DUKIYA DA ƳAƳA FITINA NE


DUKIYA DA 'YA'YA FITINA NE


 Allah ya fadi gaskiya dayake fadamana acikin Suratut-tagaabun yake cewa: Abin sani kawai dukiyoyinku da 'ya'yanku fitinane, shi kuma Allah a gurinsa akwai lada mai girma(aljannah). Wannan lada mai girma ba'aso kayi sake dukiyarka da 'ya'yanka su hanaka samunsa. Tabbas wannan abune tabbatacce wasu 'ya'yayensu sun zame musu fitina ta yadda suke kokarin tara musu dukiya ko ta halin qaqa idan ma'aikacin gwamnatine ko mai riqe da wani muqami na siyasa ne zaka aikinshi kenan sata da cin dukiyoyin al'ummah yana tarama ''ya'yansa dan kada suyi talauci abayan rasuwar. Ya yarda ya tara ma 'ya'yansa haram su mutu sutafi wuta kuma koda sunyi addu'a aqi karba saboda komai nasu haramunne kunsan hadisin matafiyin nan wanda yayi qura ga wahala yazo yana addu'a akaqi karba daga ciki har akace abincinshi haram, abinshansa, da tufafinsa duk haram ne kuma tun yana karami anciyar dashi da haram manzo s.a.w yace tayaya za'a amsa addu'arsa? Idan dan kasuwane cin riba da tara kudi kota halin qaqa shima dai duk saboda iyali karsu wahala. Bashshi ma dukiyar ta halas ce dayawan masu kudi saboda tsoron talauci wa 'ya'yansu yasa basa ciyar da dukiyarsu wajen taimakawa addinin Allah, basa taimakawa danginsu wanda a wannan dukiyar taka akwai haqqinsu aciki ba abanza Allah zai zabo ka kai kadai acikin danginku yabaka dukiya ba akwai haqqin 'yan uwa da maqota acikin wannan dukiya taka kuma idan kaciyar Allah yayi alqawarin ninka maka kuma zai gafarta maka ya saka ka a aljannah amma abin ban takaici 'ya'yanka zasu hanaka samun gidan Aljannah lallai 'ya'yanka da dukiyarka anan sunzama maka fitina. Yanzu ka amince kazama baqin marowaci katarawa 'ya'yanka dukiya baka taimakon jama'a? Ko kasan cewa inkabar musu dukiya insunyi alheri da ita ladan nasune su kadai insukayi sharri kuma tare zaku raba zunubin kayarda da haka? Ko kasan cewa abinda kaciyar shine naka wanda kaboye abanki kuma na masu gadonkane kana mutuwa su za'a bawa kayarda katafi bakomai kabarmusu dukiyar anan? Allah kabamu dukiya mai albarka wadda zamu dinga ciyarwa dan neman yar darka.
Post a Comment (0)