KA JURE! KI JURE KA YADDA DA QADDARA !!

KA JURE! KI JURE KA YADDA DA QADDARA !! to kowana fanni ! Harkan so ! Kudi ! Cikin sha'anin iyalai...Dogon jinya da makaman ta su !
:
Annabi Sallallahu alaihi wa sallam yace "babu wani musulmi da cutarwa ze sameshi na rashin lafiya, kowaninsa, face ALLAH ya kankaremasa zunubansa kaman yadda bishiya take kade ganyenta" bukhari 5648 muslim 6571. 
    Idan zamu riqa la'aqari da wadannan hadisan, dan meye zamu damu da cuta inta same mu ??
    Alhali muna aikata zunubai kala kala, acikin sallah da wasu ayyukan alheri, anasamun matsala agaremu, hakan yasa arubuta mana zunubai !
# Wani in damuwa ta dameshi, sekaji yana fatan mutuwa ! Laa subahanallah bakaji fadin Manzon ALLAH(ﷺ) ba dan gane da hakaba ??
.
Yace (kada dayanku yayi burin mutuwa saboda wata cuta data sauqa akansa, idan yazama dole seka roqi mutuwa, to yace "ALLAH ka rayani matuqar rayuwana shine alheri, ka kasheni matuqar mutuwa shiyafimin alheri" bukhari 6351 Muslim 2670.
.
Bakasan me zaka samuba idan ka mutu, gwanda kabi shawaran baban al-qasim (ﷺ), rayuwa cikin jarrabawa ni'imane daga cikin ni'imomin ALLAH, kuma kowa bayasan mutuwa yanason rayuwa me dadi !
   Antambayi Manzon ALLAH (ﷺ) wani mutum ne yafi alheri, yace (Wanda aka tsawaita rayuwansa, kuma ayyukansa sukayi kyu) yace wasu mutane ne sukafi sharri Yace (Wanda ama tsawaita rayuwansa, ayyukansa suka mu nana) sahihil jami'e 3297.
.
Shawara dan uwa/ 'Yar uwa idan cuta ko damuwa ya sameka/ki. "Daure da istigfari" koda ba abinda yasameka kazama me yawan istigfari "
 Domin Annabi (ﷺ) yace:- WALLAHI NI INA ISTIGFARI, INA KUMA TUBA ZUWAGA ALLAH, AKOWACCE RANA SAMADA SAU 70) Bukhari 3607 daga Abu huraira.
.
# sheek Albany yace "MEYA WAJABA GA MARAR LAFIYA" ya yadda da qaddaran ALLAH, yayi hakuri kuma akan qaddara, kuma ya kyautata zato wa ubangiji, (mamallakin Sarki me rahama) wannan shiyafi alheri agareshi! Seya kawo hadisin (Abin mamaki ga lamarin mumini, komansa alheri..) ya kawo maganan manzon ALLAH (ﷺ) kada dayanku ya mutu, face yana kyautata zato wa ALLAH madaukakin sarki) 
:
Kuma ya tsaya tsakanin kwadayi(rahama) da tsoro (azaba)...
# ..
 Don neman Qarin bayani duba (KITABUL JANA'IZ) na Nabil bin muhammad Mahmod (shafi 9-11)
=
23-Ramadan 1439
Abu ja'afar

1 Comments

Post a Comment