13. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...
Muka tashi daga Bubakar, muka nufi Jarra, Wata rana mun yi sirdi, muna shirin tashi daga zango, sai wani bawan Ali ya zo ya dafa yarona, ya ce masa, “Za ka koma Bubakar. Yanzu Ali ne @bukarmada ubangijinka." Ya kuma juyo wurina, ya ce, “Duk abin da ka ke da shi za a koma da shi, sai dokinka. Amma Ali ya ce zai bar maka tafintanka.” Ban ce masa kala ba, amma na firgita da ganin yadda Demba ya zama bawa. Sai na yi maza sai masaukin Ali. Na same shi yana kalaci tare da fadawansa. Idona duk sun rufe hankalina ya tashi. Na ce masa in dai shigowa kasarsa da na yi shi ne laifin da na yi masa, to, ai ni ma horon da ya yi mini ya isa. Ya tsare ni babu gaira babu dalili, ya washe mini kayana duk, ya gwada mini azaba iri iri. Amma duk wannan bai dame ni ba kamar yadda ya kama mini yarona yanzu ya bautar. Shi dai yaron nan Demba ba bawa ba ne, da ne kamar @bukarmada kowa, kuma bai yi wani laifi ba. Yarona ne kurum, kuma ko bawa ne, ai irin wahalar da ya sha ta isa ya sami ’yanci. Ni na rabo shi da garinsu, na zo da shi don ya rika taimakona, ba kuwa zan yarda wani abu ya cuce shi ba. Saboda haka wannan kama shi da aka yi aka bautar mugun abu ne babba, kuma mummunan zalunci ne.
Duk abin nan Ali sai dubana kurum ya ke yi. bai ce kome ba. Sai da na kare, sa’an nan ya yi wani busasshen murmushi na mugunta, ya dako mini harara. Ya ce tafinta ya gaya mini maza in rufe bakina, in kuwa na ki, yanzu da ni da Demba za mu kama hanyar Bubakar, abin da ya same shi ya same ni. Da ganin hararar wannan mugu ka san akwai wani abu a karkashinta. Na kasa danne zuciyata, na yi ta @bukarmada shawarwarin yadda zan raba duniya da wannan bala’i. Amma ina? Ni kadai ne, ba ni da kowa, ba makami, kuma a cikin hannunsa na ke.
Yadda hankalina ya tashi, na Demba ma ya fi haka. Mun riga mun shaku da juna. Kuma da ya ke Ubangiji ya yi shi mai harka ne da ban dariya, sau da yawa shi ya kan shagaltar mini da zuciya har in dam manta da wahalar da na ke ciki. Saboda kuma ya san harsuna dabam dabam, yana taimakona a duk kasar da muka shiga. Amma aikin banza ne a nemi tausayi da imani ga @bukarmada mutanen wofi. Ina ji ina gani Demba. ya zama bawa!
Ina kuka da hawaye, Demba yana yi, haka muka rabu. Muka yi hannu da juna, muka yi sallama. Na ce masa ya yi hakuri, zan yi iya kokarina in na koma Gambiya im fanshe shi. Muna cikin wannan hali na bakin ciki, sai wadansu mutum uku suka zo suka tasa shi a gaba sai hanyar Bubakar. @bukarmada
Muka tashi sai Jarra. Na yi hamdala, na gode wa Allah, domin na sani zan sami hanyar tserewa. Da muka isa, kowa yakama masauki, ni kuma na tafi gidan abokina Daman Jumma. Na kwashe duk abin da Ali ya yi mini na gaya masa, har ma na ce ina so ya rokam mini shi im fanshi yarona Demba. Na ce in Ali ya maido mini da yarona zam biya shi fansa da hajja ta bayi biyu. Daman Jumma ya je ya yi iya kokarinsa don ya ciwo kan Ali, amma a banza. Ali ya ce ya ga Demba shi ne idona, shi ne @bukarmada hakimu, shi ne kafata, don shi ke ja mini hanya, shi ke nuna mini wuri wuri, shi ke mini tafinta. Saboda haka ba zai bar shi ya komo hannuna ba. Da Daman Jumma ya matsa, sai Ali ya ce in shi ya ke so ya sayi Demba zai sayar masa, amma dai ban da ni kuma.
Ban san yadda suka kare ba, don ran nan ina zaune sai ga babban bawan Ali ya zo, ya ce mini ubangijinsa ne ya aiko shi ya gaya mini zai koma Bubakar. Wai 'yan kwanaki kurum zai yi, kuma zai komo bayan ya yi hawan @bukarmada Sallar Azumi. Amma ba zai tafi da ni ba, sai in yi zamana a Jarra har ya dawo. Na yi murna ainun da jin wannan labari, amma ban yarda Ali zai iya barina a baya ba sai da tafintana Johnson ya zo ya cc mini ga shi can ya mika, sauran mutanensa kuma za su bi shi da safe. Gari na wayewa su kuma 'yan sauran suka yi sirdi, suka rankaya.
Babu irin barnar da Larabawan nan ba su yi ba'a cikin dan zaman da suka yi a Jarra. Bugu da kari ma ba su tashi garin ba sai da suka kama 'yam mata uku a bakin rijiya, suka tsere da su, suka bautar.
Ina Jarra watan azumi ya kare, kashegari mutanen grin suka yi Salla. Suna kiran wannan rana Banna Sali. Lalle kuwa wannan rana babba ce gare su, don da dare sai duk garin ya rude da kanshin dafe-dafe. Gari na @bukarmada wayewa sai abinci na ke ta gani ana shiga da shi gidaje. Ran nan dai mace da namiji, yaro da babba, da da da bawa, duk kowa ya ci abinci mai kyau iyakar cinsa ya bari. Kowa kuma ya ci ado, har bayin. Aka yini ko ina sai kade-kade ka ke ji, ana ta rawa, ana nashadi.
Da ya ke na tabbata ba zan sami yarona Demba ba, sai shawara ta zo mini ta neman hanyar gudu don in tsira da nawa 'yancin. Ban da wannan kuma na ga alamar mai masaukina ya fara gajiya da ni, Johnson tafintana kuma ya ce shi ba zai bi ni ba. Da ma haka ya ture mini, Ubangiji ne ya nufe mu da sauran ganawa, har @bukarmada Larabawa suka kama shi suka kawo wa Ali. Abin duniya duk ya dame ni, na rasa na yi. Babu Johnson, babu Demba, lalle ba shi yiwuwa in Kara gaba ni kadai. In kuma na tsaya Ali ya komo, ban san irin abin da zai same ni ba, ko da ma ga shi ana shawarar kwakule mini ido im Fatima ta gan ni. To, ta kuwa gan ni. Babu kuma damar in koma Ingila, don da shan kunyar mutanen kasarmu, su ce na kasa gano Kwara, gwamma in zama bawa har abada a hannun Ali, ko kuwa in yi gaba namun daji ko yunwa su kashe ni.
Ina cikin shawarwari sai kwaram muka ji wai ga yaki nan tafe, Sarkin Ka’arta ya tasam ma Jarra. Ran nan na ga abin @bukarmada tausayi! Nan da nan gari ya harmutse, sai kuka ka ke ta ji na mata da yara, suna shirga wa dabbobi kaya, suna shirin gudu!
Da na ga mutanen gari suna gudu har da mai gidana Daman, ni ma sai na bi su, tare da Johnson. Ga mu nan sai wani gari wai shi Kwaira. Nan muka sauka. A ran nan ina cikin @bukarmada fadama ina ba doki ruwa, sai aka ce ga wadansu Larabawa su hudu tare da babban bawan Ali. Na ce Johnson ya je ya ji irin abin da ya kawo su. Da ya dawo sai ya ce wai Ali ne ya ce su zo su tafi da ni. Sai na ji gabana ya fadi ras, don a duniyan nan babu abin da na ke tsoro kamar komawa hannun Ali. Na san karshena kisa ne. Ina komowa gida sai kuwa ga Larabawa nan, suka kewaye dokina, suka tambayi dakin da na ke kwana. Daya @bukarmada daga cikinsu ya ce sai a kwance dokin a kai gidan Sarkin Kwaira don kada in gudu. Sai wani ya ce a bar ni da dokina, don babu yadda zan iya tserewa a kan wannan kanjamammen kuru.
Da dare ya yi na shiga ba Johnson magana, na ce ya daure ya yi karfin hali mu tafi tare, ya ki. Na ce masa zan riba masa yawan jingar da muka yi, watau maimakon dukiya ta bawa hudu zam ba shi ta bawa takwas. Ya ce shi babu abin da zai daga da shi gaba . In ya tashi daga nan, Gambiya zai nufa. Ya kosa ya @bukarmada sadu da matarsa da ’yan’uwansa.
Ganin babu alamar jiyayya da Johnson, sai na daura niyyar tafiya ni kadai. Yamma tana yi sai ga Larabawan nan sun zo sun yi shimfida a kofar dakina daga waje, suka tura mu ciki da ni da Johnson. Cikin daren duk ba su yi barci ba, wai suna kumuna kada in gudu. Sai da gari ya waye tangaran sa'an nan Johnson ya zo ya rada mini wai ga su can @bukarmada barci ya kwashe su. Sai na shiga saka a zuciyata. Na ce to fa, yanzu kuma dabara ta rage ga mai shiga rijiya. Ko dai in yi kokarin fid da kaina, ko kuwa in koma haunun Ali. Ko da sunan wannan mugu ya zo raina, sai na ji gumi ya feso ya rufe ni. Wata zuciya ta ce in dakata har dare, wata kuwa ta ce dakatawa ba za ta fisshe ni ba.
Sai dai na nade kai da ragga, na zabi zan gudu. Saboda haka sai na tashi a hankali, na tsallake su sadaf sadaf, na dare bisa dokina. Muka yi ban kwana da Johnson, na ce ya kula da takardun nan da na ba shi zuwa wurin Dr. Laidley a Gambiya, ya kuma gaya musu ya bar ni lafiya, na nufi Bambara. Sai na buga kaimi, na yanki daji, na yi ta yi. Bayan na ci kamar mil daya daga Kwaira sai na bullo ta wata ruga, ashe ta Larabawa ce. Da ganina kuwa, suka saki kiwo suka yi ta bina suna ihu, suna jifa da duwatsu. Na tsere da kyar. @bukarmada Ban ko mai da numfashi ba sai na ji kira a bayana. Ko da na waiga sai na hango Larabawa guda biyu a sukwane bisa ingarmu, sun nufo ni, suna kada bindigarsu.
Na tabbata aikin banza ne in ce zan tsere masu a kan nawa kanjamammen dokin. Saboda haka ban ga abin yi ba sai in yarda da kaddara, sai na juya na tarye su. Da zuwa kowane ya @bukarmada kama kalmazurun linzami, suna huci, suna zagi, suka ce sai in koma wurin Ali. Ka san in zuciya ta firgita, tana zulumin abin da zai same ta ko alheri ko mugunta, to, ba ta cika kula da wanda ya faru ba. Abin da tafi so dai shi ne duk wanda zai faru ya faru kurum, ta huta. Haka zuciyata ta ke a lokacin. Bakin ciki ya ishe ni, na kosa im ma kashe ni Ali zai yi, ya kashe ni in huta da zullumi. Na yi @bukarmada sallama da duniya a zuciyata, ba na ko sha'awar kome cikinta, na wuce gaba Larabawan nan suna biye, muka juya.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Telegram: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada