*_LAULAYIN CIKI YASA INA WAIWAYE A SALLAH???_*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum malam Dan Allah macece take fama da yawan zuban yawu a bakinTa na laulayin ciki, Wanda yakai kafun nayi raka'a daya ya cikamun baki sai na dan juya in zuba akan tsumma, sallan yayi ko bani da halin juyawa kadan?
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam To 'Yar'uwa Annabi S.A.W yana cewa: "Waiwaye a sallah wani faucewa ne da Shaidan yake fauta daga sallar bawa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lambata: 718. Malamai suna cewa waiwaye a sallah makaruhi ne saboda hadisin da ya gabata.
Waiwaye yana halatta idan akwai bukata, saboda akwai lokacin da sayyidina Abubakar ya fara limanci, saboda Annabi S.A.W baya nan, bayan Annabi S.A.W ya dawo sai ya shigo masallaci, sahabbai suna ganinsa sai suka fara tafi, sai sayyadina Abubakar ya waiga lokacin da ya ji tafi ya yi yawa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2544.
Malamai suna cewa: waiwayan da Abubakar ya yi yana nuna hallacin yin waiwaye saboda bukata, tun da Annabi S.A.W bai masa inkari ba.
Don neman karin bayani duba: Fataawaa nurun Aladdarb 9\225.
A bisa abin da ya gabata, ya hallata ki dinga yin waiwaye saboda zubar da yawun da ya zama lalura, saidai duk abin da aka halatta saboda bukata, ba'a so a wuce gwargwadonta.
Allah ne mafi sani.
19\4\2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_______________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.