*_KURAKURAN MALAMAI ABIN GAFARTAWA NE KO DA A MAS'ALOLIN AQIDA NE!!!_*
Sau da yawa a kan samu matasa masu zafin kishin Sunna da son da'awa da karantarwa, wadanda suka yi shigan karfi ma ilimi, sukan bibiyi kurakuren malamai suna bayyana wa mutane –wai- suna da kurakurai, sun saba wa Manhajin Salaf a kaza da kaza, suna yadawa a cikin jama'a, alhali kuskure abin gafartawa ne a wajen Allah, ko da kuwa a mas'alolin Aqida ne.
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce:
ﻻ ﺭﻳﺐ ﺃﻥ ﺍﻟﺨﻄﺄ ﻓﻲ ﺩﻗﻴﻖ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻣﻐﻔﻮﺭ ﻟﻸﻣﺔ، ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺫﻟﻚ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺎﺋﻞ ﺍﻟﻌﻠﻤﻴﺔ، ﻭﻟﻮﻻ ﺫﻟﻚ ﻟﻬﻠﻚ ﺃﻛﺜﺮ ﻓﻀﻼﺀ ﺍﻷﻣﺔ . ﻭﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻐﻔﺮ ﻟﻤﻦ ﺟﻬﻞ ﻭﺟﻮﺏ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺗﺤﺮﻳﻢ ﺍﻟﺨﻤﺮ ﻟﻜﻮﻧﻪ ﻧﺸﺄ ﺑﺄﺭﺽ ﺟﻬﻞ ﻣﻊ ﻛﻮﻧﻪ ﻟﻢ ﻳﻄﻠﺐ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻓﺎﻟﻔﺎﺿﻞ ﺍﻟﻤﺠﺘﻬﺪ ﻓﻲ ﻃﻠﺐ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺑﺤﺴﺐ ﻣﺎ ﺃﺩﺭﻛﻪ ﻓﻲ ﺯﻣﺎﻧﻪ ﻭﻣﻜﺎﻧﻪ ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻣﻘﺼﻮﺩﻩ ﻣﺘﺎﺑﻌﺔ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺑﺤﺴﺐ ﺇﻣﻜﺎﻧﻪ ﻫﻮ ﺃﺣﻖ ﺑﺄﻥ ﻳﺘﻘﺒﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﺴﻨﺎﺗﻪ ﻭﻳﺜﻴﺒﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﺟﺘﻬﺎﺩﺍﺗﻪ ﻭﻻ ﻳﺆﺍﺧﺬﻩ ﺑﻤﺎ ﺃﺧﻄﺄ ﺗﺤﻘﻴﻘﺎ ﻟﻘﻮﻟﻪ : } ﺭﺑﻨﺎ ﻻ ﺗﺆﺍﺧﺬﻧﺎ ﺇﻥ ﻧﺴﻴﻨﺎ ﺃﻭ ﺃﺧﻄﺄﻧﺎ { . ﻭﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺟﺰﻣﻮﺍ ﺑﺎﻟﻨﺠﺎﺓ ﻟﻜﻞ ﻣﻦ ﺍﺗﻘﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ؛ ﻛﻤﺎ ﻧﻄﻖ ﺑﻪ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻭﺇﻧﻤﺎ ﺗﻮﻗﻔﻮﺍ ﻓﻲ ﺷﺨﺺ ﻣﻌﻴﻦ؛ ﻟﻌﺪﻡ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺑﺪﺧﻮﻟﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺘﻘﻴﻦ .
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ( /20 165 - 166 ) ، ﺩﺭﺀ ﺗﻌﺎﺭﺽ ﺍﻟﻌﻘﻞ ﻭﺍﻟﻨﻘﻞ ( /2 315 )
"Babu kokonto, lallai kuskure a kananan mas'alolin ilimi (wadanda suke ba bayyanannu ba) abin gafartawa ne ga wannar al'umma, ko da kuwa kuskuren ya kasance ne a mas'alolin ilimi (na Aqida).
In ba haka ba da mafi yawan malamai masu falala na wannar al'umma sun halaka (sun hadu da azaba a Lahira). Saboda idan Allah zai gafarta ma wanda ya jahilci wajabcin Sallah da haramcin shan giya saboda ya rayu a garin jahilci, tare da kasancewarsa bai nemi ilimi ba, *TO MALAMI MAI FALALA MAI IJTIHADI (KOKARI) WAJEN NEMAN ILIMI GORGODON ABIN DA YA RISKA A ZAMANINSA DA WURIN DA YAKE NA ILIMI, IDAN NIYYARSA TA ZAMA BIYAYYA WA MANZON ALLAH NE GORGODON IYAWARSA, TO SHI YA FI CANCANTA ALLAH YA KARBI KYAWAWANSA, YA BA SHI LADA A KAN IJTIHADODINSA, KUMA BA ZAI KAMA SHI A KAN ABIN DA YA YI KUSKURE BA,* don tabbatar da fadin Allah: (Ya Ubangijinmu kar ka kamamu in mun manta ko mun yi kuskure).
Ahlus Sunna sun tabbatar da samun tsira a yanke ga dukkan wanda ya ji tsoron Allah (T), kamar yadda Al- Qur'ani ya fadi hakan, kawai sun dakata ne a game da mutum mu'ayyani (sananne), saboda rashin sanin shigansa cikin masu Taqawar (a bisa tabbas da yakini)".
*ALLAH YA SAKA WA MALAMAN SUNNA DA ALHERI, WADANDA ALLAH YA SANYA SUKA ZAMA SABABI NA YADUWAR SUNNA A NIGERIA, A DALILINSU MUTANE DA YAWA SUKA FITA DAGA SHIRKA DA BIDI'A, ZUWA GA TAUHIDI DA SUNNA, DUK KUWA DA KURAKUREN DA WASU SUKE AIBANTASU DA SU.*
*_ALLAH YA TAIMAKI RAYAYYU DAGA CIKINSU, YA KARA SHIRYAR DA SU, WADANDA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA ALLAH YA YI MUSU GAFARA DA RAHAMA._*
Daga:- Dr. Aliyu Muh'd Sani
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.