ANA YIN WUTIRI NE A ƘARSHEN DARE

*_ANA YIN WUTIRI NE A KARSHEN DARE!!_*

                               *Tambaya*
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Malam menene hukuncin yin wuturi a lokacin taraweeh bayan kuma mutum yana son yin tahajjud cikin dare?

                                     *Amsa*
Wa'alaikum assalam, in har mutum ya san zan yi wata sallar bayan tarawihi, to abin da yake dai dai shi ne ya jinkirta wutirinsa zuwa karshen dare saboda hadisin da Bukari da Muslim suka rawaito cewa: Annabi (S.A.W) yana barin wutirin sa in ya yi sallar dare zuwa lokacin sahur, da kuma hadisin da Annabin yake cewa: Ku sanya wutiri sallarku ta karshe da daddare"
Bukari ne ya rawaito da Muslim.  

Allah ne mafi sani.

Amsawa:- Dr. Jamilu zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)