TAKAITACCEN TARIHIN JARUMI SALMAN KHAN

TAKAITACCEN TARIHIN JARUMI SALMAN KHAN
Salman Khan Jarumin Fim Din India ne wanda yake fitowa a Fina Finan Bollywood, kuma Mawaki ne, Furodusa ne Sannan Mai gabatar da Shirye Shirye ne a Gidajen Talbijin. Masana sunyi Ittifakin cewa Salman Khan Shi ne jarumin da ya fi kowa samun nasara a Fannin Kasuwancin Fina Finan sa.
Cikakken Sunan Shi : Abdul Rashid Salim Salman Khan
Ranar Haihuwar Sa: 27 December 1965 (shekara52)
Wurin Da Aka Haife Shi: Indore, Madhya Pradesh , India
Wurin Zaman Sa: Mumbai , Maharashtra, India
Kasarsa : India
Sana'oin Sa: Jarumin Fim • Furodusa • Mawaki • Mai gabatar da Shiri
Shekarar Da Ya fara 1988
Mahaifin Sa: Salim Khan
Mahaifiyar Sa: Sushila Charak
Salman Khan babban DA ne ga tsohon Marubucin Fina Finan India Salim Khan , Salman Khan ya fara Sana'ar Fim ne ta hanyar fitowa a matsayin mai takewa Jarumi baya a cikin Fim Din Biwi Ho To Aisi (1988), sannan jarumin ya samu Karbuwa sosai ne ta hanyar jan Ragamar Fim Din Sooraj Barjatya mai suna Maine Pyar Kiya (1989).daganan Salman Khan ya ci gaba da samun sa'a da Nasarori a da Karbuwa a wurin jama'a ta hanyar fitowa a cikin Manya Manyan Fina Finai irin su Hum Aapke Hain Koun..! (1994), Karan Arjun (1995),
Biwi No.1 (1999),
Hum Saath-Saath Hain (1999) da sauran su.
Sakamakon Kokarin da yayi a cikin Fim Din Kuch Kuch Hota Hai (1998), jarumin ya samu lambar Yabo Filmfare Award a matsayin Best Supporting Actor . Bayan samun tangarda da yayi a harkar tasa da yayi a Shekarun 2000, Salman Khan ya samu Mashahuriyar Daukaka a Tsakankanin Shekarun 2010s ta hanyar fitowa a cikin wasu Kasaitattun Fina Finai irin su Dabangg (2010), Ready (2011), Bodyguard (2011). Ek Tha Tiger (2012),
Dabangg 2 (2012), Kick (2014), Prem Ratan Dhan Payo (2015), Bajrangi Bhaijaan (2015), Sultan (2016) da kuma
Tiger Zinda Hai (2017), duk wadannan Fina Finan sai da suka zama cikin Fina Finan India da suka fi kawo kudi a akwatin Kasuwancin Fina Finan India. Fina Finai 12 kawai da jarumin yayi sun kawo kudi kimanin Dala Miliyan 16 (US$16 million).
Salman Khan ne Kadai Jarumin da ya taba fitowa a cikin Fina Finan da suka fi kowane Fim kawo kudi na tsawon shekaru 10 a Tarihin Bollywood, kuma Shi ne Jarumin da yafi kowane Jarumi tsada wajen biyan kudin aikin Fim kamar yadda Forbes ta fada a rahoton ta na 2014.
Jarumi Salman Khan yana taimakon mutane sosai, son taimakon nasa ne ma yasa ya kafa kungiyar taimakawa nakasassu da Marayu mai suna Being Human . Rayuwar Jarumi Salman Khan rayuwa ce mai cike da Cakwakiya, Kasancewar shi mutumin Kirki ne Kuma mutumin Banza a lokaci guda kamar yadda masu bayani suka fada. Hakan yasa wasu suke yi masa munanan Fenti a duk lokacin da suka samu Damar yin hakan, Abu dai har yakai inda ya kai inda har Lakabi 'yan adawarsa suke yi masa da "DAN GIDAN MATSALA", sai dai kuma har izuwa yau, Salman Khan na daya daga cikin Jaruman Fina Finan India da suka fi kowa samun soyayya ta fitar hankali daga wajen' yan kallo.
Idan za'a yi maganar Irin Cakwakiyar dake tattare da rayuwar Salman Khan ne, to za'a kwana ba'a gama ba, Misali: akwai labarin Tsatstsamar alakar su da Aishwarya Rai ,Harbin da Yayiwa dabbar da bai kamata ba (wacce wasu suke bauta mata) , buge wasu da yayi da mota har daya daga cikin su ya mutu, sabanin da suka samu da Arijith Singh da dai sauransu.
Jarumin yana da Kamfanoni guda biyu Salman Khan Being Human Production (SKBHP) da
Salman Khan Films (SKF).
Mahaifiyar sa Sushila Charak ta canja sunan ta daga baya izuwa Salma Khan, Zuri'ar sa ta wajen Uba 'yan asalin Pathan ne daga kasar da aka sani a yanzu da suna Afghanistan, hijra sukayi daga can suka zo Indore, Madhya Pradesh a a Tsakankanin shekarun 1800s.
Mahaifiyar sa kuma' yar Maharashtra ce ,Mahaifin ta Baldev Singh Charak ya fito ne daga comes from
Jammu-Kashmir Yayinda mahaifiyar ta itama ta fito daga Maharashtra .
Akwai matar baban Jarumi Salman Khan mai suna Helen wacce ita kuma tsohuwar Jarumar Fim ce. Yana da 'Yan Uwa maza guda biyu, Arbaaz Khan wanda ya auri
Malaika Arora Khan , sai Sohail Khan; sannan yana da kanne mata guda biyu Alvira Khan Agnihotri , wacce ta auri Jarumi kuma Darakta Atul Agnihotri da kuma Arpita wacce ba Salim bane Mahaifin ta, sun maida ita 'Ya ce kawai.
Salman ya kammala karatun sa ne a St. Stanislaus High School dake Bandra ,
Mumbai , kuma Arbaaz da Sohail ma a nan suka yi karatun.
Yayi karatu a The Scindia School , na wasu shekaru a Farkon rayuwar sa tare da Arbaaz. Da ya fara zuwa St. Xavier's College dake Mumbai amma sai ya daina zuwa. dropped out.
Salman Khan ya fara Fim ne ta hanyar fitowa a matsayin mai takewa babban Jarumi baya a shekara ta 1988 a cikin Fim Din
Biwi Ho To Aisi duk da cewa wani ne yayi muryar sa. Fim Din sa na farko a matsayin Jarumi a Bollywood shi ne Maine Pyar Kiya (1989), daya daga cikin Fina Finan India Wadanda Suka FI kawo kudi sama da kowanne.
Da Fim Din ne ya fara samun damar shiga Gasar lambobin Yabo na Filmfare Best Actor.
A 1990 Fim daya Salman Khan yayi, shi ne Baaghi: A Rebel for Love,shima wannan Fim ya kawo kudi sosai, sannan yayi Fina Finai guda uku a 1991,
Patthar Ke Phool, Sanam Bewafa , da
Kurbaan wadanda suma ba laifi sun taka Rawar gani. Kuma a wannan shekarar ne a fito a cikin wani Fim tare da with Sanjay Dutt da Madhuri Dixit mai suna
Saajan . Wannan Fim ya samu Yabo sosai kuma ya kawo kudi sosai.
Duk da wannan gagarumar nasara da ya samu, kusan duk Fina Finan sa na 1992–1993 sun fadi a harkar Kasuwancin Fina Finan India.
A shekara ta 1994, Salman Khan ya fito a cikin Fim Din Rajkumar Santoshi Andaz Apna Apna, tare da Aamir Khan . Duk da cewa Fim Din bai kawo kudi sosai ba, ya samu Yabo sosai. Ya dawo da samun nasarar sa ne da Fim Din Sooraj Barjatya mai suna Hum Aapke Hain Koun..! Shi da Madhuri Dixit . Fim Din ya samu lambobin Yabo na Filmfare Awards guda uku Best Film, Best Director da kuma Best Actress. Sannan Fim Din ya samu lambar Yabo ta kasa wato National Award a matsayin Fim Din da yafi kowane Fim samun Karbuwa a wannan shekarar. Fim Din ya kawo kudi kimanin Dala Miliyan 21 a duniya baki daya (US$21 million).
Wannan Fim sai da yayi shekara bakwai yana kan matsayin Fim Din da yafi kowane Fim kawo kudi ba tare da an buge shi ba. A shekara ta 1995 Salman Khan ya fito a cikin Fim Din Rakesh Roshan mai suna Karan Arjun tare da Shah Rukh Khan. Wannan Fim shi ne ya zama Fim na biyu da yafi kowane Fim kawo kudi a wannan shekarar, kuma kokarin da jarumin yayi a Fim Din yasa ya sake samun damar shiga Gasar jarumin Jarumai na Filmfare.
A shekara ta 1996, Salman Khan ya fito a cikin Fina Finai biyu ne, Khamoshi: The Musical, wanda ya fadi warwas a akwatin Kasuwancin Fina Finan India sai kuma Jeet . Haka kuma ya sake fitar da Fina Finai biyu a shekara ta 1997: Judwaa da Auzaar .
Judwaa ya samu Karbuwa sosai Yayinda Auzaar shima ya dan tabuka.
Salman Khan ya fito a cikin Fina Finai 5 a shekara ta 1998,Pyaar Kiya To Darna Kya tare da Kajol ,Jab Pyaar Kisise Hota Hai, sannan ya kare shekarar da fitowa ta musamman a cikin Fim Din Kuch Kuch Hota Hai wanda a Sanadiyyar hakan ya samu Damar shiga Gasar
Filmfare Award under a matsayin Best Supporting Actor category.
A shekara ta 1999, Salman Khan ya fito a cikin Fina Finai uku ne,
Hum Saath-Saath Hain,Biwi No.1 , da kuma Hum Dil De Chuke Sanam tare da
Aishwarya Rai da Ajay Devgan, shima wannan Fim ya bashi damar shiga Gasar Filmfare a matsayin Best Actor kuma Fim Din ya samu Karbuwa sosai.
A 2000, Salman Khan ya fito a cikin Fina Finai biyu
Har Dil Jo Pyar Karega da Chori Chori Chupke Chupke.
Sannan a 2002 ya fito a cikin Hum Tumhare Hain Sanam da
Tere Naam a (2003). Masana sun ce Salman Khan bai taba yin Nagartaccen wasan Kwaikwayo irin Tere Naam ba. Daga nan ne fa Salman ya balle da yin Fina Finai masu kawo kudi sosai irin su Mujhse Shaadi Karogi (2004) dayNo Entry (2005) .
Fina Finan sa na 2006 sun hada da Jaan-E-Mann da Baabul , sai dai duk sun fadi a akwatin Kasuwancin Fina Finan India.
Salman Khan ya fara shekara ta 2007 ne da Fina Finai irin su Salaam E Ishq, sai
Partner. Sannan jarumin ya fito a cikin wani Fim Din Hollywood mai suna Marigold: An Adventure in India. Jarumin ya fito a cikin Fina Finai uku 2008, amma duk basu tabuka abun Arziki ba.
Daga nan ne Salman Khan ya Jagoranci shirin wasanni wato game show mai taken 10 Ka Dum kashi na biyu a 2009, wannan shiri yayi nasara fiye ma da na Farkon, domin masana sunce wannan shiri shi ne ya taimakawa Sony Entertainment suka dawo da Martabar su a matsayin Kamfani na uku da yafi kowane Kamfani a Fannin Shirye Shirye a India.
2009 shekara ce da ta zama shekarar nasara wa Jarumi Salman Khan, domin daga wannan shekarar ce Fina Finan sa suka ci gaba da samun Karbuwa wacce har yanzu bata sauya mai ba. Farko dai shi ne Fim Din Wanted ,Wanda Prabhu Deva ya bada umurni, wannan Fim ya kawo kudi na ban mamaki, daga nan sai Main Aurr Mrs Khanna da London Dreams .
Wadannan Fina Finai sun samu rashin Yabo da rashin Karbuwa har ake tunanin nasarar Salman Khan zata koma gidan jiya, amma sai 2010 ta ce musu yanzu aka fara.
Fim Din da ya fara fitarwa a 2010 shi ne Veer, sannan ya saki Dabangg a ranar Eid, 10 Satumba 2010. Wannan Fim yayi kyau sosai kuma ya samu Yabo da Karbuwa ta yadda sai da ya kusa share duk wani Tarihin da wani Fim Din India ya taba kafawa a wancan lokacin, domin a kalla Fim Din ya kawo kudi kimanin Crore Miliyan ₹808.7
Fim Din sa na farko a 2011 shi ne Ready, sannan sai Bodyguard , duk wadannan Fina Finan sun karbu kuma sun kawo kudi suma sosai. A 2012 Salman Khan ya saki Ek Tha Tiger wanda suka fito tare da tsohuwar budurwarsa a ciki wato
Katrina Kaif . Fim Dinsa na biyu a 2012 shi ne Dabangg 2 , duka wadannan Fina Finan sun kafa manya manyan Tarihai a India.
Daga nan jarumin ya huta na tsawon shekara daya. A 2014 ya saki Jai Ho inda ya fito tare da Daisy Shah. Daga nan sai Kick, a 2015 kuma Bajrangi Bhaijaan, sai kuma Prem Ratan Dhan Payo , a 2016 kuma ya saki Sultan.
A 2017, Salman Khan ya fito a Fina Finai biyu ne
Tubelight tare da dan Uwansa Sohail Khan, sai dai Fim Din bai kawo kudin kirki ba duk da kyan da yayi. Fim dinsa na gaba shi ne Tiger Zinda Hai , ci gaban Ek Tha Tiger. Wannan Fim ya kawo kudade masu yawa sosai.
Ana sa ran Jarumin zai fitar da Kick 2 a bikin KIRSIMETIN 2019.
Jarumin ya kafa Kamfanin sa na kansa a 2011 mai taken SKBH Productions (Salman Khan Being Human Productions). Duk kudaden da aka samu daga Fina Finai ana zuba su ne a cikin Asusun kungiyar taimakon da ya kafa mai suna
Jarumin ya sake bude wani sabon Kamfanin a 2014 mai suna SKF (Salman Khan Films ).y
A shekara ta 2008, Salman Khan ya Jagoranci shirin 10 Ka Dum . Shirin ya karbu sosai domin har saida ya zamo na daya a India. Sannan ya sake Jagorantar shirin a shekara ta 2009 wanda a Sanadiyyar hakan ya samu lashe Gasar Best Anchor Award a 2008 day 2009. A 2010 kuma Salman Khan ya Jagoranci Bigg Boss 4 . Shima wannan shirin ya karbu fiye da tunani.
Salman Khan ya taimaki mutane da dama a Masana'antar Fina Finai ta India, Misali, shi ne ya fara Taimakawa Hrithik Roshan da Arjun Kapoor wajen samun Horasawar da ya taimakawa jikin su a Farkon tashin su. Saawan Kumar Tak, Daraktan Sanam Bewafa , yasamu taimakon jarumin sosai Yayinda yake bada umurnin Saawan... The Love Season kuma duk a kyauta.
Salman Khan ne ya bada Shawarar a dinga yin aiki da makada irin su Himesh Reshammiya da Sajid–Wajid. Shi ne ya Karfafawa Sanjay Leela Bhansali Guiwa kan yayi Fim Din Khamoshi: The Musical da Hum Dil De Chuke Sanam . Shi ne ya taimaki Govinda Yayinda yake gab da faduwa ta hanyar bashi aiki a Fim Din Partner . Har wayau Salman Khan ne ya bada shawarar Mohnish Bahl wa Sooraj Barjatya akan Fim Din Maine Pyar Kiya da kuma Baaghi: A Rebel.
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Infohaiman999@gmail.com

Post a Comment (0)