TUN KAFIN AURE 05

TUN KAFIN AURE💐5


A mota Hafsi  ta sami Saif yana jiranta. Tana shiga wani kamshi mai dadi ya bakunci hancinta tare da sanyin AC. A kunyace ta zauna tare da gaishe shi. Matar kinyi kyau sosai ga kamshi mai dadi da kike yi. Fari tayi masa da ido har na kai ka kamshi Saif? Har kin fini ya bata amsa yana dariya.

Yana tuki suna hira bata ankara ba taji ya kama mata  hannu ya dora akan gear ya hada ya rike. Tana kokarin kwacewa ya matar kina son muyi accident ne kike neman canza min gear? Cikin muryar shagwabar da ta saba magana tace da hannuna fa ka hada Saif. Au hannunki ne ma ba nawa ba. Naka ne mana amma ba'a gama baka ba sai an daura aure. Ku mata komai sai an daura aure ne? Ko kin manta ansa mana rana. Ai yanzu abinda ya rage tsakaninmu kadan ne.
Suna shiga unguwar ta fada masa su bi ta bayan layinsu Ummati sai ta sauka. Ba musu layin suka shiga da yake a tsuke yake ba mutane sosai. A nan Saif ya sami damar kebewa da Hafsi don a gidansu akwai idon jama'a. Rikota yayi ya hanata fita....matar ni fa duk kin rikita min lissafi tun ranar saturday da muka yi hoto. To yanzu me kake so ayi. Wayarsa ya dauko yana nuna mata pictures din. Hafsi ta sami tarbiya daidai gwargwado kuma shima Saif din ya fito ne daga gidan mutumci sai dai koyi da tarbiyar nasara yasa idanunsu ke neman rufewa. Ganin hotunan yasa suka fara shiga wani yanayi. Yadda ya riketa kamar ba zai saketa ba yana kokarin hada bakinsa da nata itama kuma bata yi yunkurin hana shi ba.

Tun shigowarsu layin Mal  Aminu ya gane motar sai dai bai gane yarinyar da ke gaba ba saboda yadda take ta kokarin rufe fuskarta. Ganin motar ta shige wata kwanar ba hanyar gidansa ba yasa yayi mamaki kamar ya wuce sai yaga anyi parking dinta a karkashin bishiyar darbejiya shiru ba'a bude kofa ba. Karasawa yayi ya tambayeshi gidan wa yake nema tunda dai a iya saninsa gidansa yake zuwa a unguwar.

Jin ya fara kissing dinta jikinta yayi sanyi hankalinta gaba daya ya tashi. Ashe akwai ranar da zata aikata irin abinda take ji a labari tana ganin bakin masu aikatawa. Wai a zamanin yanzu a haka ne kawai masoya zasu nunawa junansu kauna. Wazu hawaye taji sun zubo mata. Hankalin Saif ya tashi...matar kiyi hakuri wallahi rudin shaidan ne amma bani da mugun nufi a kanki. Yana cikin share mata hawaye suka ji an bude kofar gefen da take zaune.....idanu ta bude a tsorace ganin waye a tsaye cikin rawar murya tace BAFFA!.
*******************

Yau ma a cikin maye ya shigo gidan anyi sa'a ma wurin shabiyu da rabi na dare ya shigo. Fito ya shigo yana yi yana karkada keys din hannunsa. Kamar daga sama yaji kira...Junaidu....ba don namiji bane da gabansa sai ya fado kasa yadda ya mugun tsorata. Cak ya tsaya kamar gunki. Don ubanka juyu ka kalleni. Mommy da ke zaune a gefe shiru tayi. Babu wanda baya tsoron Hajiya Ramatu. A kano take aure a gyadigyadi wurin da aka fi sani da dangi, shiyasa ma ake kiranta da Hajiyan Dangi.

Tsawa ta daka masa bazaka zo ba ne. A hankali ya dawo ya zauna a kan kafet. Hajiyan Dangi doguwar macece kamar mahaifisu ga jiki. Ita kadai ce mace a gidansu kuma ita ce babba. Allah bai bata haihuwa ba sai dai ta rike yara da yawa daga danginta har na mijinta. Cikinsu harda Senator Rufai kaninta. Mace ce mai riko da addini kuma mai sa ido akan tarbiya. Yanzu Junaidu wannan wannan rayuwar ka daukarwa kanka? Tana magana ta soma hawaye gidan malamai manyan mutane muka fito amma saboda giyar kudi na dibanka kana neman lalata rayuwarka. Ta kalli Mommy yanzu sai da lamarin ya baci haka kika sanar dani. Mommy dai hakuri ta ba ta. Bandanan kansa Hajiyan dangi ta fizge. Gobe kaje ka aske wannan shegen kan kuma kazo ka nuna min. Ko ci kanka bai ce mata ba haka ya tashi ya basu wuri. Yana shiga daki tabarsa ya kunna ya fara busa hayaki kai ka ce bakinsa salansar mota ne. A haka Junaid ya tuna bai yi sallar laasar, magriba da isha ba. Tsaki ya ja tare da mikewa ya nufi toilet. Haka ya yi alwala irin yadda kwakwalwarsa ta karanta masa sannan yazo ya fara ramuwar sallolin da bai ma san abinda yake karantawa ba.

A dakin da take sauka kuwa Hajiyan Dangi ce ta yanke shawarar ba zata koma kano ba sai kaninta Rufai ya dawo daga Australia sunyi magana akan Junaid. Babu abinda taki jini kamar yaro yaki ya rinka keta dokokin Allah ba tare da an dauki mataki akansa ba.




Batul Mamman💖


Post a Comment (0)