YADDA AKE YIN DAMBUN KIFI


*Dambun Kifi*

*Zubaida Isah*✍🇳🇬

www.zubaidaisah.wordpress.com

Kifi manya 3
Mai kofi 2
Lemon tsami 1
Attaruhu
Albasa isasshiya
Curry, citta, tafarnuwa, sinadarin dandano, gishiri
Ruwa kofi 2

•Ki matse lemon tsami a ruwa, ki wanke kifin da shi. Wannan zai taimaka wajen rage qarnin kifin. Ki bar shi ya tsane ya sha iska.

•Ki zuba kifi a tukunya ki sa ruwa da albasa da citta da tafarnuwa ki bar shi ya dahu luguf. Sai ki tace in akwai ragowar ruwa.

• Ki ciccire kayar (manyan). Ki sa hannu ki dan dagargaza shi. Sai ki zuba mai a kasko in yai zafi ki sa kifin da sinadarin dandano da albasa yankakkiya da jajjagen attaruhu.

•Ki yi ta juyawa zai dauki awa guda ana juya shi. Kina juyawa za ki ga yana brown a hankali har ya zama brown gabadaya.In yayi zaki ga ya fara alamun kamawa ,man ya tsotse kenan. Sai ki yi ta juyawa da sauri sauri. Sai ki sauke kar ki bari ya kone.

•Sai ki dora colander a kan wani mazubi , sai ki zuba dambun a cikin net ki daure sosai. Ki dora net din a kan colander. Ki danne shi da abu me nauyi. Sai ki barshi ya kwana a haka. Za ki ga mai ya fita sosai. 
Dambun kifi akwai dadi ga kamshi.

*Note*
~Shi ba a sa masa mai da yawa kamar dambun nama.
~Ba ruwan ki da dakawa a turmi ko tukawa da muciya. Bayan ya dahu yayo luguf, kina sawa a mai kina juyawa za ki ga yana dagargajewa.
~Ki matse shi da kyau yadda man zai fita sosai.
~Ba ya son wuta da yawa wajen dafawa da suyar gabadaya. 


*IG@zubayda-isah*
Post a Comment (0)