KISHIYA ƳAR UWA CE

👩‍❤‍💋‍👩 *KISHIYA ƳAR'UWA CE!*👩‍❤‍💋‍👩

👩‍❤‍💋‍👩Kishiya ƴar'uwa ce kuma alkhairi ce idan ka yi sa'ar ta gari. Ƙarin auren maza wani abu ne da babu macen da zata iya kauce masa ko ture sa in Allah Ya ƙaddarasa. Komin kuwa biyayyarta, soyayyarta da yawan tattalinta.

👩‍❤‍💋‍👩Ƙarin aurensa ba yana nuna ya dai na son uwar ƴaƴansa, ko kuwa wacce zai ɗauko ta fita bane. A'a tana nan a matsayin masoyiyarsa abar ƙaunar sa. Amma fa in itama ba ta canza akan halayenta na gari ba.

👩‍❤‍💋‍👩Haka ne! Kuma babu karya! Kishiya aba ce mai zafi. Abun da nauyi a ce zaka fara raba masoyinka da wata. To amma waɗannan jarabawowin mu ne mata, kuma ko wane jarabawa akwai alkhairin da ka iya zuwa da shi.

👩‍❤‍💋‍👩Kishiya ta gari tana iya taimakawa mace wajen ganin sun tafiyar da gidan mijinsu yanda ya dace. Kuma tana zuwa ne cikin gidanki da wasu kariya da zata baki, ƴaƴanki da kuma mijinki.

👩‍❤‍💋‍👩1. In baki da lafiya zata taya ki kula da ƴaƴanki. Haka nan kuma mijinki yana da in zai sauke sha'awarsa. 

👩‍❤‍💋‍👩2. In zaki yi wata tafiya da ba zai yiwu ki ɗauki yara ba, kishiyarki ta gari ita zata miki ɗawainiya dasu har ki dawo. 

👩‍❤‍💋‍👩3. In kina jinin al'ada mai daɗewa ko in kin haihu mijinki yana da wani ginin da zai karesa daga faɗawa neman matan banza.

👩‍❤‍💋‍👩4. Kishiyar arziƙi tana iya canza mijinki, ku hada kai ku yaki wasu halaye nasa tare. Kuma wata ma tana iya kawo miki zaman lafiya in kina samun matsala da dangin miji. 

👩‍❤‍💋‍👩5. Uwa uba zaki iya barin duniya ma gaba ɗaya, sai wannan abokiyar zaman taki ta gari ta cigaba da ɗawainiya da ƴaƴanki da nata har su girma. Ko kuwa kina da tabbacin lokacin da aka ɗiba miki zai kai har ki gama tarbiyyan ƴaƴanki da kula dasu su girma?

👩‍❤‍💋‍👩Tsoro yana kama mata akan kishiya ne saboda na gari sun yi karanci, kuma kusan kowa ta shigo gidanki yanzu kokari take yi miji ya dawo hannunta. Ke ki zama abar wulaqantawa kuma ba kowa ba, to da an yi rashin sa'an namiji mara adalci shi kenan sai dayan ta shiga kuncin rayuwa.

👩‍❤‍💋‍👩Mata mu yi haƙuri, mu jure, mu cije mu ci waɗannan jarabawowin. Kuma mu tuna ibada mu ke yi, kuma ko wane ibada yana da sakamako.

👩‍❤‍💋‍👩Har na ji zazzabi a jikina, wallahi kishiya ba daɗi. Ita ce gaskiyar da nake faɗi mai mun nauyi da wahala. Amma gaskiya in ta kama a ko ina ka faɗe ta koda kuwa a kanka ne, kuma koda baka sonta a karan kanka. Sannan ka cire son zuciya ka yi adalci ma ɗaya bangaren.

👩‍❤‍💋‍👩Yaa Allah Kai mana tukuici da Aljannah Firdausi sanadiyyar haƙurin da zamu yi da kishiyar duniya. Oh mu! 😭

🖎 *Sadeeya Lawal Abubakar.* 😕

📚 *MARKAZUS SUNNAH*


Post a Comment (0)