AN GINA CINIKAYYA NE AKAN YARJEJENIYA

*_AN GINA CINIKAYYA NE AKAN YARJEJENIYA!!!_*

                              *Tambaya:*
Assalamu alaikum, Ni dai na kasance ina sana'ar saida fatar shanu wacce ake kira da kirgi. Mu awajan siya Ana hada mana manya da kanana, Alal misali idan muka siya dubu 5000-5000 bugun goro, akwai Kuma wanda in shi kadai ne bazai kai 5000 ba. Ni kuma dana kawo kasuwa sai nace dole sai an siya babba da karami farashi daya shin ya halatta nai haka ? ko kuwa sai dai na ware babba daban karami daban. Na sai da kowanne da halinsa ko ko ya'abun yake Allah ya gafarta mallam?? 

                                *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, To dan'uwa, In har mai saye ya ga fatun da za ka siyar masa yadda ya kamata, kuma ya yarda zai saya da farashin da ka fada, babu matsala a shari'ance, saboda ciniki yana kasancewa akan yarjejeniya tsakanin mai saye da mai sayarwa, kamar yadda aya ta: 29 a suratun Nisa'i take nuni zuwa hakan.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)