MIJINA BA YA AZUMI SAI YA GA WATA, KO YA WAJABA NA YI MASA BIYAYYA???

MIJINA BA YA AZUMI SAI YA GA WATA, KO YA WAJABA NA YI MASA BIYAYYA???


                              *Tambaya*
Salamun alaikum, Dr. Tambaya ce aka jefa mani ina gabatar da darasi wa mata a garin Firji: mace ce mijinta bai yarda ya dauki azumi ba sai ya ga wata da kansa (bai yarda da sanarwar Sarkin Musulmi ba), to inda mushkilar take shi ne, ita matarsa ta yarda da sanarwar Sarkin Musulmi amma sai ya ce kada ta kuskura ta dauki azumin, to shin minene matsayinta? Domin ta ajiye azumin saboda tsoron kada ya wulaqanta ta.


                                      *Amsa*
Wa'alaikum assalam A Zahiri ba za ta masa biyayya a nan ba, Tun da Azumi rukuni ne daga cikin ginshikan musulunci.

Annabi S.A.W yana cewa: 
إنما الطاعة في المعروف
Ana yiwa jagora biyayya ne idan ya yi umarni da abin da ya dace da sharia"
Sannan yana cewa: "Ana yin azumi ne ranar da mutane suke yin azumi"

Allah ne mafi sani

23/05/2018

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.


Post a Comment (0)