Tarihin Tsoffin Biranen Hausa: Baɗari da Goɗiya.
Daga Sadiq Tukur Gwazo
08060869978
A mafi ingancin zance, maguzawa ne suka fara kafa garuruwa a kasar hausa. Muna iya cewa ma sune asalin hausawa. Amma dai, bari kuji abinda muka samu daga tarihin waɗannan tsoffin garuruwa guda biyu.
Garin Baɗari.
Wannan gari yana da tsohon tarihi. Ya kamata kuma a sanyashi a sahun tsoffin biranen hausawa.
Tarihi ya nuna cewa, wani bamaguje mai suna Bugau shine wanda ya kafa wannan tsohon gari shekaru da dama da suka gabata. Ance garin ya riganyi Garuruwan Goɗiya dana Kano da kafuwa. Tsiransu da kano shekaru takwas ne, domin kuwa shi Bagauda daya kafa kano ance ai kanine ga Bugau.
Zuwa yanzu dai babu takamaimen tarihin daga inda Bugau da kaninsa Bagauda suka taho, babu labarin kabilar su kuma ko na iyayensu, amma dai labari ya nuna cewa su biyun duk 'yanuwan juna ne, kuma da hausa suke magana, tana iya yiwuwa ma Bagauda ya zauna a Baɗari kafin daga bisani ya tashi ya riski kano kuma har ya sareta ta zama gari.
Garin Baɗari daɗaɗɗe ne wanda za'a iya cewa ya kai kimanin shekaru dubu ɗaya da hamsin da kafuwa. Garin ya shahara a zamanin-da wajen sana'ar rini da bugu ta yadda har yanzu shashin shahararriyar karofin garin yananan. Sannan kuma alkarya ce a baya inda baki ke zuwa daga sassa mabanbanta.
Kasancewar mutanen garin sun bar tsohon garin izuwa sabo shekaru kimanin sittin da ɗaya da suka gabata, amma har zuwa yau akwai shacin ganuwa bai dusashe ba wanda ke nuna cewar garin yasha gwagwarmayar yaki acan baya. Sannan akwai shashin babbar fadar masarautar wadda akayi da ginin marmara, sai kuma shacin wata tsohuwar rijiya mai suna Fafagu shima yana nan har yau bai dusashe ba.
Bama iya nan ba, har yanzu ana iya shaida kushewar wani Mutum mai suna Garega a tsohon garin. Shidai Garega ance Bamaguje ne, daga kano yayi laifi aka koro shi. Dan haka dayayi yamma da kano da tafiya mai nisa sai ya riski Baɗari, sai kuwa ya zauna a garin har ajali ya sameshi. Bayan an binneshi a kushewa ne sai bishiyar Lalle tafito a saman kabarin nasa, wannan yasa wajen ya zama abin nuni gakowa. Kuma Koda yake zuwa yanzu an sare wancan lalle, amman dai an samu cewa kafin a sare shi idan mata sunyi kunshi da lallen baya kamawa.
Ance Fulani sunzo garin ne lokacin Jihadin Shehu Usmanu ɗan Fodio. Ga kuma yadda abin ya faru kamar yadda muka ji.
Akace akwai wani fulanin mutum Basulluɓe dake zaune a Adamawa mai suna Muhammadu Kigudu (ana kiransa Kigu) da sukayi rigimar sarauta a garinsu, sai bai samu wannan sarautar ba. Wannan tasa yayi fushi tare da tasowa dashi da wansa mai suna Gabbu, da dabbobinsu da kuma bayinsu izuwa sokoto wajen shehu Usmanu. Sun zauna da shehu babu jimawa sai aka basu shugabanci, inda shi Muhammadu Kigudu yazo ya zauna a garin Guɗe a matsayin shugaba, shikuma Gabbu ya zauna a garin Gwarzo a matsayin shugaba.
Daga bisani sai Kigudu ya dawo Baɗari da mulki. Ana kiran sarautar 'ɗan Badari'.
Bayan rasuwar sa kuma sai ɗansa Yusuf yayi sarauta. Shima bayan yarasu sai kuma aka danka sarauta a hannun wani mutum bafulatani jinsin Ruma dake kasar Katsina. Jikan wannan mutumi mai suna Abdullahi shine wanda ya ɗauke tsohon garin izuwa inda yake har zuwa yanzu, sai daga baya ne aka samu an maidowa da jinin Muhammadu Kigudu mulkin garin.
Abu ɗaya da zamu iya cewa yayi saura wanda kuma za'a iya tunawa dashi a tsohon garin Badari shine Tambari. Wanda akace yanzu haka yana masarautar getso sanadiyyar 'yar sarkin Baɗari da wani sarkin Getso ya taɓa aura, sai kuwaƴ ta tafi dashi izuwa can don a rinka kaɗa mata shi...