1⃣ALALAN FULAWA
ingredients:
* Fulawa
* Kwai
* Nama
* Kifi danye
* Markadadden kayan miya
* Albasa
* Attarugu
* Curry
* Gishiri
* Maggi
Procedures:
Ki tafasa Kifi, ki bare ki fidda tsokar, ki kwaba fulawa da kauri kamar kwabin alala, fulawa gwangwani hudu, sai ki fasa kwai hudu akai, ki zuba kifin da kika murmusa ki yanka nama kanana ki zuba, ki zuba markadadden kayan miya ludayi daya ki yanka albasa da attarugu, kisa curry, gishiri da maggi. Ki zuba mai gwangwani daya ki juya sosai, ki shafa mai a gwangwanaye ki zuzzuba ko ki kulla a leda ki dafa.
2⃣ ALALAN KABEJI
ingredients:
* Kabeji
* Wake
* Hanta
* Kwai
* Kifi
* Attarugu da Albasa
* Maggi, Curry da Gishiri
* Manja ko Man gyada
Procedures:
Ki surfa wake gwamgwani hudu ki zuba attarugu da albasa ki kai a markada miki, ki yanka kabejinki kanana mai dan yawa ki zuba akai, ki yanka dafaffen kwai kizuba akai, kisa maggi, curry, gishiri ki juya sosai, kisa mai gwangwani daya, ki kara juyawa ki zuba a gwangwani ko leda ki dafa.
3⃣ALALAN DANKALI
Ingredients:
* Dankali
* Nama
* Kwai
* Attarugu
* Albasa
* Curry
* Maggi
* Gishiri
* Mai
Procedures:
Ki dafa dankalinki ki marmasa ko ki daka, ki tafasa nama ki daka kizuba akai, ki jajjaga attarugu da albasa kizuba akai, kisa maggi, curry, gishiri da mai, ki fasa kwai kizuba akai ki juya sosai, ki zuba a leda ko gwangwani ki dafa.
4⃣ALALAN PLANTAIN
Ingredients:
* Plantain
* Garin plantain
* Cray fish
* Dry fish
* Attarugu da Albasa
* Curry
* Manja
Procedures:
Ki bare plantain guda uku ko hudu, ki yanka kanana ki mutsittsike ko ki markada a blender, ki zuba garin plantain kofi daya da rabi akan plantain din dakika nika, ki gyara busasshen kifinki da dakakken cray fish akai, kisa maggi, gishiri, attarugu, albasa da mai akai ki juya, idan yayi kauri ki kara ruwa yazama kamar kullin alala, ki zuba a gwangwani ko leda ki dafa.
5⃣ALALAN DOYA
Ingredients:
* Doya
* Nama
* Kwai
* Hanta
* Maggi da gishiri
* Currry
* Mai
Procedures:
Ki daka doyarki danya a turmi ko ki markada ta, ki markada danyan namanki, ki markada kayan miyarki ki zuba a kai, ki zuba maggi, gishiri da curry, ki zuba hantarki da kika yanka kanana, ki yanka dafaffen kwanki kanana, ki zuba kisa mai ki juya sosai, sai ki dinga zubawa a leda kina kullewa, ki zuba a tukunya ki zuba ruwa akai ki dafa minti ashirin ya dahu.
6⃣ALALAN KWAI, NAMA DA HANTA
Ingredients:
* Kwai
* Nama
* Hanta
* Albasa
* Attarugu
* Maggi da gishiri
* Curry
* Mai
Procedures:
Ki tafasa nama da hantarki da tafarnuwa da thyme da maggi da gishiri, ki yanka namar kanana, hantar kuma ki daka ta ki hada su guri daya, ki jajjaga albasa da attarugu ki zuba a kai ki fasa danyen kwai ki zuba akai, kisa maggi, gishiri, curry da mai ki juya sosai, ki zuba a leda ko gwangwani, ki dafa wannan alala yana gina jiki sosai.
7⃣ALALA DA MAI DA YAJI
Ingredients:
* Wake
* Attarugu
* Albasa
* Maggi da gishiri
* Alayyahu
* Manja
Procedures:
Ki wanke wake ki cire dusa ki zuba attarugu da albasa ki kai inji a markado miki, kisa maggi da gishiri ki juya sosai, ki shafa manja a gwangwanayenki ki dinga zuba kulli waken a gwangwanayen, idan kin zuba a tukunya ki turara, idan ya dahu sai ki juye a kwano ki zuba manja da yajin barkono akai.
8⃣ALALAN AGUSHI
Ingredients:
* Agushi
* Wake
* Kifin gwangwani
* Hanta
* Attarugu
* Albasa
* Maggi da gishiri
* Curry da mai
Procedures:
Ki sami wakenki gwangwani uku ki wanke ki fidda dusar, ki sami agushinki gwangwanin madarar ruwa daya ki soya, ki zuba waken, ki sami attarugu da albasa ki kai a markada miki, ki zuba kifin gwangwani guda biyu, ki zuba hantar ki, maggi, gishiri, curry da mai kadan, ki juya sosai, ki buga sosai, ki zuba kulla a leda ki dafa.
ALALEN DOYA
doya
kwai
hanta
maggi
gishri
curry
mai
albasa and attaruhu
garlic idan kina so
dafarko zaki samu doyanki ki gurza a abun gurza kubewa sai kiyi blendng tare da attaruhu da albasa idan kin kammala sai kizo ki zuba spices dnki da mai ki dan buga kullun sai ki yanka dafaffen kwanki da hanta a cikin kulln ki kulla a leda ki dafa yanda ake dafa alale.
ki barshi ya dahu sosai sannan idan an gama sai servng ku gwada walh akwai dadi.
Tags:
Girke-Girke (Cookings)