ZALUNCI NE A RIKA DANGANTA KUNGIYAR IZALA DA WANI MUTUM GUDA KADAI

ZALUNCI NE A RIKA DANGANTA KUNGIYAR IZALAH DA WANI MUTUM GUDA KADAI:
1. Lalle nau'i ne na cin amanar Kungiyar Izalah tare da keta mata huruminta wani ya ce: ita kungiya ce da ba wasu musulmi ba ne suka hadu suka kafa ta; a'a wai wani mutum guda ne ya kafa ta!
2. Lalle dasisa ce da makircin wasu masu hamayya da da'awar Sunnah, suka dora wasu gafalallu a kan cewa Kungiyar Izalah kungiya ce da mutum guda kadai ya kafa, wannan mutumin kuwa shi ne Sheikh Isma'ila Idris!
3. Lalle su wadannan masu hamayya da da'awar Sunnah sun yi abin da suka yin ne; saboda su cusa Kungiyar Izalah cikin jerin gwanon darikun bidi'ah; irinsu Tijjaniyyah, da Kadiriyyah da masu kama da su.
Su kuma kauda kasancewar mizanin Kungiyar shi ne: Alkur'ani, da Hadithi, da Ijma'i, ta inda mizanin nata zai koma zuwa ga abin da shi Sheikh Isma'ila Idris ya ce, da kuma abin da khalifofinsa a bayansu suka ce!!
4. Tabbas abin da ke rubuce a cikin constitution; watau tsarin mulkin Kungiyar Izalah shi ne: Ita kungiya ce da wasu musulmi suka hadu suka kafa.
Suka kuma hadu suka rubuta mata constitution dinta watau tsarin da za a rika gudanar da ita a kan shi.
5. To amma abin mamaki duk da irin wadannan bayanai filla-filla da suke cikin constitution din ita Kungiyar sai da 'yan bidi'ah masu hamayya da da'awar Sunnah suka sami nasarar dora wasu gafalallu a kan cewa:
Kungiyar Izalah kungiya ce da wani mutum guda kawai ya kafa!!
Allah Ka tausaya wa wannan Al'ummah tamu Ka dora ta a kan gaskiya a cikin komi nata.
Ameen.

Post a Comment (0)