MARABA LALE DA ZUWAN LOKACIN SANYI {HUNTURU}

MARABA LALE DA ZUWAN LOKACIN SANYI {HUNTURU}


Hakika magabata na 'kwarai *{السلف الصالح}* sun kasance idan lokacin sanyi {Hunturu} ya shigo su na murna da farin ciki da shigowarsa. Saboda yini yana gajarta, dare kuma yana tsawaita, kuma hakan ke basu damar samun lokaci mai yalwa domin yin Qiyãmul-laili da kuma azumtarsa.

Hadithi ya tabbata daga Manzon Allah {S.A.W} ya ce: "Azumi cikin Sanyi, ganima ce sassanya". {Ahmad }

Sayyidina Abdullahi bn Mas'ud (R) ya ce: " Maraba lale da lokacin hunturu albarka na sauka a cikinsa sai ya kasance darensa ya tsawaita aita Qiyamul-laili sannnan yininsa yanayin qaranci sai ya zama azumi yai dadi".

Al'imam Alhasanu Albasariyyu {R} ya ce: "Madallah da zamanin masu Imani lokacin hunturu {Sanyi} darensa yai tsawo ta yanda mutum zai tashi yayi 'kiyamullaili".

Haka ma an ruwaito daga d'aya daga cikin magabata yana cewa: "Da badin d'aya daga cikin abu uku ba da na gommace na zama 'kudan zuma abubuwan sune : nai ta yin azumi lokacin sanyi, na biyu nai ta yin Qiyamul-laili, sannan nai ta yin karatun Alqur'ani da daddare ina jin dadi wadannan abubuwa da badan su ba dana gwammace Allah ya mayar dani 'kudan zuma bazan damu ba". 

Haka magabata ke daukan lokacin hunturu ta hanyar cin gajiyarsa kuma suna ji a ransu lokaci ne da zasu zage dantse wajen 'kara kusanci da Allah. Shiyasa a shari'armu ta musulunci ta kwadaitar damu idan irin wannan lokacin yazo akwai ibadu da ake so ya zama mun rikesu 'kam'kam daga cikinsu:

1) Azumi
2) Kula da lafiya
3) Kyautata alwala
4) Tsayuwar dare {Qiyãmul-lail}
5) Nisantar duk wani abinda zai iya jawo gobara.

Allah Ta'ala ka bamu ikon bin tafarki da aiki da Sunnar Annabi {S.A.W}, kuma wannan yana yi da muke ciki na sanyi Allah ka sa mu ga wuce warsa lafiya.

*_'Dan uwanku a Musulunci: ✍_*
*_Abu Ja'afar_*
*_Yusuf Lawal Yusuf_*
3th Rabi'ul Auwal, 1440Ah
{11/11/2018}.
Post a Comment (0)