TAKAITACCEN TARIHIN JARUMA ANUSHKA SHARMA

TAKAITACCEN TARIHIN JARUMA ANUSHKA SHARMA
Anushka Sharma jaumar Fim ce wacce take fitowa a cikin Fina Finan India Wadanda suke fitowa karkashin Masana'antar Fina Finai ta Bollywood.
Bayan shirin fim, har wayau jaumar tana aiki a matsayin Furodusa tare da yin tallan hajoji a Gidajen talbijin.
Ranar Haihuwa: 1 May 1988 (shekara 29)
Inda aka haife ta: Ayodhya , Uttar Pradesh , India
Kasa: India
Jami'ar Da Tayi: Bangalore University
Sana'ar Ta: Jarumar Fim, Furodusa, Kwararriyar Tela
Shekarar: 2007
Mijin Ta: Virat Kohli
Dan Uwanta: Karnesh Sharma
Anushka Sharma ta fara Fim ne tare da Jarumi Shah Rukh Khan a cikin wani Kasaitaccen Fim mai suna Rab Ne Bana Di Jodi a Shekara ta 2008, Wanda da wannan Fim Din ne ta samu Damar shiga Gasar Jarumar Jarumai Filmfare Award.
Jarumar ta kara samun Daukaka ne Yayinda ta fito a cikin Fina Finan Kamfanin Yash Raj Films guda biyu wato Baaja Baaraat (2010) da kuma Jab Tak Hai Jaan (2012); inda har ta samu kyautar  Best Supporting Actress award ta Filmfare da Jab Tak Hai Jaan. Sannan ta zo ta samu gagarumar nasara da Fim dinta wanda suka fito a ciki tare da Jarumi Aamir Khan Wato PK (2014), sai Kuma Fim Din da ta fito a matsayin 'Yar Dambe wato Sultan (2016), dukkan wadannan Fina Finai sun sami Karbuwa sosai ba kadan ba wanda hakan ya sa ita ma Jarumar ta karbu a wajen' yan kallo da ma sauran masu Shirya Fina Finai.
Bugu da kari Anushka Sharma Wakiliya ce ta hajoji da dama wadanda ta talla ta, kuma har ta fitar da salon irin dinkunan ta na kanta domin sauran mata. Haka kuma Jarumar tana daga cikin Jaruman Fina Finan India Wadanda suke bada gudummawa ga wadanda Annoba ta Afkawa, da kuma kokarin ganin an samu daidai to a tsakanin maza da mata da kuma kiyaye Hakkin Dambobi. Sannan ita da dan uwanta Karnesh ne suka kafa Kamfanin shirya Fina Finai mai suna Clean Slate Films .
Mahaifin ta Kanel Ajay Kumar Sharma, Soja ne, mahaifiyar ta mai suna Ashima Sharma,ita kuma 'Yar aikin gida ce. Mahaifin ta dan asalin is Uttar Pradesh ne, Yayinda mahaifiyar ta kuma' yar Garhwali ce.
Yayanta Karnesh Sharma kuma Furodusa ne, wanda shi ma yayi aiki a karkashin sojin ruwa.
Anushka Sharma tasha fadin cewa ta ji dadi matuka da ta kasance 'Ya a wajen soja domin hakan ya taimaka mata sosai wajen saita rayuwar ta yadda ta dace. A wata Zantawa ma da akai da ita a 2012 cewa tayi "Ina Matukar Alfahari da Kasancewa ta' yar soja fiye da Kasancewa ta Jarumar Fim".
Anushka Sharma ta taso ne a garin Bangalore. Tayi karatun ta ne a makarantar Sojoji, kuma ta samu digiri dinta ne a Fannin ARTS Daga Kwalejin Mount Carmel College .
Da Farko tayi tunanin fara Sana'a ne a Fannin Tallace-Tallace ko kuma aikin Jarida, kuma bata da wani Burin yin shirin fim a wancan lokacin.
Bayan ta Kammala karatu ne sai ta koma Mumbaai domin fara aikin Tallace-Tallace. A nan ne ta shiga Elite Model Management, inda ta sami horarwa a hannun Prasad Bidapa.
Anushka Sharma ta fara fitowa a Fim Din ne a shekarar 2008, cikin wani Fim
Aditya Chopra mai suna Rab Ne Bana Di Jodi tare da Jarumi Shah Rukh Khan. Bayan ta ci Jarabawar da suka yi mata, sai suka yi Yarjejeniyar yin Fina Finai Uku tare da ita. Da wannan Fim ne ta sami damar shiga Gasar Filmfare.
Bayan shekaru biyu da yin Rab Ne Bana Di Jodi, Anushka Sharma ta sake fitowa a matsayin Jaruma a cikin Fim Din Badmaash Company,
Wanda
Parmeet Sethi ya bada umurni kuma suka fito tare da Shahid Kapoor , Vir Das da kuma Meiyang Chang .
Fim Din ya samu Karbuwa da kuma rashin Karbuwa a wajen 'yan kallo da kuma masu sharhin Fina Finai.
A shekara ta 2010 ne Jaruma Anushka Sharma ta kammala Kwantiraginta na Fina Finai uku da tayi da Yash Raj Films ta hanyar fitowa a cikin Fim Din Baaja Baaraat, Wanda Maneesh Sharma ya bada Umurni kuma suka fito a ciki tare da sabon Jarumi wato
Ranveer Singh.
Saboda ta shiryawa fitowa a cikin Fim Din, sai da Jarumar ta koyi yaren Punjabi wanda kuma ta ce shi ne Abu mafi Wahalarwa tattare da aikin ta a cikin Fim Din.
Fim Din Anushka Sharma na farko wanda ba Kamfanin Yash Raj Films bane ya dauki nauyi shi ne Patiala House (2011), wanda ya bada umurni Nikhil Advani suka kuma fito tare da
Akshay Kumar a cikin Fim Din
A shekara ta 2012, Anushka Sharma ta sake fitowa tare da Jarumi Shah Rukh Khan Da
Katrina Kaif a cikin Fim Din Yash Chopra na karshe wato Jab Tak Hai Jaan.
Fim Din ta na gaba shi ne Fim Din Vishal Bhardwaj mai suna Matru Ki Bijlee Ka Mandola (2013), a Fim Din sun fito ne tare da Pankaj Kapur, Imran Khan Da kuma Shabana Azmi.
Jarumar ta kuma fito a cikin Fim Din PK tare da Aamir Khan wanda shima ya kawo kudi kimanin Dala Miliyan 110 a duniya gaba daya.
Anushka Sharma ta bude Kamfanin shirya Fina Finai mai suna
Clean Slate Films , Fim Din wannan Kamfani na farko shi ne NH10 (2015), inda ta fito a matsayin Jarumar Fim Din.
Fim Din ta na gaba shi ne Fim Din In Anurag Kashyap mai suna Bombay Velvet (2015), sun fito ne tare da Ranbir Kapoor da kuma Karan Johar.
Haka kuma a 2015 din dai, Anushka Sharma ta fito a cikin Fim Din Zoya Akhtar mai suna Dil Dhadakne Do , wanda ya kunshi Jarumai irin su Anil Kapoor , Shefali Shah, Priyanka Chopra da Ranveer Singh.
Anushka Sharma ta fito a Fim Din ta na gaba ne Fim Din Yash Raj Films wato Sultan (2016) inda ta fito tare da Jarumi Salman Khan. Da farko tayi tunanin kin Amsar Fim Din saboda bata da jiki irin na 'yan dambe. Kafin a fara Fim Din, sai da ta samu horo na tsawon sati shida, kuma sai da ta koyi iya magana da Harshen Haryanvi sannan kuma ta zanta da wasu' yan wasan Dambe daban daban daga India. Shima wannan Fim ya samu Karbuwa sosai kuma ya kawo kudi masu yawa a akwatin Kasuwancin Fina Finan India.
Jaruma Anushka Sharma ta sake samun wata gagarumar nasara Yayinda ta fito a cikin Fim Din Ae Dil Hai Mushkil wanda Karan Johar ya bada umurni inda suka fito tare da a Rabir Kapoor da Aishwarya Rai .
Shima wannan Fim Din ya samu Karbuwa sosai domin ya kawo kudi kimanin Dala Miliyan 31.
Anushka Sharma ta fara shekarar 2017 ne da Fim Din Phillauri , inda ta fito tare da Jarumi Suraj Sharma da Diljit Dosanjh.
Bayan fitowa da tayi a cikin Fim Din, da kuma daukar nauyi, ta kuma yi Waka a cikin Fim Din.
Fim Din ta na gaba kuma shi ne Jab Harry Met Sejal tare da Shah Rukh Khan karkashin Jagoranci Imtiaz Ali. Sai dai duk wadannan Fina Finan basu wani tsinana wani abun Arziki ba a akwatin Kasuwancin Fina Finan India.
Har izuwa 2017, Anushka Sharma tana kan shirya Fim Din ta na gaba mai suna Pari tare da
Parambrata Chatterjee.
Sannan ta amince da fitowa a Fim Din Navdeep Singh mai suna Kaneda , tare da Arjun Kapoor da Diljit Dosanjh, sannan ta fara aikin Fim Din Rajkumar Hirani wanda zai yi akan Tarihin Jarumi Sanjay Dutt,bugu da kari, zata fito a cikin Fim Din Shah Rukh Khan Katrina Kaif wanda Anand L. Zai bada umurni mai suna Zero. Har wayau dai, Jarumar zata fito tare da Jarumi Varun Dhawan a cikin wani Fim mai suna Sui Dhaaga wanda Sharat Katariya zai bada umurni.
A shekara ta 2014 an ruwaito cewa jarumar tana neman shaidar Master Degree a Fannin Tsumi da tanadi wato economics. Sannan jarumar ta fara Kauracewa cin duk wani dangi na nama a 2015.
Jarumar tayi fama da lalurar ZUMUDI wacce har izuwa yanzu bata gama Warkewa daga gare ta ba.
Jaruma Anushka Sharma 'yar Addinin Hindu ne, kuma da ita da ahalin ta duk Mabiyan Anant Dham Atmabodh Ashram a Haridwar .
Jarumar ta auri tsohon Masoyin ta Virat Kohli a ranar 11 December 2017 a Italy.

Post a Comment (0)