*_IDAN KWANAKIN KAFFARAR KISA SUKA RATSO A RANAR IDI, MENENE HUKUNCI?_*
*Tambaya:*
Assalamu Alaikum. Allah ya karama rayuwa albarka. Malam don Allah a taimakamin da amsar tambayarnan.
Mutumin da yake azumin kaffarar mutuwa ya zaiyi da ranar sallah. Shin zai aje azumin na ranar ne koko zai wuce kawai da azumin shi.
Allah ya bada ikon amsawa.
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Amin Allah ya amsa adduarka.
Malamai sun yi sabani game da azumin kaffara idan ya ratso ranar idi zuwa maganganu guda biyu:
1. Ba za'a tsaya ba saboda ranar idi za'a cigaba da azumin saboda aya ta (92) a suratun Nisa'i ta shardanta yin azumin kaffarar Kisa a jere, dakatawa saboda idi kuma zai Kore wannan sharadin, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.
2. Ya wajaba ya sha azumi a ranar idi, saboda yin AZUMI haramun ne a wannan ranar kamar yadda hadisin Umar dan khaddabi ya tabbatar, wannan yasa ba shi da laifi idan ya sha tun da shari'a ta yi masa izni.
Zance mafi inganci shi ne na Biyu, saboda idan hani da umarni suka ci karo da juna ana gabatar da hani, saboda haka mai kaffarar Kisa zai sha saboda Idi ko tafiya ko haila.
Don neman Karin bayani duba: Al Muntaka min Fataawa Alfauzaan 1/152
Allah ne mafi sani.
31/08/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.