Ƴar Bautar Ƙasa 13

*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*

Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*13*


Rana bata ƙarya.

Ayaune dubban mutane suka hallara ababbar kotun ƙasa dake Abuja domin suraran shariar su salma.

An fafata ankai ruwa rana tsakanin barrister kabeer,da lauyan Alhaji Adamu,sabida ƙwararren lauya ya ɗauka, daga ƙarshede su barrister kabeer suka gabatar da shaidunsu,da hujjoji,wanda hakan shi yajanyo alƙali ya yanke hukunci batare da ɓata lokaciba.

Kotu ta wanke salma daga zargin da ake mata inda shikuma Alhaji aka yanke mishi hukuncin kisa ta hanyar rataya...

Haka kotu ta watse kowa se barka yakewa salma itako se kuka takeyi,na farin ciki.

Da kyar take taka ƙafarta sabida tsawon shekaru biyun datayi a gidan yari ɗaure take cikin sarƙa.

Ahaka suka fito harabar kotun,ƴan jarida ne suka zagaye salma suna mata tambayoyi,da sauri doctor yasha gabanta,ya kareta,sannan ya dakawa ƴan jaridar tsawa da cewa.

"Dalla malamai ku ƙyaleta,ina ruwanku dason sanin halin farincikin datake ciki,meyasa lokacin da aka kamata bakuje kunyi mata irin wannan dairar ba?to bazatayi magana ba"yana kaiwa nan yajata da ƙarfi suka bar gurin.

A mota suka sami barrister yana jiransu,doctor sakinta yayi yaje ya buɗe gaban motar yashiga,salma hannu tasa zata buɗe bayan motar,da sauri doctor ya dakatar da ita da cewa.

"ke gidan ubanwa zaki bimu kuma?ay mungama aykinmu,dan haka kibi wani sarkin bamuba,dan munan da kika ganmu babu wani me neman mata,acikin mu bare kice ko kinyi kasuwa ne,kuma babu ɓarawo anan bare kice zaki bimu mu ƙara miki sani akan harkar dan haka tun wuri ki kama kanki,useless kawai"

durƙushewa tayi agurin tana kuka jikinta se rawa yakeyi,numfashinta na haurawa sama zuwacan ta kife agurin a sume.

A gigice doctor ya buɗe motar yazo gurinta kinkimarta yayi yasaka abayan motar,sannan shima yashiga bayan ya ɗora kanta akan cinyarshi sannan kabeer yaja motar da gudu suka nufi Asibitin da najeeb yake Ayki.

A hanya kamin suje,najeeb yafara bata taimakon gaggawa,inda ya ɗora bakinshi akan nata yafara hura mata iska ta baki,sannu a hankali tafara numfashi sama sama,a haka suka ƙaraso asibitin.

Doctor be jira akawo gadon ɗaukar marasa lafiyaba dakanshi yaɗauketa yayi cikin Asubitin da ita kabeer na binshi abaya.

Hankalin doctor be kwantaba seda yaga salma ta dawo cikin hayyacinta ba abinda ke damunta.

Abinci yadunga bata abaki harseda tace ta ƙoshi sannan ya ƙyaleta,shide kabeer yana gefe,cikinshi ya cika da dariya amman ya danne shiyasa ya ƙosa su fita.

Allurar bacci doctor yamata,shima da kyar ta yarda,sabida tana kunyar yaga jikinta,shiko ko ajikinshi dan juyawa yayi yana kallon kabeer rai aɓace yace.

"Malam baka ganin zan mata allurane?dan Allah kaɗan je daga waje,haba mutum se shegen sa ido"

Ba musu kabeer yafita,sannan,doctor yajawota jikinshi ya matseta ya ɗaga doguwar rigar dake jikinta,yaɗan matsar da fant,ɗin yayimata allurar,sannan ya saketa se kuka takeyi.

Shiko ba abinda yafi bashi mamaki,se irin dattin da yaga fant ɗin yayi,hakan na nufin shikaɗai take sawa acan kenan,sosai ranshi ya ɓaci dan haka kwantar da ita yayi,yafara yimata general check off na cututtuka,inda yasamu,tana da maleria da typhod.

Magunguna ya ɗauko da suka dace yabata tasha,sannan tafice daga ɗakin.

A harabar Asibitin suka haɗu da kabeer.

kabeer yana ganinshi yamiƙa masa key ɗin motar yace.

"Don Allah kaɗanyi driving ɗin inni nace zanyi komai ze iya faruwa"

ba musu ya amshi key ɗin suka shiga motar yaja suka ɗau hanya.

Ay kabeer kamar jira yake,yafara tuttular da dariyar data cika mushi ciki.

shiko najeeb ƙara shan kunu yayi alamar ba wasa.

"wlh najeeb baka da kunya,wai har zancema son salma kakeyi amman ka ƙaryatani,inba sonta kake yiba ina ruwanka da ƴanjaridar ɗazu,?in ba so meyasa ka ruɗe sanda ta faɗi bayan kaine silar faɗuwar tata?inba so meyasa ka gaza jira mu iso asibiti kadubata,kafara bata taimako tun amota?,finally,meyasa kaji kishin inga jikinta sanda zakayimata allura?"kabeer ya faɗi yana dariya.

wani uban tsaki najeeb yaja,sannan,yace.

"Kaide anyi ɗan iska wallahi,inbanda kaiɗin,bakasan aykinaba,taya zanga mutum asume amatsayina na likita nawuce batare dana taimakeshi ba?kuma shi kenan danni ɗin ɗan iskane se inbari kaga jikin patient ɗina alhalin kaiba muharraminta bane?su kuma ƴan jarida in aka barsu ay zuwa zasuyi su yaɗa ƙarya da gaskiya,shiyasa na hana badan komaiba,sedan ƴar uwatace a musulunci,kainifa kabeer ka isheni wallahi banason salma bana ƙaunarta sam,dan bata jikin jerin matan danakeso,inkuma kasake magana wallahi sena saukeka a titi"

Shuru kabeer yayi amman fa bedena dariyaba,musamman sanda suka tsaya awani boutique,yatambayi najeeb mezasuyi anan,yabashi amsa da cewa.

"salma zamu siyawa kayan dazata canja najikinta sunyi datti"

Sosai kabeer yake dariya ahaka suka shiga gurin,yazaɓo mata dogayan riguna masu kyau guda biyar,sannan ya isa gurin su fant da bra,ido kabeer ya ware yana kallonshi,ba abinda yafi ba kabeer dariya kamar ganin yadda najeeb in ya ɗauko fant ko bra,seyayi ɗan tunani kaɗan,sannan se ya jujjuya,wani yaɗauka wani ya ajiye,hakanne yasa kabeer ya gano,doctor yana kallo salma aranshine sannan ya zaɓi wanda yake ganin ze mata daidai.

"mutumina kace abun yayi zurfi har haka ashe bansaniba,ah lalle salma tagama da zuciyarka sauran mata se haƙuri,princess over the universe ta iso"kabeer ya ƙarasa zancan yana dariya.

Duka najeeb yakaimasa,sannan yace.

"Tunda kazama maye bari na kyaleka duk abinda zakace kaje kaita cewa tunda de ni nasan basonta nakeba ay shikenan"

Har suka dawo Asibitin kabeer bedena tsokanarshiba,sanda suka shiga ɗakin tana bacci dan haka ajiye kayan sukayi,har zasu fita doctor yaga gashi ya rufe mata fuska,komawa yayi ya gyara mata,sannan suka fice.

muje zuwa.

surbajo for life.


Post a Comment (0)