NASIHA GAME DA ZUHDU (GUDUN DUNIYA)
_قال الإمام علي اب الحسين فى كتابه "الزهد والوصية"؛_
_وإن صافيت أو خاللت خلا## ففى الرحمن فاجعل من تؤاخى._
_ولا تعدل بتقوالله شيئا##ودع عنك الملالة و التراخى فكيف تنال فى الدنيا سرورا## وأيام الحياة إلى انسلاخى وجل سرورها فيما عهدنا## مشوب بالبكاء وبالصراخى وقد عمي ابن آدم ﻻيراها## عمى أفضى إلى صمم الصماخى._
_Babban Malami kuma jagora Aliyu bin Husain yake cewa a littafin zuhdu da wasiyyah:
_- Idan zakayi abota da wani ko zaka riqi wani amini, To ina baka shawara kasanya wannan abota taku ko aminan taka tazama ankulla tane dan Allah ba dan duniya ba._
_- Kuma kada kayarda ka musanya tsoron Allah da wani abu daban, kacire duk wani nauyin jiki da kasala katashi kaji tsoron Allah da gaske malam._
_- Tayaya zaka samu wani farin ciki ma na din-din-din a wannan duniyar?, Alhalin kwanakinka na rayuwa acikinta suna tafiyane kullum zuwa ga karewa(kullum kwanakinka karewa suke amma baka lura kai kullum dai duniya duniya kudi kaidai kayi kudi gashi shekara da kwanaki sai karewa sukeyi)._
_- Kuma mafi yawancin farin cikin duniya cikin abinda muka sani kuma muka tabbatar, a cakude suke da kuka da kururuwa( yau inkana cikin farin ciki kana dariya nan gabakuma za'asameka kana kuka harda kururuwa)._
_- Amma duk irin wannan nusarwa game da duniya dan Adam idanuwansa sun makance baya ganinsu(gani irin nabasira ma'ana dai idanun basirarsa ta toshe shi kullum gani yake zai samu farin ciki mai dorewa acikin wannan duniya), Makantar har takai ga kunnuwansa sun toshe baya jin wannan nusarwa da gargadi da zaisa ya dauki matakin lura._
.
_قال المصنف رحمه الله: قيل لمحمد بن الحسن رحمه الله: أﻻ تصنف كتابا الزهد؟_
_Malam mai littafi(Imam Azzarnuji) yaci gaba da cewa: An cewa Muhammad bin Hasan Allah yaji kansa: Malam baka rubuta mana littafi akan gudun duniya(zuhdu) ba?_
_قال؛ صنفت كتابا فى البيوع! يعنى الزاهد هو الذى من يتحرز عن الشبهات والمكروهات فى التجارة، وكذالك فى سائر المعاملات والحرف._
_Sai ya bada amsa yace: Ai na rubuta littafi game da sha'anin kasuwanci! Yana nufin me gudun duniya shine wanda yake kokarin kiyayewa daga aukawa shubuha da abubuwan qi a game da sha'anin fataucinsa ko kasuwarsa, Hakama kuma yana kiyayesu a sauran ma'amaloli da sana'o'i. Karin bayani: Na'ama maganar shehin malami da ya rubuta littafin zuhdu da wasiyya ta fito fili kenan cewa ba'a gudun duniya(zuhdu)sai da ilmi dan wani zakaga ya dauka zama da kazantama da noqe-noqe shine zuhdu a'a zuhdu sai da ilmi akeyinsa kanemi ilmi kasan haram da halas kuma ka kaucewa aukawa shubuha shine ake nufi da zuhdu sabanin haka kuma kuskurene da yawa daga cikin sufayen dariqu sun halaka ta wajen kin zuwa su nemi ilmin addini suntsaya suna zuhdu da sa tufa ta tsummokara da cin abinci kadan wani ma sai yayi sati baici abinci mai kyau ba saidai dan guntun dabino da ruwa ga tulun jahilci ga girman kai ya hanashi zuwa gaban malamai yayi karatu waya gaya maka Allah jiki ko sura yake dubawa zuciya da aiki yake dubawa kuma tsoron Allah dashi ake tsere ba da tamalluq ba inkanason cikakkena bayani akan yadda shaidan ya rudi wasu daga cikin sufayen dariqu ya hanasu neman ilmi da zama da yunwa duk wai da sunan gudun duniya(zuhdu) kaje ka karanta littafin Talbisu Iblis na ibnul-Jauzi._
.
*✍🏻Abdul'aziz Sayyadi.*
Daga Zauren
*🕌Islamic Post WhatsApp.*
_Ku turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256* don shiga group dinmu a WhatsApp._