Tarihi: HAMZA ALMUSTAPHA YA FALLASA YADDA TSOHON SHUGABAN KASA SANI ABACHA YA MUTU.

HAMZA AL'MUSTAPHA YA FALLASA YADDA TSOHON SHUGABAN KASA SANI ABACHA YA MUTU.
Tsohon mai tsaron, tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji Sani Abacha, Manjo Hamza Al'mustapha ya bayyana yadda shugaban ya rasa ran shi.
Hamza Al'mustapha ya karyata batun cewar wai Abacha Kwayar Tufa (Apple) yaci ya mutu.
Yace tun daga ranar wata lahadi bakwai ga wata shida na shekarar alib dubu daya da Dari Tara da chasa'in da takwas 7-6-1998 lokacin da Abacha ya gaisa da wani daga cikin masu tsaron shugaban kasar Palestine Yasaer Arafat a filin jirgin sama dake babban birnin tarayya hada hannun su keda wuya daga lokacin yanayin shugaban ya chanza.
Washe gari likitan shi yazo ya duba shi harya mishi Allura ya kuma shawarce shi kan ya samu ya kwanta yadan huta, da misalin karfe 9pm baki suka fara shigowa Wanda ya shigo daga karshe shine Ganaral Jeremiah Timbunt Usteni wanda shine ministan Abuja a lokacin sunyi hira har karfe 3:35am na dare, banyi kasa a gwiwa na sai na bayyana ma ADC.
Da misalin karfe biyar 5am na Asuba sai daya daga cikin masu tsaron gidan shugaban ya rugo a guje gidana yace Abacha yana cikin wani yanayi mai ban tsoro saboda haka in zo cikin gaggawa, daga wannan lokacin sai nayi tunanin ko dai Juyin mulki aka shirya mana ne? Sai nace ma Iyali na taje ta dauke ma Sojan hanli tace ya jira ni, ni kuma sai nabi ta baya na je inda shugaban yake; ina zuwa sai na tarar yana Huci, numfashin shi sama-sama, a lokacin bazai yiwu in taba shi ba kamar yadda tsarin dokar aikin mu yake.
Banyi kasa a Gwiwa ba sai naja da baya na kame na kwala mishi kira Sani Abacha ka bani dama in taba ka, sau biyu ina yin haka amma baice mu komai ba.
Daga nan sai na gane akwai babbar matsala sosai nan da nan sai na gayyaci babban likitan shi Dakta Wali ya bayyana a kusan mintuna Takwas 8 take ya yima shugaba Abacha Allurori guda biyu daya a kirji daya kuma a kusa da wuya; daga bisani Likitan ya bayyana mun cewa gaskiya sai dai muyi hakuri amma Abacha ya ruga mu gidan gaskiya.
Daga wannan lokacin na Umarci Wali ya jirani inje gidana don shirya ma dukkan matsala da zan iya fuskanta saboda rasuwar shugaban.
Babu wata magana kan cewa Abacha yaci guba Apple shi yasa ya mutu; inji Hamza Al'mustapha.
Daga Jaridar Dimokuradiyya

Post a Comment (0)