Hasheem Salees Adam Kayarda
AURE BA WASA BA NE
Allah sarkin iko, shi ne mai zamani kuma mai bayar da aron numfashi ga duk wanda ya ga dama. Haka duniyar ta gada, wasu a tsawaita musu kwana, wasu kuma a gajarta musu. Wadanda a ka tsawaita ma kwana a duniyar nan su na gamuwa da gane gane iri iri, wasu na da zuciyar iya jurewa masifu da fargaba, a bangare guda kuma takaici na iya hallaka wasu.
Wadanda ke raye a wannan zamani na gane gane. Wasu al’amjuran ma sa mutu m ya yi zaton almara, tatsuniya ko hikaya ne.
Zamani ya zo da abubuwa da daman gaske, wasu masu kyau wasu kuma marasa kyau, don haka ne ma mafi kyawun shawarar masana shi ne kowa ya yi riko gam da al’adarshi ba tare da aro wata al’ada daga wani wuri ba.
Al’adun mutane na da ban mamaki, a wurin wasu kazantarku ita ce halas dinsu, ku kuma tsaftataccenku shi ne gurbataccensu.
Kafin na ci gaba da koro bayani sai na bayar da misalin irin bambance bambancen da ke tsakanin al’adu domin mu sa ke fahimtar yadda al’amarin ya ke da haske.
A baya gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da batun auren jinsi daya, hani ga dokar da za ta bayar da dama ga namiji ya auri namiji, haka nan ma mace ta auri mace ‘yar uwarta.
A wasu kasashen turai, sam wannan dabi’ar dabbobin ba abun kyama ba ne har ma sun lamince ma masu sha’awa, sun shigar da ita cikin kundin tsarin mulkinsu a kan halascin yin irin wannan aure. Wannan ya nuna wa sauran al’ummar duniya da ke tsananin kyamatar wannan halin dabbanci cewa al’adar wadancan turawa ta yi hannun riga da irin dattijuwar al’adarsu.
Haka nan idan mun dawo da misalinmu gida Nijeriya, mu na iya fahimtar bambancin al’ada a tsakanin kabilun da ke kudancin kasar da kuma kabilun da ke Arewaci.
Kaitsaye a na iya kawo wasu kabilu masu al’adar sai mace ta yi ciki a waje kafin nan a daura mata aure. Irin wadannan kabilu su a wurinsu namiji ba zai yi aure cikin duhu ba, dole ne sai ya yi gwajin shin matar da ya ke son aure ta na haihuwa ko kuwa juya (marar haihuwa) ce?.
Wanda irin wannan al’ada idan mu ka dauko shi mu ka zuba a cikin jerin al’adun mutanen Arewacin Nijeriya sai abun ya yi wani irin banbarakwai ba ko kyawun gani ballantana ji. A Arewa idan namiji na son yarinya da aure, dole ne sai ya nemi izinin iyayenta, sannan kuma bai halasta gare su su kebe ba a killataccen wurin da ba mutane ba yayin zance ko da kuwa ya biya kudin sadaki, matukar ba a shafa fatihar daurin aure ba.
Da wadannan ‘yan misali na ke son jaddadawa mai karatu cewa duk wata al’adar da mutanenmu (‘yan arewa) ke sha’awar aro wa daga wasu al’adun abun haushi ne da kyama. Saboda idan da wani zai dauki ta mu al’adar ya kai inda mu ke aro tasu ba za su aminta da ita ba, fito na fito ma za a yi da ita duk tsaftarta.
Abun na da matukar ban mamakin gaske yadda al’amarin aure ya kicime a wannan yanki (arewa) mai dadadden tarihin tsaftatacciyar al’ada, dattako, dabi’un kirki da kuma sanin ya kamata.
Lalacewar tarbiyyar ma akwai wacce idabn da a nan abun ya tsaya a na iya cewa da saukI ko kuma a ci gaba da fatan samun canji cikin gaggawa, amma fa.
Idan mace ba ta yi aure ba, a al’adarmu a na yi ma kaifin tunaninta uzuri yayin da ta aikata wasu laifukan, amma ita kuwa matar aure, uzurin kenan a janyo hankalinta da cewa, ‘in an girma a san an girma. Shekaru kadan za ki tara ‘ya ‘ya da jikoki.”
Don haka ya na da kyau matan aure su natsu da kyau su fahimta, duk wani abu na rashin mutunci ba nasu ba ne. saboda duk lokacin da ki ka jefa kanki cikin sahun marasa mutunci, wannan bakin fentin sai ya mamaye ilahirin ‘ya ‘ya da jikokinki.
Akwai matan da natsattsu ne amma mu’amalarsu da kawaye, sai su fara badalolin babu gaira ba dalili. Haka kuma akwai matan da zuciyarsu tas ta ke babu birbishin yaudara da cin amana a cikinta, amma da zaran sun fara ta’ammuli da yanar gizo sai shaidan ya yi musu saka.
Guguwar wayoyin salula masu dauke da yanar gizo da kuma sauran kafofin sadarwa ‘social network’ ya jefa ma’aurata cikin wani mawuyacin hali. Da yawa aurensu ya tsinke, wasu kuma an samu giftawar zargi, wasu kuma an rasa zaman lafiya rikicin yau daban na gobe ma daban.
Sai ka ga mata da mijinta, ba kunya ba tsoron Allah ta na yin hira da wani jibgegen katon da ba muharraminta ba. Wasu matan sai su ce ai gaisuwa ne kawai kuma daga ita ba wani abu. In ji wa?
Ke ki na ganin tarbiyyar kwarai ce da aurenki ki rika gaisawa da wasu mazan da ba ‘yan uwanki ba a waje?. Idan kuma an gaisa din, sai hira mai ma’ana ta shiga tsakani ki ka biye a ka ci gaba, wannan kuma me ki ka aikata?
Ba ma wannan ba, da yawan matan aure su na amfani da kafafen sadarwa na yanar gizo su na ha’intar mazajensu. Da yawa su na tattara samari, musamman matasa wadanda su ke soyayya da su (soyayya a kan aure).
Wannan wane irin zamani ne haka?. Ke da akwai igiyar aure sargafe a wuyanki, me za ki yi da shafukan sadarwa irinsu Facebook, twitter, badoo, bbm, 2g0, mxit, twitter da sauransu?. Ba wai yanar gizon ba ne ba a so ku yi aiki da shi don ku na matan aure, amma ya na da kyau ne ku mutunta aurenku.
Masana a fannin sanin halayyar jama’a dai sun ce ita zuciya wata bahaguwar aba ce wacce ke gamsuwa da sake sake masu kyau da marasa kyau. Idan ma tsarkin niyya ki ke ‘chatting’, ki na iya haduwa da shaidanin da zai iya dagula miki lissafi, to me zai hana tun farko ki watsar ki huta, aure fa ba wasa bane.Allah ya kyauta.