*_LOKACIN YAYE YARO A MUSULUNCI_*
*Tambaya:*
Aslm ya shaikh :Allah yaqara wa doctur lafia amin. Don Allah mallam wane lokaci ne mafi inganchi da ya dace a yaye yaro daga barin shan nono a shariance? Nagode Allah yasaka da alkhairi amin.
*Amsa:*
To dan'uwa ina rokon Allah ya amsa addu'arka, Lokaci Mafi çıka na yaye yaro shı ne: idan ya kai shekaru biyu, kamar yadda aya ta: 233 a suratul Bakara ta tabbatar da hakan, saidai ya halatta a yaye yaro kafin ya cika shekaru biyu, mutukar ba zai cutu ba, kuma iyaye guda biyu sun cimma daidaito akan hakan.
Don neman karın bayani duba: Tafsirin Qurdubi 3/162.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.