✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*ABOKIN FIRA
*
*Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_
*DRS NA 023*
*Wani Hani ga Allah Baiwa*
Wasu fatake ne suka yi tafiya a cikin jirgin ruwa wanda yake
makare da hajarsu ta kasuwanci. A yayin da suke cikin tafiya suna raha
suna nishadi suna tattauna al’amurransu na ‘yan kasuwa, sai kawai
aka ji igiyar ruwa ta yunkura kamar za ta kifar da jirgin. Nan take suka
shiga taitayin su. Wani ya ba da shawarar a rage ma jirgin lodi domin
kayan da ya dauko sun yi masa nauyi sosai. Ba tare da tsayawa yin
shawara ba aka yanke hukuncin a zubar da kayan Alhaji Jatau saboda
su suka fi zama kusa da gabar teku, kuma daman babu cikakken shiri
tsakanin sa da manyan ‘yan kasuwa. Da Alhaji Jatau ya yi gardama sai
suka ga ba su da lokacin jayayya da shi a wannan yanayi da ake ciki.
Don haka, sai aka sa karti suka wurga shi tare da kayansa cikin teku,
suka ci gaba da tafiya abin su.
Alhaji Jatau ya ji kawai kunfan teku yana yawo da shi ba abin da
yake yi sai Hailala yana neman agajin Mai-sama. Can sai ya ji an jefa
shi a wani dan tsibiri takaitacce da babu mutum balai aljani a cikin sa.
Da ya farfado ya dawo hayyacinsa sai ya lura da wasu ‘yan ganyayyaki
wadanda ya rika cin su kamar yadda akuya take cin ciyawa. Idan ya
koshi sai ya sha ruwan da ke kwarara mai dadi daga tsakiyar wannan
tsibiri. A rana ta biyu ya saki jiki ya fara sabawa da wurin har ya ciro
wasu rassan itatuwa ya gina ma kansa ‘yar bukka wacce ya tsuguna a
cikin ta. A rana ta uku sai ya samu wata dabara ya dantse wata ‘yar
makwarara inda ‘yan kananan kifaye suke wucewa. Sai ya fara farautar
su yana gasawa yana yin kalaci.
Ranar da Alhaji Jatau ya cika kwana bakwai a cikin wannan tsibiri,
da daddare ya hura wuta kamar yadda ya saba don gasa kifayensa
sannan ya je wurin tarkonsa don kama wasu. Daga can sai ya hango
wuta ta kama ‘yar bukkar tasa. Da yake abin ba mai yawa ne ba koda
ya iso bukkar ta kone kurmus. Alhaji Jatau ya damu matuka da wannan
ci baya da ya samu. Amma ya yi haquri ya mayar da lamarinsa ga
Allah Gwanin Sarki.
A daidai lokacin da alfijir yake ketowa sai wani dan karamin jirgi
ya dunfaro tsibirin da Alhaji Jatau yake cikin sa. Da jirgin ya iso sai ya
ga wasu mutane baki da bai san su ba. Suka nemi ya shigo jirginsu
domin su tsallakar da shi. Ya tambaye su, ya aka yi suka san da zaman
sa a wurin? Sai suka ce, ai mun hangi wuta ne tana ci a wannan yankin
jiya da daddare, shi ya sa muka gane akwai mai neman taimako. Da ya
ba su labarin abin da ya faru da shi da ‘yan kasuwar da suka wurga shi
a cikin teku sai suka sanar da shi cewa, wannan jirgi tun a wannan
ranar da suka jefar da shi ya haxu da ‘yan fashi kuma duk sun kashe
wadanda ke cikin sa sun yi awon gaba da kayansu.
*Darussa:*
▶ Shirin Allah gare ka ya fi naka ga kanka.
▶ Kada ka cuci kowa. Idan an cuce ka ka nemi hakkinka wurin
Allah
- Wani hani ga Allah baiwa ne
📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.