YADDA ZA'ARABUDA GISHIRINTFUSKA

YADDA ZA'ARABUDA GISHIRINTFUSKA



Shin mene ne gishirin fuska? Gishirin fuska wani abu ne fari mai kama da gishiri a kan fuska. Abubuwan da ke kawo gishirin fuska su ne, yawan gumin fuska da maikon fuska. Idan muka yi gumi, fuskarmu takan fitar da maiko. Idan ba mu rika wanke fuskarmu a lokacin da ta yi gumi ba, sai ya taru ya zama gishirin fuska. Idan muka yi kokarin cire gishirin fuska da hannu, hakan yakan janyo kurajen fuska. A dalilin hakan ne ya sanya a wannan makon muka kawo hanyoyin rabuwa da gishirin fuska.
· Mu rika wanke fuskarmu a kalla sau biyu a rana da ruwan dumi da sabulu. Yin hakan na magance samuwar gishirin fuska, kuma yakan hana su fitowa.
· Mu zuba tafasasshen ruwa a kwano ko roba, sannan mu rufe kanmu da tawul, sai mu kawo kanmu a saman ruwan zafin, domin fuskarmu ta tiraru na tsawon minti 10. Yin hakan zai narkar da maikon fuska da ke kawo gishirin fuska.
· Mu samu bakar hoda (baking soda)- Za mu iya samun ta a shagon da ake sayar da kayan hada kek, daga nan sai mu kwaba ta da ruwa, sannan mu shafa a fuskarmu. Bayan hakan, sai mu jira ta bushe. Bayan ta bushe, sai mu wanke da ruwan dumi.
· Idan kuma ba za mu iya tirara fuskarmu ba, sai mu sanya tawul dinmu a ruwan zafi, sannan mu matse kafin mu goga a kan fuskarmu.
· Shan ruwa kamar kofi 8 ko 10 a rana na magance fitowar gishirin fuska.
· Lemun tsami na busar da maikon fuska. Za mu iya shafa ruwan lemun tsami ta hanyar amfani da auduga, bayan mun shafa kuma sai mu goge fuskarmu da wata audugar. Hakan na magance gishirin fuska.
· Zuma na taimakawa wajen rage gishirin fuska da kuma kurajen fuska. Mu shafa zuma a fuskarmu, sai mu bar ta har tsawon minti 10, sannan mu wanke da ruwan dumi.
A karshe muna fata za a rika amfani da wadannan hanyoyin da muka kawo don a magance gishirin fuska
DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 08080678100

Post a Comment (0)