♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*13*
da ɗare Usman ya kawoma Momi kayan (tufafi) data aikeshi ya siyo,
aiko murna gurin Mairo ba'a magana sai tsalle take tana wani shafar tufafin tana jefasu sama tana rawa.
duk wani bachin rai dake ranta ranar gushewa yayi sai faman godiya take yima momi.
tun abun naba Momi dariya har ya koma bata tsoro ganin irin murnar da take kamar zata haukace sai faman uhu take, tana daredare harda hawaye,
momi dai da taga ba kanta baro mata ɗakin tayi ta sauko k'asa,
nan ta tararda Qasin yana aikin rubuce2,
guri ta samu ta zauna suka soma fira.
Mairo na jin muryarsa ta kwaso tufafin ta nufo downstairs da gugu tana faɗin “Qasin kaga tufafina da-”
kasa karasa maganar tayi saboda wani mugun kaye da tasha saman tile aiko nan kuka ya chaja salo ta koma yin na gaske,
dariyace tazo ma Qasin haka ya matseta ya nufeta ya tadata tsaye yana bata hak'uri yana murza mata gurin data gimu.
momi kan faɗa ta hau yi mata “yarinya ba kai sai bak'ar hauka tun ɗazu take murnar tufafin nan kamar mahaukaciya kekan kauyenciki yayi yawa Maryam”
Qasin na dariya yace “haba momi koni ai murna zanyi inna samu sabon tufafi zuwa fa tayi ta gwada min ko?”
kai ta ɗaga masa tana kuka, handkerchief ɗinsa ya ciro yana share mata hawaye.
“ya isa haka jeki gwada tufafin mugani suna miki kyau”
da ininniyar kuka tace “thom”
ta nufi ɗaki.
tana shiga ta cire kayan jikinta ta ɗauki wata diguwar riga tasa da gudu ta fito ta nufo parlour.
bata tararda shiba sai momi dake zaune saman kujera tana kallon tv,
gurinta ta nufa tana nuna mata kayan, koɗata momi tayi tana yaba yadda kayan suka karɓeta nan dariyarta ta dawo ta rik'a tsalle tana mulmula a k'asa saida momi ta soma yi mata faɗa sannan ta tashi ta nufi ɗaki.
''' * * *'''
tun daga lokacin Mairo bata k'ara saka tufafinta na kauye ba saidai wayanda momi ta siya mata,
kuma ba laifi Usaman ya iya zaɓi dan duk tufafin data saka saisun yi mata kyau sun k'arɓi jikin ta,
kyau ta ma ba laifi da farinta sai kara fitowa yake ga gashin kanta kullum sai momi ta gyara mata shi,
taci maikyau tasha maikyau tasa maikyau wasa wasa cikin wata 2 tayi bulbul kamar ba itaba,
aiki kan yanzu Mairo ta ɗan fara sabawa dan kullum tare da momi suke haɗa breakfast kuma duk wani karamin aiki ita momi take sawa tayi tun tana fushi har ta gaji ta daina sai in taje ɗaki ta rika kuka tana zagin momi da cire mata albarka,
zancen guduwa yanzu ta daina tunda taga momi bata bari a fita da ita kuma in zata fita bata zuwa da ita babu yadda batayi ba momi tak'i yarda duk wata dabara ta ta saita rushe ta daina ma yima momi zancen ta hakura,
*_3 months later....._*
yau da far'ah Mairo ta tashi saboda tayi markin Gwaggo,
koda Momi ta shigo ta tasheta zaune ta tararda ita harma tayi alwala tana sanye da hijab,
da mamaki momi ta shiga bathroom bayan ta ɗoro alwala ta fito ta nufi waduraf tana faɗin “Maryam ya akayi yau kika rigani tashi?”
carbi ta nunawa momi tana wani gyaran murya kamar wata babbar mace wai ita mai tasbihi ba a magana,
“hmm Maryam manya”
momi ke faɗar haka tana k'ok'arin ɗaura zane,
hijab tasa ta shimfiɗa carpet ta rik'a carbin tana salati har aka tada sallah sannan suka bi zan'in masallacin dake kusa dasu,
suna karewa bayan suyi yan addu'o'e suka nufi kicin.
*_8:45am_......*
Mairo ta shiga jera breakfast a dining sai tsaki take tana faɗin “mumo yau munyi rana”
tsayawa tayi tana kallon agogn dake manne gefen gurin tana tunani yadda momi ta koya mata,
ta daɗe a tsaye tana kallon agogon ganin bata tuna ba yasa ta shiga shirmen ta “kinga fa mumi har wannan mai laulaye tayi (8) da mai k'afa ɗaya (4) da mai kai sama (9) gaskiya munyi rana yau”
da dariya momi ta fito kincin ta nufo dining tana faɗin “waike Maryam yaushe zaki daina wannan shirmen naki ne? ke kullum ana koya miki abu amman kamar kara toshe miki k'wak'walwa ake”
turo baki tayi ta nufi kujerar data saba zama ta zauna,
momi bata sake cewa komai ba ta shiga zuba mata abincin harsu Usman da Nura da Siraj suka fito suka nufo dining,
bayan sun zauna kowannensu ya shiga zubama kansa,
har suka fara ci Mairo bata ci nata ba sai kunbure2 take tana harararsu duk da momi ce take son ta harara amman ba dama.
babu wadda ya tanka mata sai Siraj dake k'ok'arin zaunawa,
“waike lafiya kike hararar mutane?”
saida tayi kwafa sannan ta kalleshi tace “ina ruwanka dani”
tashi yayi da niyar ya doketa momi ta tareshi “ai tace maka ina ruwanka da ita bai isaba?”
“tho momi baki ganin yadda take hararar mutane”
“ba da kai take ba ni take son harara bata da dama saboda nace bata gane agogo”
komawa yayi ya zauna yana dariya “LOL yarinya aike kullum liki minandak'u ce kulli yaumin ɗifɗif”
kifa kanta tayi da dining tana kuka,
momi ta kalleshi da siffar masifa “wai Siraj mi yasa kake wasa da ita ne bafa tabashiyarka bace mahaifinta da naku uwa ɗaya uba ɗaya suke”
hannu ya ɗaga “tho momi kice ta daina wasa dani”
“ai kai ka soma wasa da ita gashi har sauran suna son yi”
jan zib yayi a bakinsa alamar bazai kara cewa komai ba,
© *Khadeeja Candy*
Tags:
Littatafai (Novels)