14. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...
Na tabbata aikin banza ne in ce zan tsere masu a kan nawa kanjamammen dokin. Saboda haka ban ga abin yi ba sai in yarda da kaddara, sai na juya na tarye su. Da zuwa kowane ya @bukarmada kama kalmazurun linzami, suna huci, suna zagi, suka ce sai in koma wurin Ali. Ka san in zuciya ta firgita, tana zulumin abin da zai same ta ko alheri ko mugunta, to, ba ta cika kula da wanda ya faru ba. Abin da tafi so dai shi ne duk wanda zai faru ya faru kurum, ta huta. Haka zuciyata ta ke a lokacin. Bakin ciki ya ishe ni, na kosa im ma kashe ni Ali zai yi, ya kashe ni in huta da zullumi. Na yi @bukarmada sallama da duniya a zuciyata, ba na ko sha'awar kome cikinta, na wuce gaba Larabawan nan suna biye, muka juya.
Mun taba tafiya, mun shiga cikin wata duhuwa, sai al'amarin duk ya sake, gaskiya ta fito fili. Daya daga cikin Larabawan nan ya ce in tsaya, in kwance kayana ya gani. Na @bukarmada kwance na baza, na koma waje guda na tsaya. Suka duba suka bincika, ba su dai ga kome na kirki wanda ya isa su dauka ba. Can sai daya cikinsu ya zo ya fizge mini wata rigar dari da ke wuyana, ya yaba a bayansa. Raba ni da wannan riga ya yi mini ciwo ainun, don kuwa ita na samu na ke maganin ruwa da ita, da dare kuma in rufa maganin dari da sauro. Sai na Shiga rokonsu kada su tafi da ita, sai dariya su ke mini. Da na ga za au tafi, na yi kamar zam bi su, wai dai don su ji tausayina su ba ni, af, sai daya ya juyo ya bugi kan dokina da gindin bindiga, ya ce ina daga kafa, zai @bukarmada harbe ni. Suka yi kaimi a guje, suka nufi Kwaira.
Daga nan na gane mutanen nan babu wanda ya aiko su don su kama ni. Fashi ya kawo su, sun kuwa yi mini. Sai na yi hamdala da na tsira da raina, na ci gaba. Amma don gudun kada a sake biyo ni, sai na saki hanya na yanki daji. Rabuwata da Ali ke nan. @bukarmada
HAKA TA CIM MA RUWA !
Da na duba gaba na duba baya, na duba dama da hagu, na ga na tsira daga hannun Ali wanda ya yi niyyar ko ya kashe ni, ko ya cire mini ido, sai jikina ya dauki rawa don murna. Sai na ji kamar na tashi daga ciwo ne, na saki jikina na mai da @bukarmada numfashina. Ga ni dai cikin filin hamada ne, amma na gwammace inda na ke da hannun Larabawa.
Ina cikin wannan murna sai wani sabon bakin cikin ya zo mini. Mutuwa dai har yanzu tana biye da ni, na ki Ali ya kashe ni, amma ga yunwa za ta kashe ni. Ba ni da kome, ba abinci, ba guzuri, ga ni kuwa a tsakiyar hamada kurum daga rairayi sai kaya. Babu ko da 'ya'yan itace, balle kuma ruwan sha. Na dai dinga tafiya har rana tsaka. Sai na ji zufa ta keto mini, idona ya rufe don tsananin zafi da kishi da yunwa. Sai na sauka, na hau bisa wata itaciya, na hanga wai ko na ga gida, ko hayaki in san @bukarmada inda mutum ya ke. Ban hango kome ba daga rairayi sai rairayi.
Na sauko, na hau, na yi gaba. Ina cikin tafiya sai na yi kicibis da garken awaki. Da na duba sai na ga 'yan yara ne, Larabawa, su ke kiwon. Na rarrashe su, da kyar suka matso inda na ke. Suka ce wai awakin nan na Ali ne, za su kai su Dina, don can am fi samun ruwa da wurin kiwo. Na roke su ruwa, sai suka nuna mini salkarsu babu ko digo daya a ciki, suka ce @bukarmada kuma tun safe su ke tafe amma ba su ga inda ruwa ya ke ba. Da na ji haka sai na tsorata, domin a lokacin nan kishi ya ci karfina, bakina ko digon yawu babu, duk ya bushe. Yadda na ke yi kuwa, na tabbata in da dokina yana da baki, kukan da zai yi ke nan.
Can wajen faduwar rana abu ya kai gagara, na ga mutuwa a fili. Tun dokina yana iya cira kafa har dai na ji ya fara sassarfa, yana alamar faduwa. Na sauka, na kora shi kamar jaki. Zuwa can na tashi zan cire wa dokin linzami, in rage masa azaba, sai kishi ya ci karfina. Idona ya rufe, jiri ya debe ni, sai na fadi somamme. Daga nan ko me ya faru, ko yaya aka yi, ban sani ba, ni dai kurum sai na farfado, na ga hannuna rike da @bukarmada kalfazurun doki. Na ce, “O. Haka Allah ya nufa ! Na rabu da kasarmu, ga ni wannan sararin hamada babu kowa babu kome, ba mutum, ba dabba, ba itace, ba ko tsiron ciyawa, daga rairayi sai rairayi. Ga ni kuwa ban kai ga bukatata ba, don har yanzu ban ga Kogin Kwara ba. Saboda in gan shi kuwa na fito tun daga Ingila, ina ratsa wadannan haddura iri iri. Watau duk wahalar da na sha tun fitowata gida ta zama ta banza ke nan, don ga kishi zai kashe ni !"
Ina cikin wannan kukan zuci sai na hango iska ta taso, kura ta yi sama. Sai kuma walkiya a arewa fal, fal. Nan da nan hankalina ya komo mini, don zafin kishi har na bude baki wai zan tare ruwa in ya fara fadowa. Sai na ji iskar tana kara matso ni, amma maimakon in ji faduwar ruwa, sai kaifafan rairayi ke ta buguna a fuska. Kafin a jima dai duk wurin ya @bukarmada murtuke, kura ta rufe mu, ta cika mini ido da baki da hanci. Da ta wuce, na yi ajiyar zuciya, na kora dokina muka yi gaba. Bayan jimawa kadan sai na sake ganin walkiya a sama, can sai na ji yayyafi, daga nan sai ruwa shaa kamar da kwarya ! Na gode wa, rahamar Ubangiji, sa’an nan na shimfida rigata bisa rairayi, na rika dauka in ta jika in kai bakina ina murdawa, ina tsotse ruwan. Da haka har na kashe kishina, dokina kuma ya sha.
Da na murmure, sai na yi gaba. A kwana a tashi ina dai tafe, wani wuri a kore ni, wani wuri a ba ni abinci. Wani wuri tilas in kwana a waje, sauro su ciza, kwari su ciza, ga kuraye ko kyarkeci, ga zaki ina jin rurinsu har gari ya waye, in sake dankar hanya. A wani gari na kwana a bukkar wani Bafillace, ya yi mini karimci ainun. Da zan tashi ya ce shi ba abin da ya ke so gare ni sai @bukarmada gashin kaina, don sun ji wai gashin Nasara magani ne. Na yanka na ba shi, ya yi ta tsalle don murna.
Ran nan sai na tasam ma Birnin Sego, tare da wadansu mutanen garin. Suka gaya mini zan. ga Jobila (watau haka su ke kiran Kogin Kwara). Da na ji haka, na yi kamar in yi fiffike in tashi, don dokin ganin wanna babban kogi. Da hantsi, kamar karfe takwas, kashegari sai muka hango sorayen Sego. Da muka zo bakin garin, sai abokan tafiyata suka dube ni, suka ce, “Geo affili!" (watau, "Dubi ruwan Kwara!”). In duba gabana, sai na hango ruwa fari fat yana gudu a hankali. Na ga wannan abin da na zo nema. Na ga kogin nan na Kwara wanda duniya ke ta nema shekara da shekaru, @bukarmada ruwansa sai walkiya wal wal wal ya ke yi a cikin rana, fadinsa sai ka ce Kogin Thames a Westminster, yana gudu yana nufa gabas. Na yi sauri na tafi gabarsa, na durkusa na kafa baki na sha ruwan. Sa'annan na daga kaina sama, na gode wa Sarki Mai kowa da kome, da ya ba ni ikon ida nufina na kai ga bukata, wahalata ba ta zama ta banza ba! Na debe kowace irin shakka yanzu, na tabbata Kwara ta fito yamma ne ta nufi gabas.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Telegram: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada