SHARHIN FIM ƊIN THE AVENGERS

SHARHIN FIM ƊIN THE AVENGERS 



* Bada Umarni: Joss Whedon

* Ɗaukar Nauyi: Kevin Feige

* Tsarawa: Joss Whedon

* Rubuta Labari: Zak Penn/Joss Whedon


The Avengers fim Ι—in jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2012 a Ƙasar Amurka. Labari ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna AVENGERS wanda Stan Lee da Jack Kirby Suka rubuta a Ζ™arΖ™ashin Kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios ne ya Ι—auki nauyin shirya fim Ι—in, yayin da Kamfanin Walt Disney Motion Pictures ya rarrabashi. 
Wannan Fim shi ne na shida daga cikin Fina Finan duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe Wiki (MCU) 

An fara Ɗaukar wannan Fim ne a cikin watan Afrilun 2011 a Albuquerque, New Mexico, kafin a Koma Cleveland, Ohio a watan Agusta, sannan aka koma New York City a watan Satumba.
An saki wannan Fim a ranar 11 ga watan Afrilun 2012 gidan sinima Ι—in Hollywood na El Capitan Theater, sannan aka sake shi Ƙasar Amurka gaba Ι—aya a ranar 4 ga watan Mayu 2012.

 Wannan Fim ya samu gagarumar nasara sosai, inda masana harkar Fina-Finai da 'yan kallo suka yabe shi sosai. Hakanan kuma Fim Ι—in ya kafa tarihi iri daban daban a harkar Kasuwancin Fina Finan duniya baki Ι—aya, sannan ya samu lambobin yabo masu tarin yawa. 

The Avengers ya kawo kuΙ—i kimanin dala biliyan $1.5 a harkar Kasuwancin Fina Finan duniya baki Ι—aya, sannan ya zama Fim na uku da yafi kowane Fim kawo kuΙ—i gaba Ι—aya a duniya kuma Fim Ι—in da yafi kowanne kawo kuΙ—i a shekara ta 2012. 

The Avengers shi ne Fim Ι—in Kamfanin Marvel na farko da ya fara kawo kuΙ—in da suka kai dala biliyan Ι—aya $1 a tikitai kawai. 
An yi na biyun sa mai suna Avengers: Age of Ultron a 2015 da kuma na ukun sa mai suna Avengers: Infinity War a 2018, sannan akwai na huΙ—un sa da ake sa ran zai fita a shekara ta 2019. 


LABARIN FIM ƊIN 

Hatsabibi Loki ne ya haΙ—u da wani fitinannen halitta da ake kira da Other, wanda ya kasance shugaba ne na wasu muggan halittu da ake kira da Chitauri. Other da waΙ—annan halittu duk suna rayuwa ne a wata daula da ke sararin samaniya. Loki da other sun Ζ™ulla Yarjejeniyar cewa other zai bashi mayaΖ™a daga cikin halittun da yake jagoran ta na Chitauri domin ya Ζ™wamushe lardin mutane idan har Loki zai iya kawo masa wani dutsen al'ajabi da ake kira da 'tesseract' wanda yake Ι—auke da wani irin Ζ™arfin tsafi na gaban kwatance. 

Nick Fury , daraktan Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. da mataimakiyar sa Maria Hill kuma sun samu isa wani keΙ“antaccen wuri inda masanin kimiyya Dakta Erik Selvig yake Jagorantar tawagar wasu masu bincike Yayinda suke bincike a kan wannan dutse na Tesseract. 

 Jami'i Phil Coulson ya bayyanawa Nick Fury cewa wannan dutse ya fara fitar da wani sabon yanayin Ζ™arfi wanda su basu gane masa ba. Kwatsam sai wannan dutsen kuma ya buΙ—e wata Ζ™ofa da kansa inda ya baiwa Loki damar shigowa daular mutane. 

Daga nan Loki sai ya Ι—auke wannan dutse sannan yayi amfani da Sandar tsafin sa ya karkatar da tunanin Selvig da wasu mutane da dama, cikin su harda Clint Barton domin su taimaka masa ya fece. Wannan hari da Loki ya kawo ne yasa Nick Fury ya sake tado da himmar Samar da tawagar Avengers. 

   Daga nan ne Nick Fury ya aiki Jami'a Natasha Romanoff Calcutta Domin ta taho da Dr. Bruce Banner Wanda ake sa ran zai iya gano inda wannan dutse na Tesseract yake ta hanyar fahimtar sinadaran 'Gamma Radiation dake tattare da shi. Shi kuwa Coulson sai ya ziyarci Tony Stark domin ya duba sakamakon binciken Erik Selvig, Yayinda shi kuma Nick Fury ya baiwa Steve Rogers aikin nemo dutsen. 

A Stuttgart kuma, Barton ya saci wani sinadarin iradium domin ya daidaita Ζ™arfin wannan dutsen Yayinda shi kuma Loki ya ja hankalin jama'ar dake wajen. Hakan ya jawo wani Ι—an Ζ™aramin artabu a tsakanin sa da Rogers, Stark da kuma Romanoff a Ζ™arshe dai Loki ya miΖ™a wuya. 


Yayinda ake kan hanyar kai Loki Hedikwatar S.H.I.E.L.D. Sai ga Thor yazo ya cece shi tare da fatar zai iya fahimtar da shi irin illar da shirin sa zai haifar ya kuma yi haΖ™uri ya koma Asgard. Bayan an Ι—an fafata a tsakanin Thor, Rogers da Tony Stark, sai Thor ya amince da a tafi da Loki izuwa ga tafkeken jirgin saman Ζ™ungiyar S.H.I.E.L.D. Helicarrier. Suna isa sai aka garΖ™ame Loki a wata magarΖ™amar gilashi, Yayinda Banner da Stark suke Ζ™oΖ™arin gano inda Tesseract Ι—in yake. 

 Daga nan kuma sai saΙ“anin Ra'ayi ya biyo bayan Shawarar yadda ya kamata a tunkari Loki da kuma ganowa da aka yi cewa S.H.I.E.L.D suna Ζ™oΖ™arin yin amfani da wannan dutse wajen Samar da muggan makaman Ζ™are-dangi akan baΖ™in haure da ke kawo musu hari daga sauran Dauloli. Ana cikin wannan gardama ne sai waΙ—annan mutane da Loki ya juyarwa da tunani suka kawo harin sumame har suka lalata inji Ι—aya na jirgin wanda hakan kuma yasa Banner ya koma Hulk. Stark da Rogers su kuma sai suka nufi injin domin su gyara shi saboda kada ya faΙ—i. 

Can shi kuma Thor sai yayi Ζ™oΖ™arin dakatar da Hulk inda suka kaure da faΙ—a ita kuma Romanoff sai ta tari Barton inda suka gwabza har ta sumar da shi wanda hakan yasa tsafin da Loki yayi masa ya karye. Loki ya samu damar guduwa bayan ya kashe Coulson sannan ya jefa Thor Ζ™asa daga jirgin Yayinda shima Hulk ya faΙ—a Ζ™asa bayan ya kaiwa wani Ζ™aramin jirgi hari. 

 Nick Fury sai yayi amfani da mutuwar Coulson wajen tilasta musu yin aiki tare da juna a matsayin su na tawaga Ι—aya. Stark da Rogers sai suka fahimci cewa Loki so yake yi ya samu nasara a kansu a bayyane domin hakan ne zai bashi damar nuna kanshi a matsayin sarkin lardin mutane gaba Ι—aya. Loki sai yayi amfani da wannan dutse na Tesseract tare da wata Na'ura da Erik selvig ya sana'anata a hasumiyar Stark Tower inda ya baiwa waΙ—annan halittu na chitauri damar shigowa lardin mutane. 

Rogers, Stark, Romanoff, Barton, da Thor sai suka haΙ—a kai domin su kare birnin New York daga wannan hari na Loki tunda a nan ne chitauri Ι—in suka sauka. Shi ma banner daga baya sai gashi yazo inda ya rikiΙ—a ya koma Hulk, a tare, wannan tawaga ta Avengers suka haΙ—a kai wajen yaΖ™ar waΙ—annan halittu tare kuma da kauda jama'a daga filin dagar. Can sai Hulk ya gano Loki inda ya suburbuΙ—e shi. 

Romanoff ta samu kaiwa ga wannan Ζ™ofa da ta baiwa halittun damar shigowa inda dakta selvig yayi mata bayanin cewa Sandar tsafin Loki ce kawai zata iya rufe Ζ™ofar.

A can gefe kuma, shuwagabannin Nick Fury dake kula da harkar tsaro ta duniya baki Ι—aya sun yi yunΖ™urin datse matsalar ta hanyar aikawa da makami mai linzami, amma sai Stark ya tare makamin sannan ya jefa shi cikin Ζ™ofar da halittun suke shigowa ta cikin ta. Hakan ya jawo tarwatsewar asalin jirgin mayaΖ™an dake daular da suke, sannan kuma ya kawo Ζ™arshen wannan hari a lardin mutane. Sai dai kuma wannan jan aiki da Stark yayi yasa Ζ™arfin rigarsa ya Ζ™are wanda hakan ya jawo faΙ—owar sa Ζ™asa a daidai lokacin da Romanoff ta rufe Ζ™ofar, sai dai Hulk ya cece shi daga wannan muguwar faΙ—uwa. 

 Bayan Ζ™ura ta lafa, sai Thor ya Ι—auki Loki da kuma Tesseract Ι—in ya tafi Asgard da su, yayin da shi kuma Fury ya tabbatar da cewa lallai tawagar zata sake dawowa yayin da aka buΖ™ace ta. A wata fitowa ta Ζ™arshe, an nuno Other yana faΙ—awa mai gidan sa cewa an samu rashin nasara akan harin da aka kaiwa daular mutane. Su kuma can tawagar Avengers Ι—in an nuno su a wani gidan abinci suna cin Shawarma 


JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA 


* Robert Downey Jr. - Tony Stark / Iron Man


* Chris Evans - Steve Rogers / Captain America


* Mark Ruffalo - Bruce Banner / Hulk


* Chris Hemsworth - Thor 


* Scarlett Johansson - Natasha Romanoff / Black Widow

* Jeremy Renner - Clint Barton / Hawkeye


* Tom Hiddleston - Loki:


* Clark Gregg - Phil Coulson


* Cobie Smulders - Maria Hill 


* Stellan SkarsgΓ₯rd - Erik Selvig


* Samuel L. Jackson - Nick Fury


* Gwyneth Paltrow - Pepper Potts 


* Maximiliano HernΓ‘ndez - Jasper Sitwell 


 * Paul Bettany - J.A.R.V.I.S.

 * Alexis Denisof - Other




<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

πŸ‘³πŸ»‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
πŸ“± _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
πŸ–₯ _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
πŸŒ€ _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 πŸŽ‘ _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 πŸ“§ _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...
Post a Comment (0)