Mairo 55

♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

*55*

Da far'ah Mairo ta shigo cike da ladabi ta k'araso kusa da Abbah ta risina.
"Abbah ina wuni?"
Da murmushi Abbah ya amsa "Lafiya kalau Maryam barka da fita wanka"
"Yauwa Abbah yanzu ka zo? Yasu Momi?"
"Lafiya kalau suke suna gaishe ki kuma suna miki barka da fita wanka"
"Ina amsawa Abbah ina Siraj?"
"Yana can gida am.. Maryam" Ta É—aga kai ta amsa "Na'am Abbah"
"Jeki waje kice ma direba ya baki jika tana nan cikin Mota ki kawo"
"Toh Abbah" Tashi tayi ta fita.
Bayan yan mintuna ta shigo rik'e da *BABBAR JAKA* ta aje mishi gabanshi
"Abbah gashi"
Abbah yasa hannu aljihu ya ciro kuÉ—i masu É—an dama ya É—ora saman jakar.
"Am...Maryam wannan kuÉ—in da kayan da kika gani na neman aurekin ne Qasin ya aiko yana son idan an Amince mishi kizo a matarshi ta biu"
Da sauri ta nuna kanta "Abbah ni?" Ta tambaya tana zaro ido. Abbah ya gyara zamanshi "Eh kefa Maryam amman fa ba cilas bane shima ya saka kanshi cikin manema ne idan kin aminta shi kenan sai ayi yar gida indan kuma baki ra'ayinshi toh mu duk wanda kika kawo zamuyi maraba dashi".
Nan da nan idonta suka kawo ruwa "Abbah bana son aure yanzu ni bana son aure dan Allah Abbah kar kumin aure yanzu kaji?"
Mamakine ya bayyana a fuskar Abbah "Baki son aure kamar yaya Maryam ai duk É—an aure bazai k'i aure ba"
Gwaggo tace "Ita fa fun abinda ya faru naga tsoro ya kamata duk tabi ta chanja"
"Karki kuskura kisa abinda ya faru da Halilu cikin ranki har ya iya zama wani dalili na tsorata ki haka Allah yake lamarinsa babu yadda bawa zaiyi sai godiya da kuma hak'uri" FaÉ—ar Abbah.
Kwanta tayi jikin Gwaggo tana kukan da baza'ace ba shagwaɓa bace.
Nisawa Abbah yayi ya kalli Gwaggo "Ina ganin lokaci ya kamata mu bata tayi tunani sannan muni daga bakinta"
Gwaggo ta lasa baki "Toh ba nak'i zancen kaba amman dai ita Mairo har wani tunani tasan ta tsaya tayi ita dai tsoro ne kawai take ji kuma nasan In'sha Allahu zata daina"
"A'a mu barta dai har nan da zuwa sati tukuna"
Kai Gwaggo ta gyaÉ—a "Toh Allah ya kaimu ya saukwake"
Abbah ya amsa da 'Amin' Nan ta kalli Mairo "Tashi ki shiga É—aki ni bari na duba abincin can ina ga ruwan ya tafasa"
Tashi tayi ta nufi É—aki Gwaggo kuma ta nufi gurin girkinta.
Sai bayan La'asar Abbah ya baro garin daf da magriba ya iso gida.

Bayan Sallar Isha'i Qasin ya shigo part É—in Momi.
Siraj kawai ya tararda zaune yana danne danne waya. Saida ya zauna sannan ya É—ago kai ya kalleshi "Yaya" "Na'am Siraj chatting kake ne"
"Eh Wallahi na É—an kwana biu ban hau bane ya naga fuskar ka kamar É—auke da damuwa?"
Ajiyar zuciya ya sauke "Ina Momi?"
"Tana part É—in Abbah"
"Bata faÉ—a maka yadda Abbah yayi da Maryam ba?"
Dakan uku-uku gabanshi yayi nan ya aje wayar gefe ya fuskanci shi sosai "Bata faÉ—a min Wallahi miya faru?"
Saida ya sauke sauke wata ajiyar zuciyar sannan ya soma magana "Abbah yace ana faÉ—a mata kuka ta dinga yi tana faÉ—in ita bata son aure kowa yayi na'am da maganar yanzu matsalar daga gurinta take"
Shiru Siraj yayi ya tsorama Qasin ido "Wai yaya da gaske son ta kake?"
Qasin ya kalleshi "Hakan nake tunani"
"Tunani kake ma kenan"
Kawarda fuska yayi kamar baya son maganar.
"Toh yanzu ya zakayi?"
"Nima ban saniba banaan miye mafita ba"
Siraj ya busarda iskan bakinshi tare da sauke ajiyar zuciya "Idai har kana sonta toh kaje ka lallaɓata koda a waya ne. Maryam ba tada matsala tana da sauk'in kai. Kuna kasan ba wani wayau ne da ita sosai ba kana lallaɓa zaka shawo kanta wannan shine kawai nake ganin mafita"
Jimm Qasin yayi kamar mai tunani. can kuma ya jinjina kai "Ina ganin haka zanyi ka kawo shawara zan samu lokaci inje In'sha Allah"
Tashi Siraj yayi yana faÉ—in "Good luck" Ya nufi k'ofar fita.
"Thank you very much" Daf da zai fice Qasin yayi mishi godiyar yana murmushi.

Saida dare ya raba sannan ya tashi ya nufi part É—in shi.
A hankalin ya tura k'ofar parlor ya shiga.
Da sauri Mansura ta tashi tsaye tana sanye da kayan bachi "Qasin ina kaje?"
K'arasowa yayi kusa da ita ya dafa kafaÉ—anta "Miyasa kika tambaya my dear?"
"Dubi fa agogo ka gani Qasin É—aya saura"
Ta faÉ—a fuskarta É—auke da damuwa.
Saida ya kalli agogon sannan ya shafa gefen fuskarta
"Ai ni bansan dare yayi ba ina can gurin fira"
"Fira?"
"Eh aure fa zan k'ara"
Wani tsire baki tayi "Taf ai Wallahi ko baka isa ba baza ka fara ba"
"Saboda mi?"
"Saboda Qasin dan Mansura kawai akayi shi. duk matar da tace zata saka sonka cikin ranta toh zata wahalarda kanta ne kawai"
Gira ya É—aga mata "Allah ko?"
"Baka yarda ba kenan nidai yanxu faÉ—amin ina kaje?"
"Ina tunatar dake a koyaushe Mansura nifa nake auren ki bake kike aurena ba dan haka inda naje inda zanje duk bai shafeki ba kedai yanzu muje mu kwanta"
Bai jira abinda zata ce ba ya duka ya tallabeta kamar yar baby ya nufi bedroom É—inshi da ita.

'''*** *** '''
*K'auye...*

"Alhamdulillahi yanzu kan cikina ya cika sosai" Mairo ta faÉ—a tana gyatsa.
Murmushi Gwaggo tayi "Haba ko kefa yanzu ba sai kiji k'arfi-k'afi ba haka nakeso kullum naga cinki kin k'oshi"
"Ai yanzu ina cin abinci ba laifi"
"Eh ai bance baki ciba amman dai yau kinfi ci da yawa dan rabon da kici abinci haka har na manta"
Mairo zatayi magana wani yaro yayi sallar.
"Assalamu alaikum wai ance ana salama da Mairo"
Mairo ta mere baki.
"Taf lallai ma jeka kace bata nan wani irin sallama yanzu da rana tsaka"
Gwaggo ta kalleta "A'a ba ayi haka ba baki san ko waye ba maza ba a musu wulakanci"
"Kofa wanene ni baza niba yanzu da rana ake fira"
"Saifa kinje ai bakinsan uzurinsa ba" ta kalli yaron "Kai jeka kace tana zuwa"
Juyawa yaron yayi ya fice bayan ya amsa da toh.
Gwaggo ta kalli Mairo "Tashi É—auki mayafinki kije nace gaki nan zuwa"
Tashi tayi tana turo baki "Amman dai ni gaskiya Gwaggo bana son irin abun nan da kike min ni gaskiya wani karon ba zani ba"
Kai Gwaggo ta É—aga mata "Eh naji yanzu dai jeki" kamar ta fasa kuka ta É—auki hijabinta da kwanon da taci abinci ta fice.

Fitowa yayi daga cikin motar. yana sanye da wando pencil black color da blue t-shirt. Jingine yayi jikin motar yana kallon k'ofar gidan.
Da ture-turen baki ta fito suna haÉ—a ido ya jefeta da wani kyakkyawan murmushi.
Murmushi ita ta mayar mishi cike da fa'ah ta k'araso gurin da yake.
"Lahhh Yaya Qasin daman kaine?"
Murmushi ya sake mata as respond.
"Amman shine baka shiga ba kace ana nemana?"
Kai ya É—aga mata still yana murmushi.
"Toh mu shiga ciki mana nida Gwaggo duk mun É—auka ma wani ne Wallahi"
Sai a lokacin yayi magana.
"A'a bazan shiga ciki ba"
"Saboda gurin ki nazo ba ba gurin Gwaggo ba"
"Ni?" ta nuna kanta.
"Eh kefa nazo taÉ—i ne dan kar wasu su fini zuga su kwace min ke"
K'asa tayi da kanta tana guntse murmushi daya zoma.
Wata irin kunya ce ta baibayeta rungume jikinta tayi kamar mai jin sanye.
Fuskarta Qasin ya lek'a "Toh duk salon k'iyayyar ce kodai baki jindaÉ—i zuwan nawa bane. daman Abbab yace kince baki sona"
Da sauri ta kalle tana zaro ido "Lahhh ni Wallahi ban ce ba"
"Abbah yace lokacin da akayi miki maganar kuka kika rigayi"
"Eh ba kai nake yima kukan ba ni bana son aure ne kawai" Cike da shagwaɓa tayi maganar tana son yin kuka.
"Maryam...?"
Amsawa tayi ba tare data kalleshi ba.
"Na'am"
"Bakisan Aure sunnan Annabi bace kike cewa bakiso karatunki bai kaiki gurinda Annabi (S. A. W) yake cewa Aure Sunna tace duk wadda yak'i Sunna ta toh baya tare dani. shifa da kanshi yace kuyi Aure ku haifafa dan inyi alfahari da yawanku Ranar Alk'iyama.
Maryam mi yasa baki son Aure? Bakison ki zauna tare dani da Momi. Maryam ina sonki bazan cutar dake ba bazan miki wani abuba please ki yarda dani"
Kallonshi tayi fuskarta na nuna abinda yake zuciyarta k'arara.
"Yaya nifa ba ce bana sonka ba ni ba sonka ne bana yiba Auren ne bana so tsoro nake ji"
"Toh ki daina jin tsoro dan Halilu ya rasu baya nufin nima zan rasu kinji dan Allah ki amince da maganar Aurena Maryam kinji?"
Kai ta É—aga mishi tana lank'wasar yatsun hannunta.
Ya É—an daÉ—e yana fira da ita yana kwantar mata da hankali saida yaga ta soma gajiya da tsayuwar sannan yasa hannayenshi aljihu yace "Nikan bari na wuce kar tsayinki ya k'are ki faÉ—ar min"
Dariya tayi "Toh mu shiga ciki sai mu zauna"
"A'a ni ba zan shiga ba yanzu zan wuce kice dai ina gaidata"
"Da gaske ba zaka shiga ba?"
"Allah bazan shiga ba wannan zuwan naki ne bana kowa ba"
Hannu yasa Aljihu ya ciro kuÉ—i masu É—an dama ya mika mata.
Hannu biu tasa ta k'arɓa "Ahh Yaya duka?"
Nan ya sake mik'a mata wasu "Wannan naki ne wannan kuma na Gwaggo kice ina gaida"
Farin ciki ne wanwar a zuciyarta "Na gode Yaya Allah ya saka da Alheri" Murmushi yayi mata yana mamakin hali irin na Mairo watau har yanzu bata daina halinta na son kuÉ—i ba.
BuÉ—e Motarshi yayi ya shiga "Na tafi Maryam kiyi min Addu'a"
"Allah ya kiyaya ya tsare na gode sosai"
"Kada ki damu amman fa zanyi kiwarki"
Rufe ido tayi ta nufi gida da gudu.
In banda kallo babu abinda ya bita dashi yana murmushi har ta shige. Haka kawai sai yaji tayi mugun burgeshi.
Ya daÉ—e yana kallon k'ofar gidan sannan ya tada motar ya kama hanya.

FaÉ—awa Mairo tayi jikin Gwaggo tana dariya ta nuna mata kuÉ—in.
"Ahh Mairo ina kika samo wanene yazo?"
Da dariya tace "Yaya Qasin ne Wallahi"
"Wane Qasin dai?"
"Na birni mana na Momi"
"Wai Qasimu kike magana?"
"Eh nayi-nayi dashi yace shi ba zai shigo ba wai guna yazo saidai nace yana gaishe ki"
"Gurin ki kuma?"
"Eh wai shi fira yazo"
"Au" Gwaggo tayi dariya "Sai yanzu na gane hausarki toh Allah yasa ki k'arɓa mashi da ga dukan alamu dai yana sonki kece dai baki sonshi"
"A'a Gwaggo nifa bance bana sonshi ba kune da kuda Abbah kuka ce amman ni bance bana sonshi ba"
"Ah toh kina sonshi kenan yanzu fa amincewarki kawai muke jira da kowa yayi na'am da Auren nan kice kawai ake jira kin amine ko?"
Murmushi tayi ta duk'unk'une kanta cikin hijab ta shige jikin Gwaggo.

*** *** ***

Cikin satin zuwan Qasin uku k'auye duk zuwan da yake bai taɓa yarda ya shiga cikin gidan ba.
Saidai yace yana gaida Gwaggo ko ya aika mata da kuÉ—i ko siyayyah.
A yan kwanakin nan da yayi yana zuwa sai duk yaji ya hak'u da ita. Ita idan tana tare dashi sai ta riga jinta cikin wani yanayi na daman.
Idan zai tafi har jin take kamar ta bishi har dai zuwanshi na ukun nan daya É—auketa suka tafi zaga gari.

*Saturday Morning*

Duk zazzaune suke part É—in Momi suna fira. Kasancewar yau weekend.
Sallamar da Abbah yayi tasa duk suka kalli k'ofa tare da amsawa. Kusa da Momi ya zauna yana amsa gaisuwar da suke mishi.
Nan suka sake dasa wata sabuwar firar yan siyasa. Sai kusan sha biu na rana Qasin ya kalli agogo yace "Bari na tashi akwai inda nake son zuwa"
Abbah ya kalleshi "Qasin baka tambaye ya akayi akan maganar Maryam ba kasan jiya sati É—aya kenan"
Murmushi yayi "Abbah tsoro nake ji"
"Tsoro sai kace ba Namiji ba" Momi ta faÉ—a
"A'a bafa irin wannan tsoron nake nufi ba na kar naji mummunan amsa nake nufi"
"Toh ba zakaji ba dan ta aminci jiya da yamma Baba Saminu ya kira yace min yarinya tace ta amince"
Wani kalar murmushi ne yazo ma Qasin ya kasa É“oye farin ciki shi sai dariya yake haka kawai yaji wani irin jindaÉ—i ya mamaye shi bakinshi har kunne ya kalli Abbah "Amman na jindaÉ—i Wallahi Allah ya tabbatar da alheri banyi tunanin zata amince ba"
Usman ya kalleshi yana dariya "Ashe yaya kana sonta"
Harara ya watsa mishi ya kawarda kai.
Siraj ya dafa shi yana murmushi "Congratulations Bros Allah ya saka albarka a ciki"
Duk suka amsa da 'Amin' suna dariya.
Siraj ya ciro wata takarda cikin aljihu shi ya mik'awa Abbah yana faÉ—in "Abbah nafa samu transfer"
"Transfer?" Duk suka kalleshi da mamaki.
Abbah ya karɓa yana tambaya "Zuwa ina kuma?"
"Abuja suka mayarda ni Abbah"
Qasin ya kalleshi fuskarshi da É—an damuwa "Amman dai gaskiya ban jindaÉ—i ba anya zaka iya zama can kuwa?"
"Zan iya mana ai transfer tazo a daidai dan daman na gaji da garin nan"
Abbah yace "Toh Allah yasa haka shine mafi alheri"
"Amin Abbah nima haka nake rok'o"
Momi dai uffan bata ceba saidai tunda ya faÉ—i maganar yanayin ta ya chanja.
Har suka gama tattauna akan maganar transfer bata ce k'ala ba saima tashi da tayi ta bar gurin.

*© KHADEEJA CANDY
Post a Comment (0)