TUNATARWA DA JAN HANKALI GAMEDA SHIGOWAR LOKACIN SANYI!

TUNATARWA DA JAN HANKALI GAMEDA SHIGOWAR LOKACIN SANYI!



     ASSALAMU ALAIKUM.
      Lokacin *SANYI* ya shigo. Lokaci ne wanda YINI yakeda Qaramci, shi kuma DARE yake da tsawo.
    Irin wannan lokaci ne magabata na Kwarai suke kira *Kakar Ibadah.* Kuma magabata sun kasance sukan taya junansu MURNA idan wannan yanayi ya shigo har suna gayama junansu cewa👇🏽
     *مرحبا بالشتاء, يقصر فيه النهار للصيام, ويطول فيه الليل للقيام*
   *Fassara* 👇🏽
  "Maraba da (yanayin) SANYI. *Yini* yana taqaituwa domin Masu AZUMI, kuma *DARE* yana yin Tsawo domin masu QIYAMULLAILI."
    A wannan yanayu masu azumi zasuji sauqin azumi domin awannin yinin basuda tsawo, cikin kankanen lokaci zakaga rana ta fadi. Sa'annan Awannin dare sunada tsayi, masu *Qiyamullaili* zasu samu isasshen lokaci suyi sallar dare har su sake komawa bacci cikin natsuwa kuma su tashi su samu sallar asubah.
    Ina kira ga kaina da kuma dukkanin 'yan uwana Musulmi, da muyi kokari mu ribanci wannan garabasa da Allah ya kawo mana, ta hanyar yawaita ayukkan ibada musamman Azumin nafila da kuma Sallar dare. 
    Ina rokon Allah Ya bamu ikon ribantar wannan lokaci mai tsada kuma Ya bamu *ikhlasi* ga dukkanin ayukkanmu na ibadah. 
    Ina rokon duk wanda wannan tunatarwa takai gareshi da ya turama sauran jama'ah gwargwadon iko, domin gangamewar fa'ida. Ina kuma neman addu'ah daga gareku. Allah ya shiryar damu zuwaga hanya madaidaiciya. Allah ya jiqan iyayen mu. 
     *Daga dan uwanku a Musulunci👇🏽👇🏽👇🏽*
   
   *Hamdany Abdullahi(Sokoto)*
    *Islamic Online Islamiyya of Nigeria(IOIN)*
  *08065203174*
  *08134300040*
Post a Comment (0)