SHARHIN LITTAFIN TEKUN LABARAI

TEKUN LABARAI
Na Danladi Haruna
Kaifin hankali da basirar yaro Kabiru suka sa Sarki Shamsuddini ya jinkirta zartar da hukuncin kisa bisa laifin da ake zargin ya aikata. A gefe guda kuma Wazirai goma sun kasa zaune da tsaye a burinsu na ganin bayan wannan saurayi. To amma gaggawarsu ta bi iska a yayin da gaskiya ta bayyana...
Littafin Tekun Labarai daya ne tamkar dubu, littafi ne da ya fito a daidai loton da ake da tsananin bukatar irinsa. Littafi ne da yake kunshe da gajerun labarai masu nishadantarwa da fadakarwa.
Ga masoya littafin Magana Jari Ce ta 1, 2 da 3, zan iya cewa, to ga ci gaban Magana Jari Ce ta 4. Domin wannan littafin da kuma littafin Magana Jari Ce tamkar Danjuma ne da Danjumai a tsari da kuma zubin labarai masu armashi.
Bugu da kari, a cikin wannan littafi an kiyaye ka'idojin rubutun Hausa, ta yadda hatta dalibai masu nazarin harshen Hausa za su iya amfani da shi wajen kyautata ka'idojin rubutunsu.
Mawallafin littafin, Malam Danladi Haruna, mamba ne a cikin Kungiyar Eidtocin Hausa, kuma yana daya daga cikin marubutan da suka zauna suka fassare littafin DARE DUBU DA DAYA daga Larabci zuwa Hausa. Don haka za mu iya cewa a bangaren kiyaye ka'idojin rubutu, da gogewa a kan sha'anin rubutu, masu abin ne da abinsu, wai dan kura da kallabin tumbi.
Ku nema ku karanta, littafin ya shiga kasuwa tun jiya Laraba - 26/08/2015. Wadanda ke cikin Kano za su iya samun littafin a kowane kantin sayar da littattafai da ke kusa da su. Sannu a hankali kuma littafin zai karade kowace kusurwa ta kasar nan har ma da makwabta.
Bukar Mada. — with Danladi Haruna

Post a Comment (0)