Ƴar Bautar Ƙasa 12

*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*

Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*Safina mum sultan,saly,Queen Aeanarh,wannan shafin nakune Allah yabar so da ƙauna,nagode sosai,kuma insha Allahu bazaku taɓe ba*

*12*

Natsuwa sukayi sosai dan su samu mafita.

Barrister ne yace.

"Malama,Salma,sunana barrister,kabeer,ni lauyane me zaman kansa,sannan ni amini ne ga doctor najeeb,inaso ki bani amsar duk wata tambaya dazan miki tsakaninki da Allah,kinyi alƙawarin bani amsar?"

Kai,ta daga masa tana kallon doctor wanda shima ita yake kallo.

"Me yasa kika jefa kanki cikin sanaar da bata dace dakeba?kina mace meyakaiki safarar miyagun kwayoyi?"

Kuka salma ta rushe dashi,cikin kukan tace.

"Wlh ni ba sanaata bace,hasalima ni bansan akwai kayan laifi acikin jakarba wlh"ta ƙarasa maganar cikin kuka.

"Jakar takice ko ba takibace?"

"wlh batawa bace"cewar salma

"to a ina kika samota?"cewar barrister.

Ƙasa tayi da kanta alamae kunya dajin nauyi sannan tace.

"Satowa nayi"

Runtse ido doctor yayi sabida maganar ta zafafa zuciyarshi.

"a ina kika sato"inje barrister

kuka ta fashe dashi,sam bakinta yakasa faɗin inda tasato jakar,duk yadda su doctor sukayi da ita dan ta faɗi inda ta sato jakar amman ta kasa.

Haka suka haƙura sukayimata sallama akan zasu dawo wani satin.

Koda suka taho a hanya doctor ya kasa magana,gaba ɗaya ranshi aɓace yake

Murmushi barrister yayi sannan yace.

"No wonder mutumina jiya ka kasa bacci,ashe amaryace ke hannun kwalawa,dole hankalinka yaƙi kwanciya"ya ƙarasa maganar yana dariya.

Tsaki doctor yayi sannan yace.

"kai daɗina dakai zancan banza wlh,to bari kaji ni wlh ba son salma nakeyiba,ba abinda zanyi daita,ɓarauniya ce fa"

"to su ɓarayin ba mata bane?,kuma zancan sata ay dana,kaida ganinta a yanzu kasan ko ɗaura mata kayan satar akayi a hannunta seta gudu tabarshi aguri,to kuma shine abun dogaro dan kawai tayi sata ada,ay yanzu ta tuba"

"to komade me zakace ni banasonta,kuma bazan taɓa sonta ba"

"hhhhh ah gaskiyane wannan arashin sonne ma jiya ka kasa bacci sabida kaganta acikin mayuyacin hali"

"wlh bana son salma tausayinta kawai nakeji amatsayinta na musulma"

"tausayi baya zuwa seda soyayya,mutumina kayarda kana cikin soyayyar salma kawai"

"karubuta ka ajiye,ni najeebullah,nafi ƙarfin salma nesa ba kusaba,na faɗa maka ni ba sonta nakeba,karka sake yimin wannan maganar pls"

Dariya yayi sannan yace

"to tuba nake angon salma"

Tsaki doctor yayi sannan yamaida hankalinsa kan titi.

"Amman najeeb nayi mamakin abinda ya hana salma faɗin inda ta sato jakar nan,nifa ina ganin kamar anyi mata sihirin daya rufe bakintane,sabida inkayi laakari tana yunƙurin faɗi amman se ta kasa"

shuru doctor yayi yana nazarin maganar zuwacan yace.

"tabbas naga alamar hakan,to amman yazamuyi,yanzu?"

"ka kwantar da hankalinka kamance mahaifina malamine,aykawai gobe mu shirya muje katsina,gurinshi muyi masa bayani danni banaso mu shiga kotu asake ɗaga ƙara,sonake ayiwa shariar salma zama ɗaya tak dan asallameta da wuri,ayi ayi ashafa fatiha dannaga angon nata kamar amatse yake"

wani duka doctor yakaiwa barrister wanda saura kaɗan motar ta kwace a hannunsa.

Dariya barrister yadunga yiwa doctor shiko yasha kunu kamar be taɓa yin dariyar ba.

Washe gari da Asuba suka ɗauki hanyar katsina,sun isa lafiya.

Inda sukayiwa baban barrister bayanin abunda yakawosu,ayko beyi ƙasa a guiwaba yayi istahara ya tabbatar musu da hasashensu,daganan,rubutu yayi na ayoyin Allah,ya wanke yabasu yace abata tasha awanke mata fuskarta da rubutun.

ba yadda barrister beyi da doctor ba akan su kwana amman fafur yaƙi shide sede su tafi aranar.

Ayko dole barrister yabishi suka ɗauko hanyar Abuja,basu isoba se ƙarfe biyu nadare,barrister se mita yake masa da cewa.

"wlh akan taka amaryar baza ka illatawa tawa amaryar ni ba ehe"

doctor yagaza bashi amsa haka sukayi sallama.

Washe gari takwas na safe a gidan yarin tayi musu.

inda doctor shida kanshi yaba salma rubutun tasha sannan ya wanke mata fuskar.

cikin hukuncin ubangiji tun kan su tambayeta tafara faɗin.

"jakar ta Alhaji Adamu canji ce ma'aikacin CBN"

Daga haka rakwashe komai ta sanar dasu tundaga ranar data fara haɗuwa dashi.

godiya suka yiwa Allah,daya bata damar faɗin sunan me jakar.

Daga gidan yarin,cbn sukaje neman Alhajin amman basu sameshiba dan haka hotel ɗin da abun yafaru sukaje.

Inda suka nuna katinsu na shaidar ayki sannan suka buƙaci da a nuna musu video na wunin ranar da abun yafaru.

Ansha wuya kamin asamo video ɗin,koda aka kunna.

Wani mutumne yashigo sanye da baƙaƙen kaya ɗauke da wata ƙatuwar jaka,wani ɗaki yanufa,abakin ƙofar ɗakin ya tsaya yakira waya,zuwacan sega Alhaji adamu canji yazo ya buɗe ya amshi jakar ya koma ciki shi kuma mutumin ya juya yatafi,baa jima sosaiba sega salma ta fito ɗauke da jakar tana ta waige waige alamar rashin gaskiya,zuwacan kuma seta daidaita tafiyarta tazo tawuce ɗauke da jakar.

gwauron numfashi suka ja dukansu,sannan sukasa aka dubo list ɗin sunaye na ranar,inda sukaga sunan Alhaji adamu canji shine yakama ɗakin da salma tafito daga ciki.

Da ƙyar manajan hotel ɗin ya amince ya basu list ɗin da plate ɗin video,seda suka sha fama dashi sannan yabasu amman dasunan aro.

Daga hotel,kotun ɗaukaka ƙara suka je suka shigar da ƙara inda aka tsadar musu da lokacin da zaa saurari ƙarar.

Amman kamin zuwan ranar,kotun taba hukumar ƴansanda umarnin atsare Alhaji Adamu kamin zuwan ranar.

Ayko cikin saa ƴansanda suka kamoshi a airport yana shirin bsrin ƙasar sabida yasamu labarin komai.

muje zuwa

surbajo for life.


Post a Comment (0)