✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*ABOKIN FIRA
*
*Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_
*DRS NA 018*
*Yadda Wata Mata ta Hana Mijinta Shan Sigari*
Wata mata. Rannan sai ta yi tunanin hanyar da za ta yi masa
wa’azi ba tare da ya samu wata kafa da zai yi mata gardama ba.
Watarana suna zaune sai ya dauko karen sigarinsa zai kunna, a
cikin raha sai ta tambaye shi, nawa ake sayar da karen sigari guda
daya? Sannan kuma guda nawa yake sha a wuni? Da ya ba ta amsa sai
kuma ya kara da cewa, ko kina so ke ma ki fara sha ne? Sai ta ce masa
a’a. Amma dai ni a matsayina na iyalinka akwai abin da nike sha’awar
in saya ba sigari ba. Ba tare da jin wata damuwa ba ya yanka mata
kudin da zai rika ba ta a madadin sigari da yake sha.
A kwana a tashi yana ba ta kudi duk safiya ashe matar nan tana
ajiye kudin nan har suka taru suka yi yawa sosai. Rannan sai ta aika
aka canjo mata su aka kawo mata sababbin kudi daga banki. Suna
zaune suna fira sai ta fito da kudin, kamar da wasa sai ya ga ta dauko
ashana za ta kyasta masu. Gogan naka sai ya rike hannunta. Ba ki da
hankali ne? A cikin sassaukar murya sai ta ce masa, ba ka san ko kudin
me ne ba? Ya ce, ko ma na mene ne ya za ki kona su? Ta ce, ai kudin
sigarina ne da kake ba ni. Ni ma yau zan kona su gaba daya. Nan take
sai jikinsa ya yi sanyi, ya fara ba ta hakuri. Sai ta ce da shi ka ga ni
yanzu ko na kona wadannan kudin baa bin da zai same ni. Amma kai a
duk safiya ta Allah sai ka kona kudinka a cikin kirjinka kana sanya ma
kanka cuta wadda a nan gaba ni ne zan zama mai jinyar ka a kan ta. In
takaice maku labari dai da haka wannan mata ta shawo kan mijinta ya
daina shan sigari, aka zauna lafiya.
*Darasi:*
▶ Abin da sauki da lumana ba su kawo ba fitina da tashin hankali
ba su kawo shi.
▶ Maganar gaskiya idan an fade ta yadda ta dace lalle ne za ta yi
tasiri, ta yi amfani.
▶ Yadda Macce take rainon ‘ya’yanta hakanan take yi idan tana da
basira ta yi tarbiyyar mijinta.
▶ Da yawa wanda yake aikata laifi amma ba ya jin girman laifinsa
sai an fadakar da shi.
▶ Sabo jarabawa ce. Duk ranar da Allah ya dauke ma bawa shi sai
ya yi masa mafita da zai bar shi.
📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.