FASSARAR FINA-FINAN INDIA ZUWA HARSHEN HAUSA: LALE MARHABAN DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA

FASSARAR FINA-FINAN INDIYA ZUWA HARSHEN HAUSA LALE MAHARBAN DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA.
Daga Abu Hidaya.
Babu shakka samuwar wadannan fina-finai cikin harshen hausa ba karamin ciyar da harshen hausa gaba zai yi ba.
Duba da yadda masu fassarar suke kokari wajen fassara ko wacce kalma da hausartacciyar Hausa.
Idan ana maganar Hausantaccen Fim din Hausa kamfanin "Algaita "Record" ko "Speedy Ventures" sune suka yi fice a wannan fage.
Kuma tabbas za'a matukar amfana da wannan sauyi domin cigaba ne a fagen bunkasar harshe.
Na dade ina kallon fina-finan Hausa wadanda masu ikirarin halattun kabilar Hausa ko abokan hausawa suka shirya, amma har yau in banda haushi da takaici babu abinda nake karuwa dashi,
domin mafi yawa daga cikin Fina-finansu babu hikima balle azancin magana.
Abin mamaki shine nakan iya zama da yara na kalli fassararren Fim din Hausa mu yi raha mu yi nishadi ba tare da jin kunya ko danasani ba.
Amma fim din da aka shirya cikin harshena yana min wahalar kallo da yara.
Wani karin abin mamakin shine yadda zaka ji dadadan kalamai masu dadin ji da sauraro daga fassararrun fina-finai cikin harshen Hausa.
Tambayar a nan ita ce shin mu bamu da hikima ko tunanin samar da wadannan kalamai da azancin zance cikin fina-finanmu?
Nasan wani zai ce ai ana yi, ni ma ba wai nace bane ba'a yi bane, sai dai zantukan fina-finan asalin Hausa ko da yaro ya yi wasu ba zai burge ba balle manya da ke furtasu da sunan barkwanci ko kalaman so.
Dan haka ina baiwa masu fina-finan asalin Hausa da su yi ko yi da masu Fassara Fina-finan ketare cikin harshen hausa wajen samar da zubi da tsari gami da jerantuwar hikimar zance da azanci harshe fina-finansu don nishadantuwar masu kallon FINA-FINAN su.

Post a Comment (0)