Zunubai na suna da yawa

ZUNUBAI NA SUNA DA YAWA TA YAYA ZAN GOGE ZUNUBAI NA ???
.
1→Ka goge (Zunubanka) da wannan Hadisin.
.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Babu wani Mutum adoron kasa da zai ce: «La ilaha illallah, Wallahu Akbar, Wala haula wala kuwwata illa billah» Face sai an shafe masa zunubansa ko da sunkai kumfar teku yawa." [Albani ya hassana shi]
.
2→ka goge (zunubanka) bayan kaci abinci.
.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Wanda Yaci abinci sannan yace:
.
« ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﻃﻌﻤﻨﻲ ﻫﺬﺍ ﻭﺭﺯﻗﻨﻴﻪ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺣﻮﻝ ﻣﻨﻲ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ »
.
Za'a gafarta masa daga zunubansa...." [Albany ya Hassana shi]
.
3→ka goge (zunubanka) bayan ka cire tufafinka.
.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: kuma wanda ya cire tufafinsa sai yace:
.
« ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻛﺴﺎﻧﻲ ﻫﺬﺍ، ﻭﺭﺯﻗﻨﻴﻪ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺣﻮﻝ ﻣﻨﻲ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ »
.
Za'a gafarta masa daga zunubansa... [Albany ya inganta shi]
.
4→ Ka goge (Zunubanka) cikin yininka.
.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Wanda Yace: «Subhanallahi Wabi hamdihi» sau dari a yini za'a gogewa mutum Zunubinsa koda ya kai kumfar teku yawa." [Sahih Muslim]
.
5→ Ka goge (Zunubanka) bayan Sallarka.
.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Wanda yayi tasbihi cikin bayan kowace sallah SubhanAllah 33, da Alhamdulillah 33, da Wallahu Akbar 33, kuma ya cika 100 da fadin:
.
« ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ، ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ »
.
Bayan ko wacce Salla ta farilla za'a gafartawa mutum zunubinsa ko ya kai kumfar teku yawa." [Sahih Muslim]
.
6→ Ka goge (Zunubanka) gabannin bacci.
.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Wanda yayi nufin kwanciya akan shimfidarsa yace:
.
« ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ، ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ، ﻻ ﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺍﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﻌﻠﻲ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ، ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ »
.
za'a gafartawa mutum zunubansa ko da ya kai kumfar teku yawa." [Ibn Hibban Ya inganta shi]
.
7→ Ka goge (zunubanka) yayin kiran sallah.
.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Wanda Yace yayin da yaji kiran sallah:
.
« ﺍﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ، ﺭﺿﻴﺖ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﺭﺑﺎ، ﻭﺑﻤﺤﻤﺪ ﺭﺳﻮﻻ، ﻭﺑﺎﻹﺳﻼﻡ ﺩﻳﻨﺎ .»
.
Za'a gafarta masa zunubansa. [Sahih Muslim]
.
8→ Ka goge (Zunubanka) da ISTIGHFARI.
.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Wanda Yace:
.
« ﺍﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﻫﻮ ﺍﻟﺤﻲ ﺍﻟﻘﻴﻮﻡ، ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺍﻟﻴﻪ »
.
Za'a gafarta masa zunubansa ko da ya kasance ya gudu daga filin yaki." [Tirmizi ya ruwaito, Albany ya inganta shi]
.
ALLAH shine mafi sani.

Post a Comment (0)