HANYOYI DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI, KAIMA KA SAMI FARIN CIKI

Imam Abubakar Sanyinna: 

HANYOYI DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI, KAIMA KA SAMI FARIN CIKI.


 

1- Idan ka shiga gidan kace Assalamualaikum’ shaaidan zai bar gidan ka.. 

2- Ka rika yawan bata labarai, da zata kawo anashawa tsakanin ku..
Saboda Allah (S.w.t) ya sanar da mu
dan Adam yana son labari.

3- Ka zama mai yawan yabonta, musamman a wajen da ake kusheta,
ka nuna bacin ranka da rashin yardar ka. Duk kushe ta da’akayi idan da yardarka to babu shakka watarana zai dame ka.. 

4- Ka zama mai yawan bata kyaututtuka. Kyauta tana kara dankon soyayya, a wurin ta kuma zata kawo girmamawa, da ragowa tsakanin ku.

5- Ka share wasu daga cikin kuskurenta.
Ka nuna baka ma san ta yi ba. Kuma ka dauka a matsayin abinda ya
shude, karka ajiye shi a kwakwalwarka.

6- Ka nuna mata tausayawarka gareta
a fili, da zuciya musamman a lokacin da batada lafiya,ko takeda
da juna biyu ko take jinin al’ada,Kai koma lafiyar ta kalau.

7- Kada ka daukaka abokanka ko yen uwanka fiye da matarka. (lokuta da dama wasu mazan
suna fifita abokansu ko yen uwanka sama da matansu) wannan kuskure ne mai haifar da husuma tsakanin ma’aurata. Wurin aboki ko dan uwanka daban wurin matarka daban.. mata na gaba da aboki ko Dan uwanka. ayi gyara da wuri wuri

8- Ka nuna mata babu wata wadda ta fita dake gabanka sai ita, Ka nuna mata
kullum a matsayin sabuwa take a gurinka. Ba zai rage ka da komi sai daukaka da girmamamawa da kimar ka da zata karu a idon ta.

9- Ka rika tunawa da ita a cikin addu’arka. Hakan zai kara kauna tsakaninku. Allah na alfahari da mai yima dan uwan sa musulmi addua.. kuma gobe kiyoma yayi masa tanadi.. kyakkyawa!

10- Kada ka nuna mata ce wa kana yi mata alfarma akan wata kyautatawa da
kake mata, kamar siyan abinci, Saboda daman hakkinta ne ka kawo mata,sannan kasan ce wa abincin kawai kake kawowa amma Allah shi ne mai ciyarwa. Zai iya kasancewar alfarma abincin daga Allah a dalilin kyatatawar ka ne a gareta.. 

11- Shaidan ne abokin gabarka ba matarka ba, Lokuta da dama idan mata da miji suka dan samu sabani har takai ana maida martani cikin fushi,To katuna ba daga ita bane shaaidan ne ke zugata, Saboda shi yana mutukar son ayi saki.

12- Ka dauki abinci ka saka mata abaki, ko ka ci abinci tare da ita.. 
Annabi (s.a.w) ya ce, “abincin ba cikinta kadai zai shiga ba, zai huce har zuwa zuciyarta.”

13- Ka kasance mai yawan yi mata murmushi/fara’a sadaka ce. Kayi ma wasu balle matarka..
 Manzo (s.a.w) ya ce: “Duk wanda ya nunawa matarsa
fara’arsa to dai-dai yake da yin sadaka.”

14- Ka zama mai yawan neman shawararta. (wasu suna ce wa ba,a shawara da mata). To wallahi ku sani ce wa manzo (s.a.w) ya kasance yana shawara da matar sa.

15- Kar ka boye mata damuwar ka,
farin cikinka ko bakin cikinka.
Domin ita magani ce a tattare da kai,da Allah yayi maka. 

Maza ayi kokari a daure a raya baiwar da Allah ya saukake maku.wallahi wannan hakkin matar ka ne akanka Allah ya azama ba waniba idan kayi Allah kayima biyayya kuma kanka kayima

Kuma Allah ya kare mu da shairin shaidan da abokanen sa. Amin
Post a Comment (0)