12. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...
Kafin dawowar Ali, a kullum sai na tuna labarin cire ido da dan yaron nan ya @bukarmada ba ni. Watau iyakar idona da ganin wani abu a duniya kafin zuwan Fatima ne kurum, da ce ta zo ta kare kallona, za a kwakule su. @bukarmada Wannan mugun abu ya firgita ni kwarai, har in na kwanta da dare ba na iya barci, sai ajiyar zuciya.
Samun abokan hira kamar wannan Sharifi, da wani kuma da ya zo daga baya, ana ce da shi Sharif Sidi Muhammadu Mura Abdullah, har ya sa na ji dama. Amma wajen maganar abinci, gwamma ma lokacin azumi da yanzu. Sa'ad da Ali zai bi matarsa, a hannun bayinsa ya bar kome na game da abincimmu, amma irin abin da su ke gutsuro mana, ko yaro na goye sai ya cinye. Sun ma ta ba jera kwana biyu, ko bakin ruwa ba su ba mu ba balle lomar abinci. Tilas sai in tura yarona Demba ya tafi wani kauye ya wo barar ’yar gyada ya zo mu ci tare.
Yunwa tana da zafi da farko, amma in ta ci, ta ci, har ta fita, sai zafin ya bace. Maimakonsa sai mutum ya rasa karfi, jiri ya rika dibarsa. A lokacin babu abin tausayi kamar Johnson da Demba. Sai su kwanta lako a cikin rairayi, kamar sun suma. Ko an kawo abinci sai na yi da gaske su ke iya tashi. Ni kam ban ji ina iya yin barci ba. Ba na aikin kome daga share gumin azabar yunwa, sai ajiyar zuciya. Amma babban abin da ya fi ba ni tsoro shi ne in na zo tashi zaune daga kwance sai in ga dif, idona ya rufe, ina aniyar suma. Idon ba su budewa sai na ci abinci!
Ran nan kwaram sai ga labarin Sarkin Bambara yana kan iyakar kasar Ludamar, zai shigo da yaki. Jin haka sai Ali ya aiko maza mu taso. Muka tashi, muka dinga tafiya har wani gari wai shi Bubakar. A nan muka sami Ali da Fatima. Ya yi murna da ganina, ya ba ni hannu muka gaisa, ya kuma fada wa matarsa ni ne Nasaran da ya ke ba ta labari. Fatima da dubanta ka ga Balarabiya sosai, kamar mijinta. Mace ce mai gashi kwarai baki sidif, kuma tana da jiki kwarai. A farkon ganinta da ni ta nuna dan firgita, don ta ji an ce ni Nasara ne. Amma bayan mun yi dan tadi, na gaya mata yadda kasashen Nasara su ke, sai ta saki jiki da ni, har ta aiko mini da masakin madara.
Yanzu muna cikin bazara ne, rana tana ganiyar zafinta, ruwa kuma yana wuya. Akwai rijiyoyi uku a kofar Bubakar, a nan duka garin ke samu ruwan shansu da na dabbobinsu. Saboda wuyar ruwa har muka daina kukan yunwa, sai na kishi. Da ce na kwanta da dare, babu mafarkin da na ke yi sai na ruwa. Sai in ga wai ga ni a rafin kasarmu ina wanka. In na farka na ga a Afirka na ke, kuma ina tsare a hannun mutane marasa imani, wadanda za su bar mutum dan'uwansu da kishi, sai in ga duniya duk ta yi mini baki. Tilas kullum sai na yi barar ruwa, kamar yadda a ke barar abinci. Wata rana na yini ban kurba ruwa ba, ga rana kuwa kamar garwashin wuta, bakina babu ko digon yawu, makogwarona ya bushe. Can wajen sha biyun dare sai na dauki jakar ruwa, na nufi rijiya. Da isata na ce ina so zan debi ruwa, sai Larabawa suka kore ni. Na jirga rijiya ta biyu, haka. A ta uku ban sami mutane da yawa ba, sai wani tsoho da yara biyu, duk kuwa bakaken mutane ne, ba Larabawa ba. Na roke su, tsohon ya miko mini guga cike da ruwa. Na sa hannu zan karba, sai ya ji an ce wai ni Nasara ne. Sai ya yi maza ya kwace, ya zuba ruwan a wata kwatarniyar da ya ke ba shanunsa ruwa a ciki, ya ce in ina so sai in sha tare da shanun. Na duka, na tsoma bakina, shanu suna sha, ni kuma ina sha, har na koshi.
Ran nan sai na sami labari Ali zai tafi Jarra. Na ce a zuciyata Allah ya sa wannan mugu ya tafi da ni Jarra, Allah kuma ya sa hanyar tsira ta ke nan. Sai na yi wa Fatima magana, don na ga duk abin da Ali ya ke aikatawa, ko da maganar mulki ne, sai ta yarda. Da na gaya mata, sai na ga alamar ta yarda, har ma na ga ta fara jin tausayin irin halin da na ke ciki. Ranar tashi ta zo, addu’ata ta ci, aka tashi har da ni.
Muka tashi daga Bubakar, muka nufi Jarra, Wata rana mun yi sirdi, muna shirin tashi daga zango, sai wani bawan Ali ya zo ya dafa yarona, ya ce masa, “Za ka koma Bubakar. Yanzu Ali ne ubangijinka." Ya kuma juyo wurina, ya ce, “Duk abin da ka ke da shi za a koma da shi, sai dokinka. Amma Ali ya ce zai bar maka tafintanka.” Ban ce masa kala ba, amma na firgita da ganin yadda Demba ya zama bawa. Sai na yi maza sai masaukin Ali. Na same shi yana kalaci tare da fadawansa. Idona duk sun rufe hankalina ya tashi. Na ce masa in dai shigowa kasarsa da na yi shi ne laifin da na yi masa, to, ai ni ma horon da ya yi mini ya isa. Ya tsare ni babu gaira babu dalili, ya washe mini kayana duk, ya gwada mini azaba iri iri. Amma duk wannan bai dame ni ba kamar yadda ya kama mini yarona yanzu ya bautar. Shi dai yaron nan Demba ba bawa ba ne, da ne kamar kowa, kuma bai yi wani laifi ba. Yarona ne kurum, kuma ko bawa ne, ai irin wahalar da ya sha ta isa ya sami ’yanci. Ni na rabo shi da garinsu, na zo da shi don ya rika taimakona, ba kuwa zan yarda wani abu ya cuce shi ba. Saboda haka wannan kama shi da aka yi aka bautar mugun abu ne babba, kuma mummunan zalunci ne.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Telegram: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada