MINENE HASSADA, KUMA YA AKE HASSADA, KUMA SU WANENE MASU YIN HASSADA?

MINENE HASSADA, KUMA YA AKE HASSADA, KUMA SU WANENE MASU YIN HASSADA? 


1- Hassada wani mugun ciwo ne da ke Nukurkusar mai yinta a cikin zuciyarsa shi kadai. 

Hassada shine Jin Zafi, Daci, ko Bacin Rai a yayin da kaga wani Dan'uwanka, Makwabci, Aboki ko ma wani kawai da ka sani a duniya ya samu daukaka, ko wani iri.

Hassada kala uku ce (3)

A- Akwai jin kyashi, shine mutum yaji a zuciyarsa don me wani zai fishi wani abu a rayuwa. Kudi, Mulki ko kuma Baiwa ko Mukami. 

B- Mutum yaji shi bayason kowa ya samu wani abun alkhairi ko karuwa sai shi kadai.

C- Wannan shine yafi kowanne muni, wato mutum yaji cewa idan dai shi bazai samu abu ba to gara kar kowa ya samu. Irinsu sune suke yin a fasa kowa ya rasa

2- Mutane da yawa suna fadawa cikin aikata Hassada ba tare da sun ankara ba misali:

A- Yawan yin magana akan ci gaban wani ko wata e.g 1- oh su wane an haye, sai kace da ba teburin mu daya ba a wajen aiki, lokacin nan kuwa kayansa basu wuce kala biyar ba.

2- Mutum ya rinka gamin wane an samu shiga, ji wai yanzu shine kaza, sai kace ba tare aka daukemu aiki ba.

3- Dubi daga malami ya shigo aji sai ya fara wani iyayi wai shi a dole ga mai kwakwalwa

*YA ZA'AYI MUTUM YA GANE CIWON HASSADA YA FARA SHIGARSA*

Yanda mutum zai gane idan ya fara koyon Hassada shine:

A- Yawan damuwa da al'amarin wani ko wata, wanda kwata kwata bai shafeka ba ta ko wani hanya.
 
B- Damuwa da son sanin halin da wata ko wani yake ciki, idan kaji mummunar labari game da wani kaji dadi a ranka ko ma kayi dariya ko shewa, idan kuma kaji labari mai dadi game da mutum sai kaji ranka ya baci, ka kasa yi masa fatan alkhairi, ka fara jin tsoron kar ya wuceka a level na rayuwa. Sai ka fara kokarin kai sukarsa a wajen abokan arzikinsa, ko kokarin fadin miyagun maganganu game dashi, ko kuma fadin kalamai na batanci game dashi. Musamman ma idan ba'a tambayeka labarinsa ba, shine Hassada

4- lllolin Hassada suna da yawa amma ga kadan daga ciki:-

1- Hassada tana cinye kyawawan ayyukan mai yinta kamar yanda wuta take cinye karmami(Kirare/kara).

2- Hassada tana haifar da ciwon Zuciya da kuma Muni ga mai yinta.

3- Hassada tana hana mai yinta samun cigaba a cikin rayuwarsa da kuma duk abunda yasa gaba ba zaiga nasara bayyanan ne akai ba.

4- Hassada tana rage lmani kuma tana taimakawa wajen aikata Shirka da fita ma daga addini ba tare da mai yin Hassadar ma ya ankara ba.

5- Hassada shine kofa na aikata mafi yawancin manya manyan kaba'irai, kamar:

A- Gulma 
B- Munafunci
C- Makirci 
D- Rashin yadda da Kaddara 
E- Rashin hakuri 
F- Karya 
G- Yaudara e.t.c

*YA ZA'AYI KA KARE KANKA DAGA CUTAR HASSADA*

Yanda zaka kare kai daga Hassada shine yafi komai sauki, saboda ai yin Hassadar tafi wuya, takurawa kanmu mukeyi sai munyi Hassadar duk da mun san illarta da kuma nauyin Zunubinta.
 
1- Mutum yayi kokarin cire kansa akan duk wani al'amurran da basu shafeshi ba.

2- Mutum yayi kokari yayi focusing akan inganta rayuwarsa.

3- Kiyayewa daga kananan Gulmace-Gulmace. 

4- Son iyawa ko son bada shawara a inda ba'a nemi taimakonka ba.

5- Addua da yima zuciyarka addu'ar tsarkakuwa daga dukkanin miyagun ayyukan da ka iya gurbata ta.

Mutane da dama sukan tsinci kansu a cikin wani yanayi mai ban al'ajabi, za kaga mutum yana yawaita Azumi, Nafilfili, tsayuwar dare, Sallolin Farilla sam basa wuceshi amma sam baya cigaba a rayuwarsa, kodai yaci baya ko kuma kullum yana nan a inda yake, babban dalilin haka shine *"Zuciyarsa Baka ce"* sam babu alkhairi a mu'amalarsa da mutane, kullum ya bude bakinsa sai dai ya fadi Sharri ko ya kulla Makirci, ko kuma zargi akan abinda ba damuwarsa bace.

Sau da yawa za kaga mutumin Banza, Mashayi ko Mazinaci amma duk abunda yasa a gabansa zai samu, wani ma sam ko Sallah ba kullum yakeyi ba, amma da ya fara neman abu sai kaga ya samu, ba komai Allah ya keso ya nuna mana anan ba, illa, mu fahimci cewa shi Allah da Zuciyoyinmu yake aiki

Saboda haka da zarar mutum yayi Addu'a yayi Addu'a yaga ba'a amsa masa ba, to ya fara bincikar Zuciyarsa, Sannan kuma sai ya binciki Ayyukansa lallai akwai inda yake da matsala.
Allah ya shiryar da mu.
Post a Comment (0)