MECECE MUTUWA?

MECECE_MUTUWA?



Hakika Fitan rai yana da wani irin radadi
wanda babu mai saninsa sai dai Mamaci..
Mamaci yayin da ransa ya kusan fita,
Muryarsa takan karye, Qarfin jikinsa yakan
tafi.. Babu damar Eehu ko kururuwar zafin
da yake ji. Domin zafin mutuwa ya riga ya
ratsa dukkan sassan jikinsa..
Ba zai samu damar neman taimako ba,
ballantana adauke masa zafin radadin da
yake ji. Sai yayi fatan wannan nishin da
yakeyi ko zai zama dalilun samun
rangwame, amma inaa!!.
Idan har akwai ragowar wani Qarfi gareshi
shine za'a rika jin wani irin gurnani yana
fitowa daga chan cikin Qirjinsa da
Makogoronsa yayin da rai yazo fita.. Alhali
launin fuskarsa ya chanza saboda tsananin
halin da yake ciki.
Yayin da ranka yazo Makogoro, awannan
lokacin zaka manta da Makusantanka,
iyalanka ko 'Ya'yanka, balle Makobta.
Awannan lokacin ne 'Dan Adam yakan ji
wata irin Qishirwa mai tsanani wacce sai ya
gwammaci inama ya bayar da dukkan
abinda ya mallaka domin a bashi ruwan da
zai kurba koda kurbi guda ne!!.
A wannan lokacin duniya da dukkan abin
cikinta zasu zamanto ba komai ba...
Ballantana dukiya ko Mulki ko wani gata...
'Dan Adam zai gane cewa ashe shi ba komai
bane.. Kuma tun daga sannan zai fara
nadamar lokutan rayuwarsa da suka tafi
wajen sa'bon Allah!!
Tunda Shugaban Halitta (sallal Lahu alaihi wa
aalihi wa sallam) ya 'dan'dana zafin mutuwa,
Ka sani cewa kaima sai ka 'dan'dana!!
Imamul Bukhariy ya ruwaito daga Nana
A'isha (rta) tana bayar da labarin jinyar da
Manzon Allah (saww) yayi adakinta, har
zuwa rasuwarsa. Tace :
"Hakika Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa
aalihi wa sallam) ya kasance a gabansa
akwai wata guga wacce akwai ruwa
acikinta, yana shigar da hannayensa acikin
ruwan sannan ya shafe fuskarsa dasu. Yana
cewa :
"LA ILAHA ILLAL LAAH!! HAKIKA MUTUWA
TANA DA RADADI!".
Sannan ya chira hannunsa sama yana cewa :
"ACIKIN TAWAGA MADAUKAKIYA!''. (Alokacin
an bashi za'bi ne tsakanin ci gaba da zaman
duniya, ko kuma komawa zuwa ga
Ubangijinsa).
Yana fa'dar haka har sai da aka karbi ransa
sannan hannunsa ya karkato...
Annabi Muhammadu kenan (saww)
Shugaban halittun Allah baki daya, wanda
bai ta'ba sa'ba ma Allah ba. ballantana kai
wanda kullum acikin sa'bon kake kwana
kake tashi.
Lokacin da Amru bn Al-As (ra) yazo rasuwa,
an tambayeshi shin yaya yake ji?. Sai yace "Ji
nakeyi tamkar sammai sun fa'do akaina,
Qassai kuma sun matseni".
Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (ra) ya
tambayi Ka'abul Ahbari ya siffanta masa
yadda mutuwa take. Sai yace : "Ya Kai Sarkin
Muminai! Hakika ita mutuwa kamar wani
reshe mai yawan Qayoyi ajikinsa, ashigar
dashi cikin cikin mutum. Bayan kowacce
Qaya ta rike wata jijiya daga jijiyoyin jikinsa,
sai kuma a samo wani mutum Ma'abocin
Qarfi, ya kama wannan reshen ya fizgoshi
da Qarfi, ya fizgoshi kenan tare da tsoka da
jijiyoyin jikin!!!.
Yanzu 'Yan uwa koda tunanin wannan ranar
bai ishemu dalilin rage sa'bon Allah ba!!.
Wannan ranar fa sai ta riskeni, sai ta riskeka,
sai ta riskeki, sai ta riskemu baki dayanmu
kamar dai yadda ta riski wadanda suka rayu
kafinmu.
Daga cikin abubuwan dake haddasa
tsananin zafin fitan rai tare da gigicewa
akwai :
- Wulakantar da Sallah.
- Wulakanta Mahaifa.
- Chutar da Manzon Allah (saww) ko iyalan
gidansa da zuriyarsa ko kuma Sahabbansa
(Radhiyallahu anhum).
- Cin Mutuncin Malamai Waliyyai da salihan
bayin Allah.
- Shan giya ko Miyagun Kwayoyi.
- Cin haram (Cin hanci, wawure kudin
gwamnati ko Kudin Marayu, ko Satar dukiyar
jama'a, etc).
- Kisan rai ba tare da hakki ba.
- Zina, Luwadi, Madigo.
Ya Allah ka kiyayemu daga Mummunar
mutuwa. Ameen.
Post a Comment (0)