TUN KAFIN AURE 04

TUN KAFIN AURE💐 4


A hankali yake tuki kamar yana tausayin kasa. Fitsararrun matasan Abuja ne suka cika wurin maza da mata wanda abin takaici 'ya'yan musulmi ne mafiya yawan cikinsu. Kallo ne ya koma kan hadaddiyar motar da ya shigo da ita tun kafin a gane waye a ciki. Wuri ya samu yayi parking yana fitowa aka fara ihu da tafi
 Juni! Juni!! Juni!!!
Junaid ji yayi kansa ya kara fashewa. Sanye yake da wani matsatstsen jeans baki da bakin takalmi mai kyau. Farar riga ce a jikinsa mai dogon hannu amma bai balle maballi ko daya ba ana ganin bakar singlet din da yayi zanzaro da ita. Hannunsa wani agogo ne mai tsada ga bandana ya daura a kansa wanda ya tara gashi ya aski gefen hagu da dama. Kana ganinsa kaga yaron da ke ji da kudi, kyau da tsabar rashin tarbiya ko rashin sanin ciwon kai.
Junaid Rufai Bukar kenan dan senate president din Nigeria wanda yake fantamawa son ransa saboda kudi da kuruciya da ke cinsa.

Tun shigowarsa harabar club din take kallonsa kamar tsohuwar mayyar da ta kwana da yunwa. Tana son namiji mai kyau a rayuwarta gashi tun da ta fara zuwa club din bata taba ganinsa ba. Yana ta gaisawa da maza da mata tana binsa da ido har ya shige ciki. Itama binsa tayi ta sami wuri a gefe ta zauna don matan da sukayi kansa suna da yawa. Sai da taga an fara rawa ta je kusa da shi suka gaisa. Amma ke bakuwa ce ko ya tambaya yana mika mata cup cike da juice wanda aka sirka da kayan maye. Yes ta bashi amsa. Matar ta hadu don ba ya kirata yarinya ba, yasan da kyar idan bata girme shi ba. My name is Tilly beauty...sunan ya dace da ke kuwa. Ni suna na Junaid. Hmm amma naji ana kiranka Juni. Cire glasses dinsa ya yi kana mata wani shuumin kallo Juni friends dina ke kirana. Nima ina son zama daya daga cikinsu. Then you can call me Juni. Haka hira ta balle tsakaninsu karshe da suka fara buguwa da kyar suka karasa daya daga cikin dakunan da ake bayarwa haya a cikin club din.

Ganin baccinsa yayi nisa ta dauki kayanta ta saka ta kare masa kallo gaskiya Juni yana da kyau ga kudi...just what she needed. Takarda ta samu ta rubuta sunanta da phone number ta ajiye masa sannan ta fita. A waje ta hadu da kawarta Rosie suna haduwa suka tafa. Aiki yayi kyau Rosie sai munji daga gareshi. Shegiya Tilly baki da kyau fa Rosie ta fada tana dariya.
*******************

Da kyar ta samu Baffa ya barta taje gidan yayarta Hadiza kwana uku bayan ta gama exams. Suna kitchen sai hira suke yi Saif ya kira Hafsi a waya. Tashi tayi ta koma daki Hadiza tana ta yi mata tsiyar ta gudu kada aji hirarsu.

Kan gado ta kwanta sannan ta amsa wayar.
(Hello matar kin wuni lafiya?)

(Lafiya kalau ya aiki?)

(Ba dadi gaskiya. Ni missing dinki nake yi sosai yau.)

Yar dariya tayi domin itama kwana ukun da basu hadu ba tun ranar da suka je daukan hoto bata ji dadi ba. Babu abinda yafi damunta kamar yadda ta kwadaitu da son sake jin ya taba ko da hannunta ne. Ya Allah Ka kara tsare mana imaninmu.
(Ina gidan Yaya yanzu amma anjima bayan laasar zan tafi.)

dadi yaji har ransa domin kamar yadda take son kasancewa tare dashi abin yafi daga wurinsa. Karshe dai yace zaizo ya dauketa.

Bayan ta idar da sallah ta zauna gaban mudubi fuskar nan tasha fenti. Hadiza ta kalleta Hafsi amma dai kinsan bai kamata ki fita da irin wannan adon kan titi ba ko. Saurin mikewa tayi to yi hakuri Yaya na yau ne kawai nayi shaawa. Saif na zuwa yayi mata waya tayi sallama da yayarta wadda har kudin mota ta kara mata. Tana rufe gate din gidan ta tsaya ta feshe jikinta da turare mai kamshi abinda bata saba ba domin tasan rashin dacewar mace ta tsaya gaban saurayi tana kamshi irin wannan banda zunubi a addinance. Sai dai ita kanta ta rasa gane dalilinta na yin hakan. Annabi SAW yayi gaskiya da ya fada mana cewa shaidan yana gudu a jikin mutum kamar yadda jini yake gudu. Shi aikin sabo da kadan muke farawa sai a hankali ya zame mana jiki. Mu kiyaye don Allah da yadda muke langabewa jikin maza ayi hoto wai da sunan pre-wedding pictures. 'Yar uwa idan baki aure shi ba meye makomar rungume rungumen da ku ka yi duk da sunan wayewa?




Batul Mamman💖


Post a Comment (0)