*_ME YASA AKA SHAR'ANTA SAKI?_*
*Tambaya:*
Malam na ga Allah yana son aure, to don Allah me yasa sharia ta yarda da saki ?
*Amsa:*
Addinin musulunci ya yi umarni da dukkan abubuwan da za su karfafa aure, sai dai wani lokacin ma'aurata suna haduwa da wasu mushkiloli wadanda za su sanya rabuwarsu ta zama ita ce ta fi alkairi, Allah Ya na cewa a cikin haka: "Idan ma'aurata biyu, suka rabu, sai Allah ya wadata kowa daga yalwarsa". Suratu Annis'ai aya ta: 130.
Akwai hikomomi da dama, da suka sa Allah ya shar'anta saki, ga wasu daga ciki:
1. Zai iya yiwuwa daya daga cikin ma'aurata ya ga ba zai iya jure dabi'un abokin zamansa ba, ya kuma shiga damuwa saboda haka, sai ya kasance babu wata hanya da za'a iya warware mushkilar sai ta hanyar rabuwa.
2. Idan har ba'a shar'anta saki ba, to daya cikin ma'aurata idan ya gaji da dan uwansa zai iya neman hanyar da zai huta daga shi, ta hanyar kashe shi, ko kuma illanta shi, kamar yadda hakan ya faru ga wasu daga cikin ma'aurata, ga wasu misalai dana gani da idona wasu kuma na ji labarinsu:
A. Akwai matar dana sani, wacce saboda kiyayyar da take yiwa mijinta ta saka masa garin batiri a cikin abincinsa, saboda kawai tana so ya mutu ta huta da shi.
B. Akwai wanda na sani, saboda da kin da matarsa take masa, ta dauki reza za ta yanki al'aurarsa lokacin da suka zo saduwa.
C. Akwai wacce ta kashe mijinta, saboda ba ta son shi.
*DUKA WADANNAN MUSHKILOLIN ZA'A IYA WARWARE SU TA HANYAR SAKI.*
3. Idan mace mijinta ba ya birgeta za ta iya rikar kwarto ya rinka biya mata bukatarta, kamar yadda shima namiji zai iya yin hakan, hakan kuma zai haifar da barna a cikin al'umma.
4. Zai yi wahala namiji ya yi adalci ga matar da ba ya sonta, ka ga saki zai zama hanya mafi sauki wajan warware matsalar.
Allah ne mafi sani.
31/8/2018.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- ΓbΓ»bΓ€kΓ₯r ΓkΓ’.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren π *_MIFTAHUL ILMI_* π (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.