAYYA DA DADI

Sunan Waka: Soyayya Da Dadi

Rubutawa: Sadiq Gatan Naija

Tacewa: Haiman  Raees

* Soyayya Da Dadi Take, Yau Na Samu Mai Tarbiyya.

* Kece Naggani Na Rike, Daure Karki Ban Gajiya.

* Taho Zo Kimin Agaji, Kece Zan Kira Gimbiya.

* Dake Zaniyo Fahari, Soyayyar Ki a Raina Tayi Ambaliya.

* Kyawu Naki Wa 'Yan Kano, Hada Ma Da 'Yan Zariya.

* Bayanan Ki Sun Yi Mini, Sune Zaniyo Bibiya.

* Aure Namu In Za'a Yi, Sadakin Ki Nai Tariya.

* Gurin Baba Harma Umma, Aure Naki Zan Tambaya.

* Sumin Lamuni In Iso, Domin Kin Shige Zuciya.

* Ina Ma Ace Ni Da Ke, Hali Namu Zai Zo Daya.

* Sirrin Zuci Ke Fallatsa, Cikin Rai Dama Jijiya.

* Ashe In Babu Ke, Ni Gara Ma To Ni Zan Bar Duniya.

* Dabi'un Ki Ke Sawa, Ana Ta Yimin
Zolaya.

* Abokai Dama 'Yan Uwa Sunce Aure Naki Nai Anniya.

* Ni Dai Kar Ki Manta Dani, Akan So Kimin Shariya.

* Idan Aka Ce Kin Tafi, Komai Nawa
Yau Zai Tsaya.

* Burina Ki Zo Min Gida, Ki Girka
Minni  'Yar Taliya.

* Zance Naki In Kimmini, Hada Min Da 'Yar Qafiya.

* Hakan Ke Saka Nai Zuru, Kamar
Wanda Bai Lafiya.

* Komai Za'a Ce Min Nayi Ni Dai Zani Yo Juriya.

* Sai Dai Kaf  Ayau, Na Gano Baki Naki Zan Toshiya.

* Amma Ni Kiban Lokaci, Na Zo In
Zam Mai Shiriya.

* Magauta Suna Kai Hari, Wai Don
Kin  Yimin Naciya.

* Diya Ga Ki  'Yar Fara, San Nan Ga Ki Zinariya.

* Tsabar Kyau Dama Kwarjini, Kamar
Yar Kasar Indiya.

* Mai Tsafta Da Kyawun Hali, Gida Namu Mui Zauniya.

* Yara Namu In Sun Iso, Karatun Su Ba Magiya.

* Furar So Ki Damo Min,  Ko Rai Zaya Dan Sanyaya.

* Kece 'Ya Guda Na Aje, Ba Zancen Nayo Kishiya.

* Duk Mai Son Yasha 'Yar Zuma, Lallai sai yasa Amiya.

* Karamci A So Kim Mini, Toni zan
Dado  Godiya.

* Mai Yin So Ya Bar Yin Fahari, In Har Yaki Zai Sha Wuya.

* Hannuna Ki Kama Mini, Idan Har Muna Tafiya.

* Karatun So Da Fadi Yake, Ina So Muje Tsangaya.

* Akan Son Ki Ni Ban Gudu, Rana Ko Zuwa Safiya.

* Kija Min Akala Muje Sirrin Zuci Nai Ajiya.

* Soyayyar Mu Wa Zai Raba, Idan Za'a So Gaskiya.

* Har Mun Yo Kamanni Guda, Silar So Dake Tun Jiya.

* Batun Son Ki Na Karfafa, Yana Nan Cikin Zuciya.

* Har Abada Mu Zauna Dake, Sai
Mutuwa Cikin Duniya.

Daga

Sadiq Usman Gatan Naija
(Dan Mama)

07065873176

1 Comments

Post a Comment