YADDA ZAKA KUƁUTAR DA ZUCIYARKA DAGA HASSADA DA GIRMAN KAI

Yanda zaka kubutar da zuciyarka daga Hasada da girman kai*
.
يقول شيخُ الإسلام الشيخ إبراهيمُ انياس *نفعنا الله بأسراره و أنواره و علومه و فهومه*
.
Maulana Sheikh Ibrahim inyass na cewa:
.
طبيعتان شرٌّ
.
Dabi'a guda biyu Sharri ne ga maishi
.
• سوءُ الظن بالحقّ و الخَلْق
Mummunar fahimta ga Allah da halittu
.
• رؤيةُ الفضل لنفسك على الغير
Ganin fifikon kai akan wani
.
فإذا رأيتَ إنسانا إما أن يكون
Idan kaga mutum, dole ya zamo
.
أكبرَ منك أو أصغرَ أو أفقرَ أو أغنى أو أَعلمَ أو أجهلَ
.
Ko ya girme maka, ko ka girme masa ko ya fika talauci ko ya fika wadata ko ya fika ilimi ko ya fika jahilci
.
فإذا كان أكبرَ منك فَقُل
Idan ya girme maka, toh ga kallon da zaka rinka yi masa
.
هذا أفضلُ مني قد فعل كثيرا من الطاعات ما لم أفعلْ
Wannan ya fini, Sabida ya aikata daiwa daga cikin aikin Alkhairi dani ban aikata ba
.
و إذا رأيتَ أصغر منك فقل
Idan kaga wanda ka girma sai kace
.
هذا أفضل مني ما فعل كثيرا من الذنوب لصغر سِنِّه
Wannan ya fini, sabida bai aikata zunubai daiwa ba dan karancin Shekarunsa
.
و إذا رأيت أفقر منك فقل
Idan kaga Wanda ya fika talauci sai kace
.
هذا أفضل مني ما اكتسب كثيرا من الإثم في المعاملات لقِلّة ذاتِ يده .
Wannan ya fini, Sabida bai aikata zunubai daiwa ba dan karancin abunda ke hannunsa
.
و إذا رأيت أغنى منك فقل
Idan kaga wanda ya fika arziki sai kace
.
هذا أفضل مني قد أَنفَق كثيرا من ماله ما لم أقدر عليه .
Wannan ya fini, Sabida ya ciyar da daiwa daga cikin kudinsa, wanda ni banida ikon yin hakan
.
و إذا رأيت أعلمَ منك فقل
Idan kaga wanda ya fika ilimi sai kace
.
هذا أعلمُ مني و الأعلمُ يكون أتقى بدليل ( إنما يخشى اللهَ من عباده العلماءُ ) .
Wannan ya fini ilimi, kuma mafi ilimi shine mafi tsoron Allah sabida fadan Allah swt Lallai masu tsoron Allah daga cikin bayinsa sune Malamai
.
و هكذا يجب أن نتأَوَّلَ في جميع عباد الله
Shehu yace toh haka ya kamata mu rinka ta'awili a cikin dukkanin bayin Allah
.
*Tanbihi*
Hakan zai sa mu kubuta daga girman Kai da hasada da bakin ciki Kuma ba komai ake nufi da darika ba face cire irin wannan datti daga zuciya
.
Allah taimaka

Post a Comment (0)