BABBAN ABUNDA AKESO IYAYE SU YI KUMA SU KIYAYE

👩🏼♠ *MUSLIM LADIES WW* ♣👩🏼


*TUESDAY TEAM*


*BABBAN ABUNDA AKESO IYAYE SU YI KUMA SU KIYAYE*



1- Dasa wa yaro jin nutsuwar zuci, da kama hannunsa domin daukaka matsayinsa, wannan kuwa yana iya kasancewa ne ta hanyar rashin wulakanta shi, da sanya masa jin daukaka da kamala ko rashin nuna masa gazawarsa. Don haka abin da ya kamata shi ne: a rika tattaunawa da shi, da neman shawararsa da nuna masa inda ya samu rauni, domin ya taso mutum mai dauke da jin cewa zai iya kasancewa jagora a kowane fage.


2- Rashin kallafa wa yaro abin da ya fi karfinsa, ko kuma ayyukan da ba ya son su, domin gudun kada ya gajiya ya kasa, wannan kuma yana iya janyo masa jin kasawa da rushe himmarsa.


3- Dada wa yaro kaimi domin ya zama wani babban mutum ta hanyar girmama masa manyan mutane da suka gabata ko rayayyu, da yi masa bayanin sirrin abin da ya sanya suka zama manyan mutane masu daraja, da kuma hanyoyin da suka bi domin kai wa ga wannan matsayin.


4- Kula da yaro domin kada girman kai da ruduwa da kansa su same shi domin yana ganin ya fi sauran abokansa kokari a karatu, da koya masa siffofin dabi’u kyawawa da ya kamata ya siffantu da su, da nuna masa wadannan ni’imomi da yake da su daga Allah ne kuma shi zai godewa.


5- Yi wa yaro bayanin abin da al’ummarsa take ciki dalla-dalla, da nuna masa yadda zai bayar da tasa gudummuwa domin kawo ci gaban al’ummarsa ta hanyar:
a. Samar masa akida ta gari da zai doru a kanta.
b. Bayanin gudummuwar da al’ummarsa ta bayar wajen ci gaban dan Adam.
c. Sanar da shi yadda zai fuskanci matsalolin da suka addabi al’ummarsa, da kuma sanya masa cewa yana da karfin da zai iya kawo karshensu.
d. Yi masa bayanin dalilan da suka sanya al’ummarsa samun ci baya, da dulmiya cikin jahilci, da mummunan halin da ta fada ciki, da kuma nuna masa cewa zai iya kauce wa wannan, kuma zai iya maganinsa.
e. Yi masa bayanin yiwuwar gyara da za a iya samarwa ta hanyar amfani da karfin da al’ummarsa take da shi.
f. Yi masa bayanin musulunci, da hikimarsa, da koyarwarsa mai kima da muhimmanci, domin gudun kada ya taso yana jahiltar addininsa. Kamar yadda sanar da shi Ubangjinsa ya zama wajibi na farko da za a ilmantar da shi a rayuwarsa. Sannan sai abin da zai biyo baya na sanar da shi hukunce-hukuncen addininsa, da kyawawan halayen musulunci da kimar da suke da ita, da koyar da shi al'adu na gari, da tarbiyyantar da shi kan kokarin aiki da su.


6- Sanya lura da karfafawa a kan babbar gudummuwar da telebishan, da radiyo, da mujallu, da kissoshi masu hoto, da labaru zasu iya bayarwa wajan tarbiyyar yara da gina su[8] . Wannan wani lamari ne da makarantu, da iyaye, da kafafen isar da sako, ya kamata su himmantu da su.


7- Duba zuwa ga tarihin gidaje na gari, muna da babban misali game da kissoshin "Gidan Abrar" wato gidan Ahlul Baiti (a.s) da ya hada da Sayyidi Ali (a.s) da Fadima (a.s) da ‘Ya’yansu Hasan da Husaini (a.s). Da koyar da kissarsu da ta zo a cikin surar Insan, wacce take koyar da mu sadaukarwar da suka yi, da alwashin yin azumi da suka yi, da kuma sadakar da suka yi da abin da zasu sha ruwa da shi karshen kowane azumi har kwana uku a jere; ga maraya, da miskini, da kuma ribataccen yaki [9] , domin karanta irin wadannan kissoshi zai sanya mana daukar ilimi da darussa masu yawa game da yadda ya kamata salihin gida mai tarbiyya ya kasance.



*SHDG*
_(SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE)_




Post a Comment (0)