:
Daga zauren
Kulafa'ur rashidun
:
Malam tambaya wai yasunan Abu halifa na gaskiyya da kuma takaitaccen labarinsa
:
******
:
To Imam Abu Hanifa asalin sunan sa shi ne *An-Nu’uman bin Thabit, At-Taimi, Al-Kufi,* an haife shi a shekara ta (80 bayan hijra) a birnin kufa na kasar Iraqi ya hadu da wasu daga cikin sahabbai kamar Anas bin Malik, amma ana cewa ba shi da riwaya ko daya daga sahabi.
.
Imam Abu Hanifa daya ne daga cikin manyan Malaman Muslinci, wanda sukaiwa addini ALLAH hidima, kuma al'muma ta amfana da tarin ilimin sa Allah ya ba shi tarin ilimi da yawan ibada, ana cewa yana saukar kur’ani duk dare.
.
Abu Hanifa yana cewa: wata rana na yi mafarki wanda ya razana ni, na yi mafarki kamar gani ina tono kabarin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) sai na tafi Basra na sa wani mutum ya tambayar min Ibn Sirin ma’anar wannan mafarki, sai Ibn Sirin ya ce: wannan mutumin zai dinga tono hadisan Annabi (Sallallahu alaihi wasallam).
.
Yahya bin Ma’in yana cewa: Imam Abu Hanifa thiqa ne, ba ya rawaito hadisi sai wanda ya haddace, ba ya rawaito hadisin da be haddace ba. A taqaice wannan shine imamu Abu Hanifa.
.
Yabar duniya a shekarata (150 bayan hijra) yau kimanin shekara (1,289) muna Addu'a ALLAH yayi masa rahama.
.
*الله تعالى اعلم،*
_Almajirinku ne kamar kullun_
.
```SANI ILYAS YAKASAI ```
_(Dan mama-Assalafy)_
.
Nake muku fatan Alkairi
========================
*```Date* ```[5-09-1439]Hj {22-05-2018}
Kuna iya samun mu ta Internet/website http://khulafau.cf
_Masu buqatan Group suyima daya daga cikin Number's innan maga ta whatsApp_
+2349033206238
+2347035269582
+2348063796175
*```Kuna iya samun mu ta facebook*```
facebook.com/khulafaurrashidun
((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ))
〰〰〰〰〰〰〰〰✔
*Wanda yaga gyara, yasanar damu !*