BANA IYA RIƘE ALWALA, YAYA SALLAH TA?

*_BANA IYA RIKE ALWALA, YAYA SALLATA?_*

                                *Tambaya:*
Salamun Alaikum, Malam barka da yau, Malam ina fama da matsalar basir wadda har takai wasu lokutan ban iya rike alwala, ko da kuwa na shiga bayi, innayi alwala sai ta karye kafin agama sallah, kuma ko nasake wata hakan zai sake faruwa.
To malam yaya zanyi?

                                    *Amsa:*
To dan'uwa ina rokon Allah ya yaye maka wannan musibar, Mutukar a mafi yawan lokutan rayuwarka kana fama da tusa, to abin da yake kanka shi ne:

-Ka rinka yin alwala yayin kowacce sallah, duk abin da ya fito bayan haka, ba zai hana ingancin sallarka ba, Allah ba ya dorawa rai abin da ba za ta iya ba.

-Amma idan a wasu lokutan take fitowa, ta yadda hakan ba ya maimaituwa a rabin rayuwarka, ko mafi yawanta, to ya wajaba ka yi alwala duk lokacin da ta fito.

-Duk cutar da Allah ya saukar tana da magani, don haka zai yi kyau ka nemi Magani iya bakin kokarinka a wajan masana.

Don neman Karin bayani duba: Alfawakihuddawany na Annafraawy 1\340.

Allah ne mafi sani.

27/12/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu zarewa
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)