Ƴar Bautar Ƙasa 14


*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*14*


Salma farkawa tayi taga leda akusa da ita,buɗewa tayi abinda tagani acikine yabata tabbacin natane,to amman waya siyo mata?.


Wanka tashiga,ta jima a toilet tana wanke jikinta,haka ta dunga zubar da ruwa baƙiƙƙirin sabida dattin jikinta,haka gashin kanta,tajima tana wankeshi,dayake a office din doctor ɗakin yake,tamkar de shine emergency ɗinshi,to komai akwai na amfani a toilet din,hadda hand drayer dan haka busar da gashin tayi.

Kusan awa biyu ta ɗauka a bayin sannan ta fito,

Fant tasak da bra ba ƙaramin mamaki tayiba ganin yadda suka mata daidai,dan ko ita taje siyowa da kanta tana mistakes,riga ɗaya ta ɗauko tasaka,rigar,ja ce da gyalenta shi kuma fari ,ajiye gyalen tayi,tafita zuwa cikin office ɗin doctor ɗin tafara neman ko turarene,ayko ta gano wani tafesa sannan tadawo ta ɗauki cumb tafara tace kanta.

Zafi take ji sosai yayin taje kan,amman haka ta daure tanayi ta runtse ido wanda kowa yaganta yasan ba ƙaramin zafi take jiba.

Doctor ne ya shigo ɗakin fuska ba walwala,itako sabida zafin da kanta yake mata batasan yashigo ba,zuwa yayi ya riƙe hannun datake taje kan dashi,da sauri ta ɗago kanta tana kallonshi,ganin shima ira yake kallone yasa tayi ƙasa da idonta.

"Shi taje kan dole ne se anyi shi tunda anajin zafi?"doctor ya faɗi rai aɓace,

Shuru tayi ta ƙara yin ƙasa da kanta,dan yanzu gaba ɗaya nauyinshi takeji.

"kar in kuma ganin hakan,inba hakaba rai ze ɓaci,taso muje kici abinci"yana gama magana yajuya yayi gaba,miƙewa tayi ta yafa gyalen rigar tabishi abaya ƙafa ba takalmi

Yana gaba tana binshi abaya har zuwa harabar asibitin se alokacin ya lura ƙafarta ba takalmi,miƙa mata takalminshi yayi yace tasaka.

tsayawa kallonshi tayi ganin ba wasa afuskarne yasa tayi saurin zira takalmin shikuma yaci gaba da tafiya ba takalmi har suka isa motarshi.

wani gurin saida takalma ya tsaya,ya fita zuwacan se gashi yadawo,da sabon takalmi aƙafarsa sannan itama ya siyo mata nata aka sako a leda.

Restaurant yasamu me kyau ya tsaya sukaci abinci sannan suka fito suka shiga mota.

Hanyar kaduna taga ya ɗauka,wani farincikine ya lulluɓe zuciyarta yau,zataga iyayenta,ɗa aminiyarta.

Suna tafe a hanya ko tari tayi,seya waiga ya kalleta,amman bazeyi magana ba ahaka har suka iso garin kaduna,waigowa yayi yakafeta da ido hakanne yasa tagane Address yake nufi tadunga nuna masa.

Ayko haka ta dunga yimasa kwatance har suka iso ƙofar gidan,sahabi suka samu zaune agaban gidan yakasa kayan miya yana siyarwa.

parking Doctor yayi,da gudu salma tafice amotar,ƙafarta sanye cikin takalminshi tanufi yayan nata tana kiran sunan shi.

A gigice sahabi ya ɗago yana kallonta,naso me karatu yana gurin yaga iri. Tafiyar yajin da sahabi yayi da kayan miyan daya kasa,gurin kwasawa da gudu zuwa cikin gidansu.

Duk miskilanci doctor seda yadara,da gudu itama salma tabi bayan sahabin zuwa cikin gidan.

Lokacin babanta yafito daga bayi ganin sahabi da gudune yafara tanbayarshi ko lafiya,ganin salma da gudune yatabbatarmishi dacewa tabbas ba lafiya.

Dagudu mahaifiyarta ta fito daga kitchen ta burma ɗaki hakanne yasa su sahabi maramata baya,suka shige suka kulle ƙofar.

Zuwa ƙofar ɗakin tayi tana bubbugawa tana cemusu itace ba mutuwa tayiba amman ina ba wanda ya saurareta dukansu se karatun qurani suke kai kace a masallacin harami🤣🤣

Magiya bawacce bata musuba amman bawanda ya saurareta,haka ta juya tafice daga gidan tana kuka.

Doctor koda ya hangota tana kuka murmushi yayi dan yasan zaa rina,fita yayi a motar yaje yasha gabanta,jan hannunta yayi suka koma cikin gidan.

Sallama yashigayi,amman jin sautin karatunsu ba ƙaramin dariya yabashi ba amman daurewa yayi beyiba yaci gaba da sallamar.

Da kyar sahabi yace sadaƙallahul azim,ya amsa sallamar,leƙowa yayi ta window ganinshi tare da salma ne yasa yamaida windon ya kulle ya ɗauko sabuwar sura ya ɗora daga inda ya tsaƴa.

Sunfi awa uku atsaye suna musu magiya sannan suka yarda suka fito,da gudu salma tanufi mahaifinta da zummar rungumeshi,ayko ya beyi ƙasa a guiwaba ya kwasa da gudu ze koma ɗakin,yana faɗin.

"wayyo Allah na nashiga uku,gurina aka aykota,Allah ka kawomin agaji"

da sauri salma takoma ta tsaya akusa da doctor,ganin hakane yasa baban nata tsayawa yana mazurai.

Duk abinda yafaru doctor yakwashe yasanar dasu,inda ya kama hannun salma ya miƙa musu yace su taɓa suji ita mutumce.

Da ƙyar suka taɓa ay suna taɓawa suka rungumeta suna kukan murna.

Ranar wuni sukayi tattalin salma,inda tanemi yafiyarsu game da bijirewa tarbiyyar da suka bata.

mutanan gari se zuwa ganinta akeyi,feefee ma baa barta abaya ba.

Kowa se murnar ganinta yakeyi,shaf salma ta mance da doctor dake ɗakin sahabi yana hutawa.

Se bayan sallar magrib data fita raka feefee ne ta hangi motarshi,gabantane ya faɗi,da sauri sukayi sallama da feefee ta nufi ɗakin sahabin.

Azaune tasameshi yana duba wayarshi,tana shiga ya miƙe yace mata.

"To Allah ya kyauta gaba,saduwar alkhairi"yayi hanyar waje ze fice.

Bakin salma har rawa yakeyi,gurin furta.

"Don Allah doctor kayi haƙuri"

Dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu,buɗe labulen yayi ze fita amman se jiyayi anriƙe masa hannu da sauri ya waiga.

salmace durƙushe akan guiwarta,idonta na zubar da hawaye,tace.

"kamin dukkan halacci,banida bakin godemaka,bani da abin biyanka dashi,sede Allah ne ze biyaka,don Allah doctor karka tafi acikin darennan,inajin tsoro kar wani abu ya cutar dakai,don Allah badan niba ka kwana gobe katafi"

ganin yadda ta marairaicene yasa doctor,komawa ya zauna wanda shikanshi,besan sanda yayi hakanba kawaide yabi umarnin zuciyarshine.

Ayko haka doctor ya kwana agidan nasu salma batare da nuna kyama,agaresuba,mahaifanta se godiya suke masa harda kuka,shi kuma se tsintar kanshi yayi dajin kunya da nauyinsu.

Washe gari da sassafe ko salma be jira tazo sun gaisaba yayi sallma da malam da sahabi ya ɗauki hanyar Abuja.

*Wai waye doctor najeeb*

muje zuwa,


Surbajo for life.

Post a Comment (0)